01|Introduction

108 1 0
                                    


CAPTAIN RIDWAN

Meesty✍️

01|Introduction

بسم الله الرحمن الرحيم

_5:04pm_
Dass park residential area

Kwance take akan gadonta na 6 by 6.Matashiyar budurwa ce,bazata fi 18-20 years ba.Abun mamaki duk tsaruwan dakinta,wanda daga gani an kashe at least a few millions,rike take da wani waya qarami mai torch wanda yaji jiki.Tana cikin haka,sai ga wata budurwa ta shigo dakin kai tsaye ba tareda sallama ba,bare izini.

'Kan ubancan,wato ma kina kwance.Wai ba tuntuni nace ki min pounded yam ba?To Wallahi tun muna gane juna ki tashi.Mtsw.'Yasmin ta ja tsaki tareda fita tana buga door din da karfi,tana tafe tana mita.

Bahijja dake kwance ne ta tashi.Kai Masha Allah,ba dai kyau ba.Fara ce irin sosai din nan,ga kyau ga diri.Siririya ce sosai amma stomach din ta is not overly flat kuma bata da tumbi.Dayake tana sanye da mini hijab bazan iya fadin ya gashin kanta yake ba.Idanunta sanye yake da medicated glasses,wanda yasa ban tantace color din eyeballs nata ba.

Atunanina hanyar kofa zatayi,sai kawai naga tashiga ensuite.Tana gama abinda zatayi ta fito tasaka hijab dogo akan na jikinta.

Tana zuwa parlor ta samu Abdul zaune da Yasmin kusa dashi.Wucesu tayi,ta fita ta kofar baya ta zauna akan wani plastic chair kusada flowers,tana tunani.

Wacece Bahijja?

Asalin sunanta Bahijja Muhammad Sadis.Only child ce.Sunan mahaifinta Muhammad Sadis,haifaffen garin Yola,Adamawa State.Su biyu ne kadai yara gurin iyayensu,daga shi sai kaninshi,Muhammad Rabi'u.Bayan haduwarshi da mahaifiyar Bahijja ce iyayensu suka rasu a wani auto crash car accident.Mahaifiyar Bahijja dai sunanta Aleesha,kuma half cast ce,inda mamanta 'yar Maiduguri ce Babanta kuma dan Egypt.

Ta taso cikin qauna da gata,saboda ita kadai ce diyarsu kuma ita din mai sunan mahaifiyar babanta ne.Shiyasa ma akece mata Ummu Abeeha.
{Maman Babanta}

At 14 years old,mamanta ta rasu agurin haihuwa,sakamakon postpartum hemorrhage yayinda babyn stillborn ne.At 16 kuma babanta ya rasu saboda ciwon zuciyan daya kamu dashi na mutuwar matarsa,dalilin daya dawo da ita hannun Uncle Rabi'u da matarsa a Bauchi.

Anan ne ta samu admission a ATBU,Biochemistry.Tana 300level ne aka aura mata Abdul,wanda ya kasance da ne ga abokin Babanta.

Shidai Abdul kawai ya aureta ne don yayiwa mahaifinshi biyayya,amma shi cousin dinsa Yasmin yake so sannan kuma ita ne zabin mamanshi,inda yanzu saura one month aurenshi da sahibarsa,Yasmin.

Aure dai a suna ne kawai,saboda Mama (mahaifiyar Abdul),ta ce in wani abun auratayya ya shiga tsakaninsa da Bahijja sai ta tsine masa.Dama shima ba sonta yake ba,sai kawai baya shiga harkanta.Sai sufi sati biyu basu hadu ba kuma suna gida daya.Karshenta ma kawai hostel ta koma da zama,saboda yanda Yasmin da Zaynab (kanwarsa) suka sata a gaba.

Yanzu ma abun daya dawo da ita rashin lafiyar da Malam (mahaifinsa) yake fama dashi ne ya dawo da ita.

