tausayi😭

27 3 0
                                    

🏵️🏵️🏵️TAKAICIN WASU MAZAN🏵️🏵️🏵️
          NA OUM AYRAH
       (FATIMA MUSA ASHAFURA)
(BESTYN UMMY AYSHER)
   FREE BOOK

PAGE:O1

🔔📚
*JARUMAI WRITER'S ASSOCIATION📚*
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa}_
https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=337435884671992&id=103920888023494&sfnsn=mo
             
          *⚜️©J.A.W📚🖌️*

BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM...
YA ALLAH NA ROK'EKA YANDA KABANI IKON FARA RUBUTA WANNAN LITTAFIN NAN LAFIYA KASANYA IN'GAMASHI LAFIYA ALLAH KABANI IKON TSARK'AKE ALKALAMINA.

DAGA MASOYIYARKU MAI K'AUNAR FARIN CIKIN KU OUM AYRAH.

""""Shak'e yake da wuyanta sosai yana gwara kanta ga bango tare da fad'in "na tsaneki Wallahi, haka kawai kinzo kin zame'man masifa a'rayuwata, daga shigowa gida sai maganar in'yo miki cefane ke ga Jakka a'cici uwar ci,to ko ubanki bai isaba, yau babu a'bunda zakici,
Tuleleyir banza banyi ko si-si ba tin fita ta, to da Kan Uwarki zanyi miki cefan'an". ya saketa tare da turata k'asa.

  Take ta fad'i kanta ya gwaru da kyauran k'ofar,"  ta saki wani malalacin ihu dan  fad'uwar da tazo da tsautsayin da yakai goshinta da fashewa, ya fara Zubar jinin kamar anbud'e pampo,Cikin kuka "tace ni kaiwa haka NAJIB!?" ashe dama wannan lokacin zai'zo da zanyi karo da TAKAICIN WASU MAZAN da ake fad'a ina k'aryatawa", ta fashe da kuka mai cin rai ,Ahankali tace  "kataimaka man ka kaini Asibiti tin kamin jini na ya k'are", ta karasa cikin kuka sosai, hannunta dafe da goshinta..

Najib daya hakimce gefe yana kad'a k'afa dan sosai yau yakejin haushin matar tashi, kuma yayi Al'kawarin ko jinin ta zai kare bazai kaita ko bakin get ba balle Asibiti,

Cikin zafin Rad'ad'in ciwo take fad'in "ka duba girman Allah ka kaini Asibita Najeeb,jinina zai kare ka tausaya min,Dan Allah". cikin wani mawuyacin hali take magana amma ko ajikinshi,cikin ikon Allah da dabara ta mike tsaye tana mai cije jajayen labbanta,hannunta d'aya yana kan goshinta da yake zuban jini,d'ayan hannun kuma tana dafe da bango, tana tafiya cikin d'auriya da tsananin azaban ciwo,haka dai ta karasa cikin dakinta da babu komai ciki sai gado da toilet(bandaki)haka dai cikin taimakon Allah ta shiga ta gyara jikinta,tana cikin d'aure kanta sai ta fara jin karan kiran Najeeb, cikin fad'a da harkowa yake kiran sunanta,

Iklimat!Iklimat!!Iklimat!!!

Cikin fad'a yake fad'in kin "fito ne ko sai nazo na taddaki cikin matsiyacin d'akin nan naki "cikin mamaki da wani sabon tsoron shi da ya d'arsu cikin ranta,ta mike cikin wani irin yanayi na ban tausayi domin wani zazzabi take jin yana kokarin rufe ta, ga wani murd'awa da cikinta keyi,amma bata da yanda xata yi haka ta mike ciki babu kwari,domin jin kiran da yake mata na mainene, domin tsoronshi  take yanzu,ta karaso parlor din ta tsugunna nesa dashi cikin muryan mai alamun jin jiki,take fadin gani Abban yazeed,cikin tsantsan tsana da daure fuska yake fadin wajan nan da kika bata da jini wa kike son ya gyara maki,
Cikin kasa da murya take fadin yanzu dama nake shirin fitowa na gyara wajan,dogon tsaki(mstwwww)yaja cikin haushin ta ya mike ya bangaje ta ya wuce,cikin dauriya ta tashi ta fara Aikin gyara wajan,Tana cikin ai'kin cikin ta yayi wata irin Murd'awa da karfin dayasa har saida tasaki kayan aikin ta silale kasa tana salati faduwarta keda wuya tafarajin danshi a'kasanta cikin mamaki takai hannunta dan ganin mike faruwa ido tazaro ganin jini sosai yana tsattsafomata salati tasaki tana fadin mike shirin faruwa dani?a k'ok'arin ta na taga  ta tashi tanemi mai taimakamata duhu ya mamaye ganinta da jinta baki daya akaro na biyu tasake sulalewa kasa asume kankace mi jini ya ballemata kimanin 10mnt Yazeed ya shigo gidan da gudunshi cikin murna yake fadin ummina na dawo,ummina kina ina,ummin..... Bai kai ga karasawa bah yaga umminshi kwance a kasa cikin jini babu alamun rai tattare da ita, haka ciki hanzari ya karasa cikin kuka wajanta ya fada kanta, yana kuka ummina mai ya same ki,ummina karki mutu ki barni,yana tsaka da kuka aka turo kofa aka shigo antee rukaiyyace ta shigo,ummin zeed ya kike ya gid......bata kai ga karasa maganar bakinta bah,idonta ya fada kan yazeed dake kuka kamar ranshi zai fita,sanbatu yake alamar baya cikin haiyacinshi,daga dukkan alamu bai san da shigowar mutun bah fadi yake waya kashe ki,ummina ki tashi muje Asibiti kada jinin jikinki ya kare,sai alokacin antee rukaiyya ta dawo cikin haiyacinta,ta fita domin kiran mijinta,yazo ya taya ta kama iklimat domin su kai ta Asibiti

#comment
#share fisabillah
#vote

OUM AYRAH CE😍😍

💮💮TAKAICIN WASU MAZAN💮💮Where stories live. Discover now