Chapter 1-2

130 8 2
                                    

🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️
*MACEN SIRRI*
🪂🪂🪂🪂🪂







*Zainab Habib/Mom Islam*

_Bismillahir rahmanir rahim_

ABUJA RUGAR MADAKI.

FREE PAGE 1-2

A can ƙasan anguwar akwai wani jeji daya kasance yana ɗauke da fulani ,wasu basa jin hausa wasu ko sbda suna tallan nono suna jin hausa. Rugar Ruwaji ta kasance tana ɗauke da shanaye masu yawan gaske ,kasancewar Ruwaji mutum ne mai arziƙin , ƴa ƴansa uku da Modibbo da Usmanu , da Ramatu ,Modibbo shine babba sai Usmanu ke binsa Jamila ce autarsu tana da shekaru 15 , yayan nata ko ya doshi talatin da biyu Usmanu shekarasa ashirin , sun yi karatun islamiya dana boko mai zurfi duk da karatun da sukayi basu yi yunƙurin barin jejin ba ,sbda ji sukeyi rayuwar nan tafi musu daɗi .

Matarsa wacce ƴaƴan suke kira da Dada tsohuwar kirki ga son mutane ita dai a burinta idan da Ruwaji ya yarje mata da tuni bata jejin nan ,koda yaushe tayi magana sai yace "mata ai komai da lokaci.

