5&6

11 0 0
                                    

*TWIST OF FATE*
_(Karkatarwan Ƙaddara)_



_By_
_REAL ESHAA_

*Littafina na kuɗine #300  Via 6030406548 Abdullahi Aishatu keystone Bank ko kuma katin MTN ta wannan number 09068403802 'Yan uwa na Niger zaku tuntuɓi number ta danjin yadda zaku biya...*

*Free Page 5&6*

_________________________Cikin wata murya me cike da Mamaki tace"Aure keda RK how come??."Cikin farin cikin daya kasa ɓoyuwa afuskarta tace"Am so happy Sister Ainah please ki tayani son sa dan Allah kidena faɗa dashi kinga yanzu munza ma ɗaya."Ohhh I see Mrs Abdulrahman Kabeer Shareef Ashe har kun zama ɗaya...Rufe fuska Sajnah tayi da tafin hannunta,se kuma ta buɗe Cikin serious talk tace"Ainah kunyar haɗu wa dashi nakeji Wayyo Allah taya zan iya kallon fuskarsa??kode inkira sane Ina son Jin muryansa...Taɓe baki Ainah tayi tace"Please Sajnah duk da cewa ban taɓa soyayya ba anma zan baki shawara kar ki nuna masa kema kina son sa kibari seya fara furta Miki Kinga da alama Iyayensa ne suke son haɗawa...Kai Sajnah ta gyaɗa tace"Zanyi ƙoƙarin haka Insha Allah.
Cikin nutsuwa da ladabi Abbey yace"Gani Mama bayan ya zauna agefenta.Kallonsa tayi fuskarta ɗauke da Murmushi tace"Gobe Idan Allah yakaimu Kabiru zasu neman Auren Sajnah,"Cikin rashin fahimta Abbey yace"Alhaji Kabeer Kuma Mama??,"Eh Alhaji Kabeer Shareef ko baza ka bashi bane??.Ƙasa da Kai Abbey yayi cike da girmamawa yace"ba haka nake nufi ba Mama anma sena keganin kamar hakan be dace ba taya za'a bawa Alhaji Kabeer Auren Sajnah bayan Sajnah tamkar 'Ya take awajen Hajiya Fatima.Galala Granny ke kallonsa kamar ba zata ce komai ba se kuma tace"Yau naji shashanci wannan aishi ake kira sauri babu wajen zuwa Ina Alhaji Kabeer Ina Sajnah in banda gida danci irin naka??.Ƙasa da Kai Abbey yayi cikin rashin fahimta,Yace"Waza anema wa Auran nata?Sassauta Fuska tayi tace"Dama haka ka tambaya tun farko da yafi Abdulrahman ne keso."Masha Allah Allah ya kawo su lafiya"Ameen ta amsa tana Murmushi," seda safe.Allah ya tashemu lafiya,har ya Kai bakin ƙofa tace"Da kata anutse Abbey ya juya tare da sake zama a inda ya tashi."Ka cewa matar ka idan taga dama ta girka abincin taran baƙi idan Kuma tana baƙin ciki tabari..."Insha Allah za tayi Mama ya faɗa tare da Ficewa...
Washe gari tun Misalin ƙarfe ta kwas Ummu taja Ainah da Sajnah kichen kasancewar weekend ne.Farar Shinka da Miyar Okazea su kayi wanda yaji dry fish,crafish,nama,ganda,store fish,se kuma tuwon shinkafa da Miyar Egusi zo'bo da yaji pinaplee sukayi da kunun aya se snacks da suka haɗa a madedecin dining suka jera komai acikin ƙayataccen warmers da jug.Ajiyar zuciya Ummu ta sauƙe da faɗin"Alhamdulillah ganin komai ya kammala kallon tayi da faɗin"Go and take shower sun kusa ƙaraso wa kallon ta tamayar kan Ainah da tayi kicin-kicin da fuska tace"Je ki Kira Mama tazo taga abin da aka haɗa.Wara manyan Idanunta tayi with so much surprise tace"What do you mean Ummuna kina nufin se ankira ta tagani??,Ɓata fuska Ummu tayi tace"Za kije abinda nasa kine ko Kuma zaki tsaya yimin Silly question??."Clamly tace"Am sorry sannan ta juya ta fice kai tsaye sashen Granny ta nufa bakinta ɗauke da sallama, Ahankali tayi ƙasa da kanta ganin uban adon da Granny taci kamar ita za