Page 5

196 21 0
                                    

BABI NA BIYAR

Tunda ya rage saura kwana biyar su Safiyya su koma makaranta Goggo ke ta bakin ƙoƙarinta na ganin ta kyautata mata. Ta ɗinka mata umiforms da housewears, sauran su sport wears kuma sai sun je a can makarantar za a ba su. An ce babu buƙatan provision, don haka Goggo ba ta ba kanta wahalar wannan ba. Ta dai ce da Safiyya za ta haɗa mata su ƙanzo, gari da ƙuli-ƙuli amma fir-fir Sofi ta ce duka ba ta so, a ganin ta tamkar zubar da girma ne. Gwara a ba ta kuɗin ta yi wani uzurin da su.

Ranar da za ta tafi Zaria ta kama Lahadi. Ko baccin kirki ba ta yi ba tsabar farin cikin za ta je FGGC Zaria. Anti Fati ta kira ta ce da Goggon za su tarbi Sofi a tasha daga can ita za ta raka ta har makarantarsu, ta ƙarasa taimaka mata da abin da ya yi saura. Ba ƙaramin farin ciki hakan ya saka Goggo ba, ta yi mata godiya sannan ta yanke wayar tana ƙara jaddada ma Sofi da ta ji tsoron Allah a duk inda take, a duk in da za ta tsinci kanta.

Wannan zuwa makarantar shi ya kara buɗe idanuwan Sofi, da wayewarta ta shiga, ta kuma ƙarasa zama wayayya. Duk da Sofi ba ɗiyar kowa ba ce, face ɗiyar Hassu bebiya, ba kuma kowan kowa ba ce ba face kowar wake amma a haka cikin ƙanƙanin lokaci ta samu karɓuwar da da dama daga cikin yaran masu kuɗin da suke makarantar ma ba su same ta ba. Tun daga kan malamai har zuwa ɗalibai sun san da zaman ta, saboda ƙoƙari da ajin da take da shi. Maganarta ma kanta cike da ƙasaita, kamar yadda takunta yake cike da izza da gadara. JSS 1 take amma hatta manyansu sun sara ma yarinyar, duk yadda ta yi laifi aka so hukunta ta sai dai idan ba a haɗa ido da ita ba, kallo guda za ta ma mutum ya ji ba zai iya hukunta ta ba, tana da wani irin ƙwarjini na ban mamaki.

Ranar visiting da ma Anti Fati ta ce da Goggo kar ta ba kanta wahalar zuwa, daga nan an shirya mata duk wani abu da ya dace, za su je tare da Shatu da kuma Umma. Don haka sai Goggo ta samu nutsuwar zuciya, sai dai a can ƙasan ruhinta, kewar yaran nata ya kasa barin ta, musamman ma Shatu da take jin ta tamkar wani sashi na jikinta.
A inda ɗalibai ke jerawa domin jiran masu ziyara ita ma Sofi take zaune tana taunar cingam tana ƙas-ƙas, kamar daga sama ta ji muryar Baba mai faɗin alkhairi yana kiran sunanta; "Safiyya Usman Baba."
Ta ɗago kai ta kalle shi ba tare da ta ce uffan ba. Duk da matsuwar da ta yi da ta gan su amma hakan ba shi zai sanya ta ɓarar da ajinta ta bayyana ta matsu da zuwan nasu ba.
Ƙawarta ƙwaya ɗaya tak mai suna Amira ce ta zungure ta, ta ce
"Sofi da ke fa ake."
"Na sani."
Kawai ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa. Ganin ta taso ya sanya Baban ya tafi domin ci gaba da uzurin gabanshi.
Da gudun Shatu ta tarbe ta, fuskarta cike da annuri ta ma kasa furta komai sai washe haƙora kawai da take yi.
"Anti Fati sannunku da zuwa. Laah Umma ashe har da ke."
Sofi ta faɗa tana murmushi.
Daddumar hannun Shatu ta karɓa ta shimfiɗa musu, sannan suka hau jeranta kayan ziyarar da suka zo mata da su.