Ranar Juma'a ,ranace da Jamila take cin ado sosai kuma bata tallar nono ko ɗaya kuma babu wanda yake matsa mata sbda sun san irin ƙoƙarinta , bayan tayi wanka ta fito ɗaure da zanin atamfa ta nufi ɗakinsu ,kasancewar sun so zama a gurin harda gini sukayi kuma filin nasu ne , man shafawa ta ɗauko ta zauna bakin gado tare da lakato man ta shafe jikinta tare da taɓa Dada dake kwance tace "wane kaya zansa ?"Dada da bacci ya fara kamata tace "haba Jamila kullum nine mai zaɓa miki kaya kisa duk wanda kikaga yayi miki man "Jamila na murna ta janyo jakar kayanta ta ciro riga da zani iri ɗaya da ɗankwali zanin babu kalmasa ta ɗaura , ta juya tasa riga wai kar Dada taga ƙirgrn dangin ta , tana gama sawa ta fice tasa takalminta na roba wanda ba kullum take sanyashi ba sai zata yawon juma'a ko kuma anguwa , ficewa tayi ta nufi ɗakin Matar Usmanu mai suna Harira ta zauna tare da cewa "ina yayana ?"Harira irin matan nan ne da bata ƙaunar taga danginsa sun raɓesa tayi tayi akan subar rugar nan su koma wani gurin Usmanu yaƙi ,yace "inhar ba babansa bane yabar ruga shima ya bari gara ma ta dena wanan zancen "Harira ta taɓe baki tace "kin bani ajiyarsa ne da zaki tambayeni ?Jamila ba baya ba gurin rashin kunya tace "to idan ba'a tambayeki ba wa za'a tambaya ta fice da gudu tana murguɗawa Harira baki "zan kamaki "Harira tace "tana ƙwafa , Jamila na fita taci karo da yayan nata suna shirin shigowa gida shi da abokinsa ,cafkota Usmanu yayi yace "ina zaki ne Jamila naga kinci kwaliya ?"Jamila na dariya tace "yaya yaufa juma'a "Usmanu na dariya yace "au ai na mance ga abokina yazo gurinki "durƙusawa Jamila tayi ta gaida abokin yayan nata ya amsa yayan ya basu guri abokin ya riƙe hannun Jamila suka ɗan fara tafiya ,sai da sukayi nisa sanan ya tsaya yace "Jamila ba tun yanzu ba ina ɗawainiya da soyayyarki a zuciyata ina fatan zaki amince in fito a matsayin mijinki "rufe fuska Jamila tayi kana tace "ni nacewa "baba bazanyi aure da wuri ba karatu zanyi kuma ya amince min "murmishi abokin yayi kana yace "naji ban katse ki ba idan munyi aure nayi miki alƙawarin barinki kici gaba da karatu kinji "kasancewarta mai wa wayon gaske tace "Laminu kayi haƙuri ni karatu zanyi bazanyi aure yanzu ba "ta juya ta dawo gida ,da gudu ta faɗa ɗakin nasu tare da sakin kuka a jikin Dada ,cikin firgici Dada ta miƙe tace "mai ya faru ne Jamila am"Jamila dake share hawaye taba wa Dada labarin kaf hirar da sukayi da Laminu bata rage komai ba ,Dada tace "Jamila am ba haka akeyi ba kinsan Laminu yana da zuciya kuma abin da tunaninsa yazo masa shi yake baya duba abin da zai biyo baya ina ganin ki bashi haƙuri ku rabu lafiya shine mafita.
Jamila dake kuka tace "nifa karatu nake sonyi Dada "uhm Dada tace "tare da miƙewa ta fice sbda fitinar Jamila .
Sai da Laminu ya daɗe zaune a gurin da Jamila ta barshi yayi dariyar mugunta tare da cewa "yaro man kaza in tasan wani batasan wani ba "ya miƙe yabar gurin , kai tsaye gidansu ya wuce ya sami mamansa wacce yake ce mata Fulani tana zaune tana gyara masara , ya zauna kusa da ita cikin shagwaɓe fuska yace "Fulani nace ina son yarinyar Ruwaji tace "bata sona wlh duk abin da ya biyo baya suyi kuka da kansu "gaban Fulani ne ya faɗi har da zata haushi da faɗa dai kuma ta sassauta murya kasancewarsa auta kuma shine ɗanta tilo bayanshi ko ɓari bata taɓa yiba a hanlin yanzu yana da shekaru ashirin da bakwai a duniya ,tace "Laminu na kabi a hankali ni da kaina zanje gidan in samesu inyi musu magana akan kana son ƴarsu "turo baki Laminu yayi kana yace "ai tace "ba yanzu zatayi aure ba kuma ta zageni ma "waro ido Fulani tayi kana tace "ikon Allah har Jamila takai matakin da zata dinga yiwa na gaba da ita rashin kunya to ai yayi ka barni dasu kawai "ba tare da Laminu ya kula Fulani ba ya wuce ya barta zaune a gurin , dandalin da suke zama shida abokansa ya nufa ,yana zuwa suka fara ɗago masa hannu yawancin su tsummokara ne a hannunsu na shaye-shaye , da alamun damuwa Laminu ya zauna a cikinsu yace "kai ku dakata wlh ina cikin wani hali ,wai kamar ni Jamila tace "bata sona ,kuma naga ƙiyayyata a cikin idonta ina wlhi da sake "abokan ne suka tuntsire da dariya ɗaya daga cikinsu yace "ai bakasan abin da zakayi ba ,kawai ka bari ta fito da nono ka hura mata hodar nan da muke siyarwa "tafawa sukayi Laminu yace "gaskiya nagode da shawara ,kwata-kwata ban kawo wanan tunanin ba ashe gara danazo gareku tabbas nagode "abokan sukace kai dalla ware tsakaninmu har da wata godiya ne "cikin muryar su data kasance babu daɗin saurara , ƙarɓar nasa yayi shima yabi sahu ,suna zaune a gurin har yamma tayi sbda ba sana'a suke ba sana'arsu itace siyarda hodar ibilis , sun bugu sosai basa tantance fari da baƙi Lamin yace "mu haɗu gobe ni nayi gida "amsa masa sukayi da a huta lpy "ya tafi yana tangaɗi .
Kai tsaye ɗakinsa dake ƙofar gida ya nufa tare da buɗe kwaɗon jiki ya shige ,ya faɗi jugub kan katifarsa yana surutai ,sallah kam babu magana sai dai muce Allah ya bamu alheri.
Washe gari tun safe Jamila ta fito wanka ,bayan ta shirya aka haɗa mata nono a robar fenti da fura da dambu da suga ,Dada ta ɗorata har zata fita Dada tace "bakici komai ba Jamila ?"waro ido Jamila tayi kana tace "ai na mance amma idan naje can zansha nono "to Dada tace "tayi mata Allah ya bada sa'a "amin Jamila tace "ta wuce , tana cikin tafiya ta haɗu da babanta tace "baba sai na dawo "yace "Jamila Allah ya dawo dake lafiya tace "amin ya wuce , tana tafiya tana waƙa har ta iso ƙofar gidan su Laminu ,tsayawa tayi ta gaishe da Fulani mahaifiyar Laminu ,amsawa Fulani tayi babu yabo babu fallasa tace "ya maman naki ?"lafiya Jamila tace "ta wuce tana ci gaba da waƙarta , tayi nisa sosai tana shirin gyara hijab ɗinta daya rufe mata fuska taji an cafki boobs ɗinta ,a razane ta fara kiciniyar buɗe fuskarta hannunta ɗaya na riƙe da robar dake kanta cikin muryarta siririya tace "dan Allah waye bana son islanci "Laminu daya rikice jin taurin boobs ɗinta ya ɓarar da nonon tare da ɗagata cak still fuskarta a rufe yake yana tafiya da ita yana waige ɗaya daga cikin abokinsa yazo da mashin suka haye , tafiya suke sosai babu ko sararawa sai da suka iso wani katafaren gurin mai kama da store, dan ɗaki ne na ajiyar abinci , mashin ɗin ya tsayar , Laminu yace "yawwa Arɗo barmu anan kaje ka sanya ihu kace kaga wani ya gudu da Jamila "Jamila dake cukuwaikuye da hijab tace "....!

Ina masoya littafin NIDA YARINYA a fito a nunamin love ta hanyar siyan zazzafan littafina mai ɗauke da tsantsar soyayya wacce ta wuce na littafin NIDA YARINYA kardai in cimaku da surutu siyan nagari..

*Littafin kuɗi ne 300 via 3175689751 Zainab Habibu first bank shaidar biya ta wanan lambar 08141799224 idan kuma katin ne mtn zaki turo ki ɗauki hoton katin ki turomin ,pls banda vtu idan zakiyi ki gayamin ,ƴan Niger suyi mgna ta wanan number 84506476*

MACEN SIRRIWhere stories live. Discover now