'Wai kam bazaki je kimin girkin bane?'Maganar Yasmin ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi.

'Maganar gaskiya bana shiga kitchen bare in yi girki saboda haka kawai kije ki dafa da kanki.'Amsar da Bahijja ta bata kenan acikin melodious voice nata.

Kafin tayi wata yunquri kawai Yasmin ta daga hannu zata mareta tayi sauri ta riqe hannun tareda wanka mata mari.

Tasss.Ai kuwa sai ga hawaye shar a fuskan Yasmin,saboda ba'a taba marinta ba sai yau.Kuka ta fashe dashi inda Abdul ya fito da gudu.

'Babe,meya same ki?'

Ai tana sauke hannunta sai ga shatin 'yatsu.Baiyi wata wata ba kawai ya sharara wa Bahijja mari sai da glasses din ta ya fadi ya fashe.Haka ta tsugunna tana lalumenshi taji Yasmin ta take mata hannu.Bata ce komai ba duk da qwallan da ta cika mata ido da kuma radadin da hannunta da fuskanta yake.Lalumen ta cigaba dayi,sai kuma tayi sa'a ta sami glasses din tasaka.Tashi tayi da niyyar komawa dakinta taji yace,

'Na sakeki saki na biyu.'

Rufe bakinshi keda wuya phone dinshi ta fara ringing.Ga mamakina sai naga ya fito wata sabon iPhone 11 pro max.Amsawa yayi sai naji yace gamu nan zuwa.

Juyowa yayi ya share wa Yasmin hawaye tareda riqo hannunta.Suna tafe yana rarrashinta.A parlor suka hadu da Zaynab ya aiketa ta kira Bahijja wacce tun bayan daukan glasses din ta tawuce daki tana tattare tarkace da kayayyakinta da tazo dasu gidan,saboda bata sa kaya ko daya daga cikin lefen da aka kawo mata ba.Don ma agwada mata kora da hali ake mata duk sizes din Yasmin ne komai.

Ce mata yayi ya dawo da ita dakinta sannan kuma kada ta kuskura ta fadawa Malam ya sake ta.Da toh ta amsa sannan suka fita zuwa duba jikin Malam din.

Wata sabuwar Toyota Avensis babba naga sun nu fa,inda Abdul yake cewa Yasmin tsarabar tafiyan da yayi ne wannan ya siyo mata.Aikuwa tayi murna harda tsalle.Nan dai suka shiga ya jasu sai Dutsen tanshi,gidansu Abdul.

Suna cikin tafiyan ne Zaynab dake danna waya take cewa,
'Aunty kin gani,El Bahrain twins sun kara posting pics din Captain Ridwan.Kai,gayen badai kyau ba.Wallahi idan na hadu dashi duk bura uba sai na samo numbern sa.'

Yasmin kuwa qyalqyalewa da dariya tayi,don ba qaramin dadi take ji ba in Zaynab ta kira ta aunty.

'Kai Zee,ko dashi za ayi ne?'

Aikuwa carab tace,'In dai muka hadu banyi aure ba.Kai ko a ranar da aka daura aure na ne to sai mijin ya sake ni alokacin'

Ita kuwa Bahijja da take jinsu aranta tace iska na wahalarda mai kayan kara,saboda tun ba yau ba take jin labarin Captain Ridwan a bakin Zaynab in tana bawa Yasmin ko Mama labarinsa.

Ahaka dai suka je suka gaishar da Malam.Ta sha habaici kam a wurin Mama.Zasu shiga motan ne tace don Allah su sauke ta a Federal low cost ta gaishe da uncle din ta ko a tsattsaye,ya zazzage ta kuma yaki tsayawa.A hanya suka tsaya a Havilah,saboda Yasmin tace tana son ta sha ice cream.Haka dai suka karisa gida,ta wuce dakinta.

Vote,Comment and Follow.
Love,
_Meesty✍️

Captain Ridwan | Very slow updateWhere stories live. Discover now