azo tambaya.Wani shegen kallo Granny ta watsa mata cikin fusata tace"Lafiya Zaki sani gaba kina yimin Dariya?,Ɓata fuska Ainah tayi tace"kinga ni ba neman rigima nazo ba Ummuna ce tace"kije kiga abinda aka shirya ma baƙi tana gama faɗin"Haka ta juya tafice batare data jira Jin amsar taba ,Cak ta tsaya tana kallon haɗaɗɗun motoci uku dake Shiga coumpound ɗinsu har su kayi parking akusa da ita.A hankali ya ziro Ƙafarsa dake cikin sauciki me kyan gaske kana ya fito sanye yake cikin bugagiyar shadda fara sol tasha ɗinkin zamani kansa sanye da baɓar hula yalwataccen sumarsa zuwa siririn sajensa na sheƙe idanunsa sanye suke cikin farin glass me kyan gaske jikinsa na fitar da sihirtaccen ƙamshi.Cikin sauri ta ɗauke Idanunta daga kansa tana jin bugun zuciyar ta na ƙaruwa cikin sar-sarfa take tafiya,Cak ta tsaya Jin an damƙe mata Hannu,Kafin tace wani abu muryan Faruk ya katseta,cikin Shagwaɓaɓɓiyar murya yace"Oooo Aunty Ainah where is My Friend??.Ɓata fuska tayi Cikin tsaresa da Ido tace"I think I told you stop calling me Aunty?. Shagwa'be fuska yayi yace"Oooo Sorry where is she?."Muje tana ciki ta faɗa tare da tafiya batare da ta yadda tasake juyawa ba,Cak ta tsaya tare da wara manyan Idanunta akansa jin abinda ya mata se kuma tayi saurin runtsewa Afusace ta fin cike hannunta daga nasa tana jifansa da mugun kallo,Ƙasa da kai Faruk yayi tare da fashewa da kuka cikin narkakkiyar murya yace"Am Sorry Ainah!.Kasa cewa komai tayi se tsaresa da Ido tayi tana mamakin abinda ya Mata,tsaki tayi tare da ƙyafta masa hannu tace"duk ranan da ka ƙara kuskuren yimin irin haka zaka sha mamakin abinda zan gwada maka Usuless.Cikin sauri RK ya ƙaraso wajen hannu Faruk ya riƙe da faɗin"me tayi maka??Hawaye Faruk ya share yace"Oooo She shouting me Dan na riƙe hannunta Ina murzawa.Tsaki Mom tayi ahasale tace"kaji min shegiyar yarinya me take nufi dashi? yaron da besan inda kansa yake bama bare ta zargesa kodan tasaba yawon gantalinta yasa take zaton haka kowa yake??.Kallonta RK yayi dan beyi zaton tabiyo bayansa ba, Lumshe Idanun sa yayi yace"please Faruk kar ka sake yin haka??.Kai ya gyaɗa cikin muryan kuka yace"I hate her! bana sonta!...Bakin su ɗauke da sallama suka kutsa kansu madedecin falon nasu su wanda ƙamshi me daɗi ke tashi.Cikin sakin fuska Abbey da Ummu ke faɗin"Sannun ku da zuwa ga wajen Zama,Anutse suka zauna cike da mutuntawa suka shiga gaisawa.Ainah na Shiga bedroom ta zauna agefen gado tare da Jan tsaki tana jin yanda tsikan jikinta ke tashi.Fitowa daga toilet Sajnah tayi ɗaure da towel Zama tayi abakin bed tana tsane ruwan jikinta,Lotion ta shafa,Kallon Ainah dake Jan tsaki akai akai tayi tace"Meyafaru Kuma?,Wani tsakin ta Kuma taja tace"Zauna in miki make-up dan batasan dogon magana. Murmushi Sajnah tayi tace"ok Ahankali Ainah tashiga tsara mata kwalliya,me kyan gaske,Masha Allah Ainah tace"tare da miƙewa siff ta buɗe wani material neavy blue da adon farin stone ajiki, da kuma manyan flowes ta ɗauka mata se kuma ta ɗaukauko mata medium veil, Kayan Sajnah ta amsa ta Sanya tare da rolling veil din,Wara Ido Ainah tayi ta rungumeta cike da so tace"you look very pretty sister ai sekisa Mr Abdul kasa numfashi.Murmushi Sajnah tayi tace"Ai bankai ki kyauba,Hararan ta Ainah tayi tare da