Book 2

485 22 2
                                    

ZAFIN HAWAYENA
Written by SaNaz deeyah

Book2

_Talla Talla Talla_

_*Kamar yadda kuka sani, a Book one kunga yadda rayuwar Amatul-ahad ta faro a gidan mijinta, da kuma abinda ke tsakaninta da Fauwaz, ga kaɗan daga book 2 wanda zai fara zuwar muku 12/12/2021.*_

Idanunta sun kaɗa sun yi jajir, ta ɗagosu ta sauke kan fuskar Zayyan wanda yake tsaye a gabanta yana huci kamar wani zaki.
   "Idan har kana son sanin tsakanina da Fauwaz to shi za ka tambaya"

Shaƙota yayi y ɗago da ita, idanunta ta lumshe tana jin raɗaɗin shaƙar da yayi mata "Idan har na gano akwai wata alaƙa tsakaninki da Fauwaz wallahi sai na kasheku" Ya saketa sannan ya juya ya fita a fusace.

                *****

A hankali ta buɗe idanunta ta saukesu akan fuskar Manal, cikin jin jiki ta ce "Mutuwa zanyi dan Allah ki ɗauki wayata ki kirawo min Fauwaz"

Kallonta Manal tayi taja tsaki sannan ta kalli Azizat dake zaune gefen tasu katifar ta ce "Kiji wani shahashanci wai in kira mata Fauwaz, to ai ni nayi tunanin za ta ce in kira Sultan"

Dariya suka sheƙe da ita sannan Azizat ta ce "Toai sai kiyi yadda ta ce, tunda ta sakko"

"Ni Manal in ɗauki waya in kira wani gardin, wallahi ba zan kira ba, Amatul-ahad tunda har kina iya magana to za ki iya ƙoƙartawa kiyi kiran waya"

Azizat ta ce "Mu ƴan iskanki ashe akwai rana da zamu iya miki, ai cuta ba mutuwa bace, sai kin tashi ki cigaba da mana rashin mutumci, to ba zamu kira ba, ki mutu ma idan kin mutu Allah yaji ƙanki" Ta ƙarasa maganar tana miƙewa tsaye.

"Kin ga ni fa bama zan iya zaman ɗakin nan ba, dan raina zai iya ɓaci" Ta faɗa tana buɗe ƙofar ɗakin.

"Nima hakan take jirani mu tafi." Manal ta furta tana bin bayanta, har sai da ta kai ƙofa sannan ta ce "Shi kwarton naki, wato Sultan yazo yayi jinya kinji."

*Waye Sultan? Mene alaƙarsa da Amatul-ahad? Ina ne wannan guri da ta tsinci kanta? Sai yaushe Amatul-ahad za ta samu sassaucin rayuwa?*

Amsoshin sune cikin kashi na biyu, ku shiga cikin group ɗina dan samun littafin a sauƙaƙe, zai fara zuwar muku ne 12/12/2021

*Dokokin Group*

1- Ba'a turo ko wane littafi sai littafin ZAFIN HAWAYENA

2- Za'a iya tura link ko document na novel ko novel group amma banda na batsa.

3- Sallama da Amsa Sallsma wajibi ne.

4- Mutunta juna wajibi ne, ban yarda ayi min ɓata ko ƙananun maganganu ba.

5- Ban yarda a turo littafin sayarwa cikin group ɗina idan ba free pages ba.

6- Yin comments na ɗaya daga cikin manyan dokokin group muddin baki comment to za ki ganki a waje ne.

7- Kada ki turo min da stickers idan bba za ki iya typing kiyi godiya ko sharhi ba, to sticker bana la'akari da ita, dan haka bana son stickers kaca-kaca a group dina

*Duk wanda ya karya min doka to zai tsinci kansa a waje*

Sign by SaNaz_deeyah✍️

https://chat.whatsapp.com/GD22N1njkxXDfiTtyDnUu0

ZAFIN HAWAYENA(COMPLETE)✅Where stories live. Discover now