001

29 4 1
                                    

*INA DA DALILI!*

_✍🏾Khadijarh Muhd Sha'abarn_
*_(Dijarty❤️)_*

*NA SAƊAUKAR GA LITTAFIN NAN GA ABDURRAHMAN MUHD (AIIMAR) JAMA'A KU SHAIDA*

*Wattpad account*
https://www.wattpad.com/user/Naanarh2021

~_Masoyana am back! son so nake yi muku💋💯_~

🔗 _*بسم الله الرحمن الرحيم*_🔗

*001*
Babu abinda ka ke ji yana tashi a dokar dajin sai ƙarar bindiga, wani kyakkyawan saurayi ne zaune akan wata kujerar ƙarfe yana girgiza ƙafa ɗaya kan ɗaya, kallon gawar mutum da ya harbe yayi babu alamar da na sanin abinda yayi domin zuciyarsa a ƙeƙeshe take, babu imani ko tausayi a tare dashi, "Dogo" ya kira sunan wani yaronsa cikin kakkausar murya, wani ƙaton mutumi ne ya je kusa dashi tare da tsugunnawa a kusa dashi, yana cewa "gani Gold!" Gold ya miƙe tsaye tare da cewa "ka je ka fito min da duk wanda mukayi da ƴan uwansu yau za'a turo da kuɗin fansarsu, dan idan lokacin da na gindaya musu yayi basu turo ba, tabbas zan kirasu domin su ji yadda zan tarwatsa kawunansu kowanne daga cikinsu" Dogo cikin ladabi ya miƙe ya nufi gurin da suke saka mutane idan sun yi kidnapping ɗinsu, Dogo ya ɗauki kusan mintina biyar a cikin wannan akurkin gurin, ba tare da ya fito ba, sai chan gashi ya fito hannunsa riƙe da wata murtukekiyar igiya yana janta, mutane ne suka fara fitowa mata da maza kowannansu hannayensu a ɗaure yake, gaba ɗaya a galabaice suke, saboda irin wahalar da suke sha a hannunsu Gold, kullum cikin dukansu suke, kuma kullum sai sun bi su ɗaya bayan ɗaya suna saita musu bindiga a tsakiyar goshinsu, ba sa basu abinci sai dai su basu ganyen bishiya su ci, wani lokacin ma ganyen bishiyar ba sa basu, ruwa kuwa rabin wani ƙaramin kofi suke basu kullum sau ɗaya, ba za su ƙara basu ba sai waje gari a irin lokacin da suka basu sannan zasu ƙara shan ruwa, Allah sarki! wasu daga cikinsu suna tafiya suna faɗuwa, jikinsu gaba ɗaya babu kuzari, motsi ma ba sa iya yi sosai, a haka suka ƙarasa gurin Gold suka jeru a gabansa, su ashirin ne, har da tsofaffa da ƙananan yara wanda basu huce shekaru tara zuwa bakwai ba, ga ƴanmata da samari, gaba ɗayansu sun gama karaya kuma sun riga da sun saka a ransu yau kam mutuwa zasuyi idan har ba'a biya kuɗin fansansu ba, dan kuwa Gold bashi da imani ko kuma tausayi bai ɗauki kisan kai a matsayi babban abu ba, idan har ya gindaya lokacin da yake son a bashi kuɗi ba'a bashi ba, kashe mutum yake yi ko kuma ya kira ƴan mafiya ya siyar musu da mutane.