tura madedecin bakinta tace"Kede kusheni kike son yi,Ina kika taɓa ganin baƙin mutum yafi fari kyau??.Lakace mata hanci Sajnah tayi tace"ai fari ba shi ne kyau ba,idan mace nada ido hanci ƙaramin baki wushirya,dimple,saje, shikenan Koda baƙa ce zakiga sihirtaccen kyawunta.Dariya Ainah tayi da faɗin"Oh really?.Zama Sajnah tayi tare da riƙe hannunta cikin gaskiya da gaskiya tace"Wallahi Ainah kina da quality da kowaneɗa namiji idan ya ganki akaro na farko zeji ya kamu da soyayyar ki,Kina da ilimi,kina da wayewa,kina da manyan hips da maza ke buƙata sannan kina da boobs Dede misali,kinga kuwa babu abinda zan nuna Miki banda hasken fata.Wara Ido Ainah tayi tace"Ohhh Ashe kinsan abinda namiji ke buƙata awajen mace,anya wannan Sajnah Granny ce??,Cike da zolaya taƙarashe maganan.Pillow Sajnah ta ɗauka,ganin haka yasa Ainah Miƙewa da gudu bin bayanta Sajnah tayi,Ihu Ainah tasanya tare da Ficewa daga bedroom ɗin tana ƙyalƙyala dariya.Cak ta tsaya tare da rusunar da kanta shaf ta mance da akwai mutane a falon,Hannu ta sanya da niyyan janyo veil ɗin dake kanta taji wayam ya Faɗi,Ƙasasa dakai tayi ta juya ta koma bedroom batare da tace"komai ba.Tsaki Granny taja tace"Bansan se yaushe Ainah zata nutsuba kullum tana girma tana ƙara shashanci.Taɓe baki Mom dake gefenta tayi tace"Ai ta ɗauki al'adun yahudawa ta ɗaurawa kanta bayan yanzu ba acikinsu take ba?,Ƙwafa Granny tayi da faɗin"shiyasa tun farko na hana Muhammad Auren wannan Tubabbiyar amma yaƙi ji...Da ido Ummi tayi wa Mom alamar tayi Shiru!.Ummu kam Murmushi tayi ta ɗauke kanta tare da miƙewa tayi musu iso zuwa dining tayi serving ɗin su.Kallon falon tayi taga RK be motsa daga inda yake ba se latse-latsen waya yake cike da kulawa tace"Son muje kaci abinci,Ƙasa da Kai yayi cike da kunya yace"Thanks Ummu am full."Ok tace"sannan ta bar wajen anutse ya Miƙe ya nufi ɗakin dake Corridor bakin sa maƙale da sallama yashiga Bedroom ɗin idanunsa akan Sajnah dake kishingiɗe,Cikin zumuɗi ta miƙe daga kishingiɗar da take ta zuba masa idanu, Murmushi ya sakar mata tare da janye idanun sa daga nata yana kallon madedecin bedroom ɗin nasu da babu wasu tar kace aciki se madedecin gadon su Wanda ke ɗauke da farin bedsheets se siff ɗin kayansu me guda shida se kuma dressing mirrow dake ɗauke da tulin perfume da mayukan shafawa,sekuma keat na kayan make-up,ƙasan ɗakin shimfiɗe yake da chanis capet pinch color labulayen ɗakin ma pinch color ne manyan windows ɗin dake arufe ya nufa ahankali ya leƙa bayan shuke shuken flowers ne awajen window nada girma zeyi rabin ƙofa sosai tsarin wajen ya burgesa lumshe ido yayi Yana shaƙar sanyayyar iskan dake kaɗawa.Anutse Sajnah ta miƙe ta isa daf dashi kamar me tsoron wani abu ta sanya hannu ta dafa kafaɗar sa,Hannu ya Sanya ya riƙe hannunta tare da juyawa Yana fuskantarta ƙasa tayi da kanta tana jin nutsuwa na diran Mata.Lallausan tafin hannunsa da gashi ke zagaye yasanya ya ɗago  fuskarta Yana kallon ƙwayar Idanunta.Lumshe Idanunta tayi tashiga motsa bakinta alamar magana take son furtawa anma ta kasa, Murmushi yayi wanda ya bayyanar da fararen haƙoronsa tare da lotsar da dimple ɗinsa cikin ƙasa da murya yace"Da alama akwai magana abakin ki!.