10

2.3K 105 10
                                    

Talba ya mikawa Daddy wayar bayan ya gama dubawa.

"Daddy ku da kuke kusa da gobnati ya kamata ace kuna fada musu halin da ake ciki mana, mutanen nan suna cikin bala'i, kamar ni ne, kana zaune kana rayuwarka sai a iskoka a koreka daga gidanka a akashe yayanka kuma a keta haddin matanka, Wallahi tausayi suke ba ni matuka"

Cewar Talba cikin wani irin bacin rai da jin zafin abun da yake faruwa. Daddy yayi murmushi yana gyara zamansa.

"Mu'az kenan, waya fada maka gobnati bata san halin da ake ciki ba? Sun san komai, wannan matsalar tsoro tana kawo kudi sosai, fiye da yadda kake tunani, duk jihar dake fama da matsalar tsaro kudin da ake ware mata dabam, idan har aka magance matsalar to abinci wasu zai tsaya, kuma duk jihar da kaga suna fama da matsalar tsaro to suna da cigaba da ake bukata"

"Amman Daddy basa tsoron hakkin rai?"

"Wannan kuma ai sai lahira, Allah dai ya kyauta kawai amman matsalar tsoro a yanzu abu ne mai wahalar magancewa, domin an fi samun kudi ta gurin tun daga manya har kanana, na mu dai addu'a ne, da kuma taimaka musu da abun da Allah ya ba mu"

A hankali Talba ya busar da iskar bakinsa ya kalli Amal data doso inda suke sanye da uniform dinta na makaranta.

"Na yi magana da PA zai yi list din abubuwan da zamu siya mu kai musu soon"

"Maa Shaa Allah, hakan na da kyau"

"Wa za a kaiwa? Baaba?"

Amal ta tambaya tana aje fular abinci. Daga Daddy har Talba kallonta su kai, ta san ba maganar Baaba ake ba, kawai ta dauko maganar ne saboda tana son fadawa Daddy abun da ya faru ne, daman ita ce yar gulmar gidan komai akai a bakinta za aji.

"Wace Baaba kuma? Yan gudun hijira ake magana"

"Au na dauka Baaba za a kaiwa, Allah yasa dai ta ji sauki"

"Miya same ta?"

Daddy ya tambaya, a nan Amal ta zauna gefensa ta labarta masa irin abun da ta fadawa Talba.

"Taya Doctor zata yanke wannan hukunci bs tare da sani na ba? Tafi ki kirata"

Daddy ya fada rai a bace. Sai ta mike tsaye gabanta na faduwa.

"Ya sai ka ce ni kai ka fada"

Talba yayi murmushi, ita ma murmushin tai ta fice, bayan ta wuce Daddy ya kalli Talba.

"Ka san da maganar ne?"

Talba yayi shiru ba tare da ya amsawa Daddy da eh ko aa ba. Wanda hakan ya tabbatarwa da Daddy cewar ya sani kenan, domin idan be sani ba kai tsaye zai fadi cewar be sani ba.
Daddy be sake cewa komai ba har sai da Momy ta shigo dauke da wasu manyan kulolin abinci ta aje a gabansa, sai da Momy ta kalli Talba sannan ta kalli Daddy tana karantar yanayinsu.

"Lafiya dai engineer?"

Daddy ya kalleta irin duban da ke fassara mata bacin ransa.

"Baaba ta fado, har kun kaita asibiti amman baki sanar da ni ba"

Dagowa Momy tai ta kalli Talba da kansa ke kasa.

"Ina ganin kamar karamin abu.... "

"Karamin abu? Da gaske? Amina kin san abun da kike fada kuwa? Mutum ya fado daga sama zuwa kasa ki kira shi karamin abu? Idan har karamin abu ne yayanta zasu dauke ta su tafi da ita ne? Ko da ma karamin ciwo ne tun da har a nan ta samu matsalar ai ya kamata ki sanar da ni, kuma be kamata a bar yayanta su tafi da ita ba, a nan ya kamata a dauki nauyin komai na ta, shekara biyu tana aiki tare da mu"

"Ranka ya dade, ba wani ciwo ne sosai ba, kuma na kaita asibiti sun bata magani sai ta kira yayanta tace zasu tafi da ita, babu yadda ban yi ba amman suka ki yarda, kuma ina da niyar fada maka anjima da dare idan ka natsu"

BAKAR WASIKAWhere stories live. Discover now