Wannan zuwan na su Anti Fati ba ƙaramin kankaro mata mutunci suka yi ba. Domin kuwa kalar shigar alfarmarsu kaɗai ya isa ya tabbatar wa sauran ɗalibai cewa naira ta kwanta musu, ga Shatu da ta ci wata 'yar ubansun 'yar kanti kalar pink, sannan ta yafa kalar ruwan hodar mayafi mai matuƙar kyau, ga kuma 'yar ƙaramar jaka mai hannun sarƙa, kai ka ce ba Shatun nan ɗiyar gidan Hassu Bebiya ba ce.
Tun daga wannan ranar sai bubbuɗawar Sofi ya ƙaru, magana ma sai da wanda ta ga damar yi, ƙawarta guda ɗaya tal har a lokacin, ita ɗin ma don mai haƙuri ce, amma ba kowacce ƙawa ba ce za ta iya ɗaukar abin da Amira ke ɗauka daga wurin Sofi ba.

Lokacin jarabawa ya yi, Sofi ta dage da karatunta kamar yadda ta saba, da yawan ɗalibai suna fatan a ce su ne ita, ta yadda take da naciyar karatun, kuma Allah Ya ba ta. Don haka da aka fara jarabawar ma burin duk 'yan ajinsu shi ne su zauna a tare da ita ko za su kwashi amsarta, don sun tabbata komai na takardar amsarta daidai ne.
Satinsu ɗaya da gama jarabawa, ranar jumu'a hutu, kuma a ranar ne za a ba su sakamako. Dukkansu babu wanda bai yi mamakin sakamakon da Sofi ta fita da shi ba. Kowanne subject A gare ta, daga mai casa'in da tara sai mai ɗari, don haka ba ma a iya ajinsu kaɗai ba, a duk JSS 1 Sofi ita ce ɗalibar da ta fi kowa maki. Da damar malamai ba su yi mamaki ba saboda yadda suka san ta, ko a aji tambaya ɗaya malami zai yi za ta tashi ta ba da amsa.
Kasantuwar zagayen karatu na farko ne ya sa babu kyauta, ana haɗa makin duka zagayun karatun ne a ƙarshen zagaye na uku sai a ba su kyauta daidai da sakamakon kowa.
Ranar hutu Anti Fati ta turo direbansu ɗaukar Sofi, Shatu ta so zuwa amma ita ma tata makarantar yau ne suke hutu, don haka shi kaɗai ya zo ɗaukarta.
Tun daga nesa ta hange shi ta kuma gane shi, ta san cewa ita ya zo ɗauka sai ta hau yanga da lauɗi, ba ta son taka ƙasa ma. Tana kallon yadda ake bin ta da ido tun daga cikin makarantar har zuwa gate inda motoci suke. Tana isa kusa da shi ta gaishe shi daƙilele, ba ta jira jin amsarshi ba ta ce
"Ga kayana a can ba zan iya ɗauka ba, mu je ka ɗaukar min."
Ta yi gaba ya mara mata baya har zuwa inda ta ajiye ƙaramar jakar da ta zuba tarkacen kayan karatunta, sai kuma ledar da kayan makarantarta suke ciki da 'yan abubuwan da ta san dole za ta buƙace su.
Kai tsaye gidan Umma (Kakar Shatu) suka wuce. Bayan dreban ya yi parking ya fito mata da kayanta sannan ya shiga cikin gida da su a ranshi yana mamakin yauƙin yarinyar, ko wata ɗiyar shugaban ƙasar ma ba za ta yi abin da take yi ba. Sai wani lumshe ido take yi tamkar 'yar ƙwaya, tana taku da ɗaiɗaya kamar ba ta son taka ƙasar, kamar wata rana ba a cikin ƙasar za a saka ta ba. Sai kuma ya yi guntun tsaki, tuna cewa yarinya ce ƙarama da ya tabbatar da ba ta ma san me duniya take ciki ba. Kawai dai halittarta ce haka, saboda kowanne yaro da kalarshi.
Satinta guda a gidan Umma aka ce ta shirya ta je Kaduna Goggo ta gan ta, amma Sofi ta ƙeƙashe ido ta ce ita babu inda za ta je ai sun yi waya da Goggon ita ta ce ta zauna ta ƙarasa hutunta a nan. Ganin yadda ta nace ya sa Umma ta rabu da ita kawai, don kar ta ɗauka ko ba su son zaman nata a gidan ne.
Ita kuwa Shatu har da kuka ta yi, saboda ta so zuwa Kaduna wurin Goggo amma Sofi ta ce ba za ta je ba, Umma kuma ta ce tunda haka ne ita ma ɗin ta yi haƙuri har zuwa sadda za a yi wani hutun.