ƙasa da kai tayi cike da kunya ta kasa furta komai wani irin kunyarsa take ji.Taɓe Baki yayi har ya buɗe baki zeyi magana ya fasa sakamakon ƙaran buɗe ƙofa da yaji.Wani irin kallo yake binta dashi tun daga kan zara-zaran yatsunta dake da duhu har zuwa kan santala-santalan cinyoyinta da yabaje acikin towel din ahankali yayi sama da Idanunsa inda ta ƙulle towel ɗin manyan boobs ɗinta acike kallonsa ya mayar kan dogon wuyanta da gashin kanta suka manne zara-zaran eyelashes ɗinsa sun jiƙe.Afusace Ainah taja dogon tsaki ganin irin kallon da yake bin jikinta dashi, Taɓe baki yayi tare da wurga mata mugun kallo irin bega abin kallon nanba.Takaici ne ya kama Ainah cikin yanayin ta narashi ɓoye abu tace"Malam wannan wani irin rashin mutuncine Zaki shigo ɗakin mutane batare da neman izini ba Sannan ka dinga ƙare musu kallo??."Clamly Sajnah tace"Please Ainah stop it na faɗa miki banason irin wannan abin ko?Banza Ainah ta mata tare da Zama agaban dressing mirrow tashiga murza lotion ajikinta.Hannunta duka biyu RK ya kama cikin muryan da Babu Wanda zeji yace"Rabu da ita kar ranki ya baci akan duk wani abu da zata min.Kai Sajnah ta gyaɗa tana sake damƙe hannunsa acikin nata.Bayan sun kammala cin abinci Daddy ya kalli Abbey tare da faɗin"Ina fatan Mama tayi maka bayanin zuwan mu??.Kai Abbey ya gyaɗa yace" ƙwarai tayi.Murmushi Daddy yayi ysce"to menene ra'ayin ka akai??."Cike da girmamawa Abbey yace"ai kai me iya bawa wani Auren Sajnah ce bare Kuma daga gidan ka Dan haka na bawa Abdulrahman auren Sajnah duniya da lahira,"Murmushi Daddy yayi da faɗin"Masha Allah tabbas nayi farin ciki,Kallon Uncle Jabeer Dady yayi yace"kashigo da kayan motan miƙewa Uncle Jabeer yayi tare da riƙe hannun Faruk suka fita tare.Ba daɗewa suka shigo hannun su dauƙe da catoon na sweet da Kuma huhun goro.Hannu Dady yasanya a aljihu tare da ciro dubu hamsin ya iyije agaban Abbey yace"ga kayan promise ɗin ta insha Allah za muso asanya rana nan bada daɗewa ba.Guɗa Granny ta ran gaɗa cike da farin ciki tace"Alhamduliilah nan bada daɗewa ba za'a Sanya rana.Godiya Mom da Ummi suka yi mata cike da Jin daɗi,Kallon Granny Mom tayi tace"Mama Ina Sajnah ce har muna Shirin tafiya bata fitoba,Washe baki Granny tayi tace"kinsanta da kunya bari naje na fito da ita.Miƙewa Ummu tayi tace"Bari na shigo da ita ta faɗa tare da nufar Corridor,Wara Ido RK yayi idanunsa akan Sajnah yace"tafiya nake ji, Murmushin mugunta Ainah dake fitowa daga toilet tayi bayan ta sanya kayanta tace"Ummu ce,kaga idan ta shigo se ka faɗa mata abinda ks keyi aɗakin,cikin tashin hankali Sajnah tace"No Sister Ainah please do something Kar Ummu ta gansa,Juya manyan Idanunta cike da isa tace""Ok beg me if kana son in rufa maka asiri,wani irin kallo yamata irin baki kai matsayin ba,"Ka faɗa ta ɗage🤷🏻‍♀️ irin damuwar kace.Saurin juyawa sukayi Jin an ɗaga labulen,Wani irin kallo Ummu ke binsu dashi cike da Mamaki tace"....

_Ga masu buƙatar atura musu PC zasu biya #500 ta wancan details._

*AYI SHEARING SABODA ALLAH*


*Ya Allah Ubangiji kaji'kan mahaifina ya Allah kagafar tamasa zunubansa ya Allah ka Kai hasken kabarin sa ya Allah kaji'kan duk kan musulman da suka rigamu gidan gaskiya ya Allah kasa idan namu yazo mucika da Imani...*

                         *ESHAA CE*🤙🏻

TWIST OF FATEWhere stories live. Discover now