Komawa Gold yayi akan kujera ya zauna tare da ɗaukar glass ɗinsa akan hannun kujerar ya saka, ya riƙe bindiga da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuwa wayarsa yake kallon dan baya son ya ɗaga musu ƙafa dai-dai dana second ɗaya ace sun cigaba da shaƙar iskar duniya ba tare da ya gama da su ba "kuyi addu'a ƴan uwanku ko da sata ne suyi su kawo min kuɗin fansanku nan da awa ɗaya, domin kuwa idan basu kawo min kuɗin nan ba, ko minti ɗaya ba za ku ƙara a duniyar nan ba, zan aika ku garin da ba'a dawowa, ina matuƙar girmama lokaci kuma ina bashi dukkanin haƙƙinsa" Cikin ikon Allah kafin lokacin ya cika ƴan uwan mutanan nan suka dinga yin waya, Gold yayi musu kwatancen inda zasu a jiye kuɗin, ya tura ɗaya daga cikin yaransa ya tsaya a wajen yana karɓar kuɗin, gaba ɗaya an biya kuɗin fansarsu kuma ya sakesu, ya rage sai wasu ƙananun yara su biyu da basu fi shekara bakwai ba da alama ƴan biyu ne, Gold ya saita bindigarsa akan ɗaya cikin ɓacin rai ya fara magana "ƴan uwanku basu da cika alƙawari, kuma ba sa girmama alƙawari, sun ɓata min lokacina a banza, kuma wannan ya nuna min alamar cewar ba sa buƙatarku, dan haka yanzun nan zan gama da ku gaba ɗayanku" Ɗago kai ɗayar tayi hawaye na zuba daga idanuwanta tace "kayi haƙuri, idan kana ƙaunar mamanka da Babanka karka kashemu, ba mu da kowa a duniyar nan"
Gold ya kalleta yana murmushin mugunta yace "ya sunanki yarinya?"
"Hassana!"
"Hassana! wato idan ina ƙaunar Mamana da Babana kar na kasheku! to ai baki sani ba, wannan furucin da kikayi ne zai sa na kasheku ko da kuma ban yi niyyar kasheku ba! domin kuwa ba na ƙaunar iyayena na tsanesu fiye da tunanin mai tunani!" Ya ƙarasa maganar cikin zafin rai, Usaina tace "kayi haƙuri dan Allah, ba haka take so tace ba, kayi haƙuri bamu da kowa, ba mu da waɗanda zasu biya kuɗin fansarmu, Inna da Baffanmu sun mutu, Kawu Tasi'u kuma yana da kuɗi amman ba zai taɓa biyanka ba, saboda ba ya sonmu"
Gold ya miƙe tsaye tare da cewa "ba wai bayani nace kuyi min ba, ku zaɓa a cikinku wa zan fara kashewa, idan kuma ku ka ɓata min lokaci yanzun nan zan azabtar da ku sannan kuma nayi muku kisa mafi muni wanda ban taɓa yi wa wani ɗan adam ba!"
Hassana ta miƙe tsaya cikin ƙarfin zuciya ta ƙarasa gabansa tare da cewa "ina so na nemi alfarma a gurinka"
Gold yace "da alama dai Hassana kin mai da ni abokin wasanki, ki kalleni da kyau kin ga alamar ni za'a nemi alfarma a wajena na yi wa mutum? Ai alfarma ɗaya zan muku na sadaku da mutuwarku"
Hassana jikinta na rawa ta kama hannunsa tace "na san baka taɓa yi wa wani alfarma ba, amman dan Allah ina so mu kayi mana!"
Gold bai tsaya yin wani tunani ba yasa bindiga ya harbi Hassana a goshi, ta faɗi ƙasa Usaina ma harbinta yayi a goshin, Gold cikin ɓacin rai yace "ni ba'a neman alfarma a wajena domin kuwa ko mutum ya nema ba zai taɓa samu ba, duk abubuwan da nake yi *INA DA DALILI!"*

Sauran yaran Gold ɗin suka saka dariya tare da cewa "Wannan haka yake oga, babu wata alfarma anan wajen, domin bamu santa ba sam"
Gold yace "ku shirya zamuje farauta, sannan kuma kamar yadda muka saba, zamu chanza guri zamu tattara kayanmu zamu koma dajin Sama!"
Dukkansu suka amsa da cewa "an gama oga!"
Gold yace "yanzu akwai sauran mutane?"
Dogo yace "A'a! babu, daman su kaɗai ne suka rage mana!"
Gold yace "kuje ku shirya zamuje farauta yanzun nan!"
"To Oga Gold!"

      ***   ***   ***

Bindigoginsu suka ɗauko a cikin ƴar bukka da duk wasu abunda suka zo dashi dajin sannan suka fito kowannansu ya rataya bindigarsa a kafaɗarsa, Gold yana ganin sun fito ya fara tafiya cikin nutsuwa da isa, sunyi nisa sosai dan sun kusan fita daga dajin, Gold ya juyo ya kalli yaransa, su goma ne har shi sha ɗaya yace "Tsagiri, Faro, Tsigi ku ƙarasa bakin titi ku hango mana idan motoci sun fara hucewa sai ku zo ku faɗa mana, amman kada ku tafi da wannan bindigunnaku"
Suka amsa da "to Ogo", dukansu suka saka bindigunsu a wani buhu suka ba wa Dogo, Sannan suka nufi bakin titi, su kuma suka ƙarasa gurin wata bishiya, suka zazzauna a gindin bishiyar.
Tsigi sun kai kusan awa ɗaya basu dawo ba, suna bakin titi, har su Gold suka fara gajiya da zama, sai chan gasu sun dawo akan wani tsohon mashin, Gold yana ganinsu ya miƙe su ma sauran suka miƙe, tun kafin su ƙaraso kusa da su Gold Tsigi yayi musu alamar motoci sun fara hucewa.

Murmushin jin daɗi Gold yayi yace "Yes!"

*#SHARE*
*#COMMENTS*
*#FREE BOOK*

*© NAANARH M SHA'ABAN*
08122188717

INA DA DALILI!Where stories live. Discover now