Lokacin da hutunsu ya ƙare babu abin da Anti Fati ba ta saya wa Sofi ba. Haka sauran yayye da ƙannen Maman Shatu ma, kowa da tasa gudummuwar har kayan ma sun mata yawa ta nemi a rage har zuwa lokacin ziyara sai a kai mata amma Umma ta ce duk nata ne kuma musamman saboda komawar ta wannan hutun aka sayo mata. Don haka Sofi sai murna, an daɗa kankaro mata mutunci a wurin 'yan ɗakinsu.
Ranar da za ta tafi Shatu ta sha kuka tunda Anti Fati ta ce ban da ita za a mayar da Sofi, akwai tahfiz, ranar Lahadi ne.

A ɓangaren Goggo kuwa ta so ganin Safiyya, ta so ta ɗora ta a idanuwanta, sannan akwai wani ɓoyayyen zancen da ta so ta tattauna shi tare da Safiyyar ko za ta samu sauƙin zuciyarta, amma Sofi ta ƙeƙashe ta ce ita ba za ta dawo ba, a ƙarshe ma cewa ta yi
'Goggonmu idan kika takura sai na zo 'yan gidan nan za su ga kamar ba kya gode wa da ƙoƙarin da suke yi ne.'
Wannan dalilin ya sanya Goggo dole ta yi haƙuri ta adana damuwarta a cikin zuciya, ta kuma ci gaba da bin Safiyya da addu'a a duk inda take.

Komawar su Safiyya hutu sai waɗanda ba su san ta ba ma suka san ta, manyan sama da su da sauran malamai kowa burinsu su ga wannan yarinyar da lokaci ɗaya ta zo da farin jini ta kuma doke ɗalibai masu yawa. Sai dai ita a nata ɓangaren, ba ta taɓa ɗaga kai ta kalli masu zuwa ganin nata ba, har gwara malamai takan gaishe su, amma manyansu, ta fi ƙarfinsu.
Akwai ranar da suka taho ita da Amira daga ɓangaren karatu za su je hostel, hannun Sofi riƙe da ƙaramin bokitin ɗibar ruwa don da ma sukan je can da shi da safe idan ba su da ruwa, sai za su dawo su tsaya a gate din hostel su cika shi. Ji ta yi an ɗunguje ta da karfin gaske wanda har ya sanya bokitinta ya faɗi ƙasa ya ɓare, baki ɗaya ruwan da yake ciki ya zube.
Ta ɗago kanta tana kallon siniyan nasu da ke sanye da kayan zama hostel kalar cincinbale, da alama 'yan purple house ne, sannan sai ga ƙaramar yarinya ita kuma da uniform a jikinta.
Ba ta ce musu komai ba sai zuba musu idanuwa da ta yi kawai tana bin su da kallo. Tun daga yarinyar har sauran 'yan mata sai suka sunkuyar da kansu suka sha jinin jikinsu.
Ta juyo ga Amira ta ce
"Mu tafi."
Haɗe da kama hannunta.
Kafin su tafi ɗin ta ji muryar yarinyar tana faɗin
"Aunty Minal ba ki ɗaukar mata matakin ba fa ga shi nan har za ta tafi. Waccan yarinyar ta raina kowa a ajinmu, ɗazu ita ce ta ja Uncle Sani ya dake ni har ya fasa min hannu."
Ta ƙarasa maganar tana nuna mata inda hannunta ya yi burɗin bulala.
Sai Sofi ta tsaya cak ba tare da ta waiwayo ba. Ta ji ɗaya daga cikin 'yan matan ta ce
"Wannan yarinyar ai mayya ce. Ke ba ki ganin daga ta haɗa ido da mutum ko me yake ransa dole ya haƙura ya ƙyale ta?"
Sai a sannan Sofi ta juyo, taƙamaimai ba ta gane wadda ta yi maganar ba, sai ta saki tsadadden murmushinta ta ce,
"Za mu haɗu a gaban PC, za ku bayyana wadda ta kira ni da mayya, sannan kuma ta faɗi wadda na lashe, idan ba haka ba kuma sai mu haɗu a kotu."
Daga haka ba ta ƙara faɗar komai ba ta ja hannun Amira da  ƙarfi suka nufi ɗakinsu.

HAKKIN UWAWhere stories live. Discover now