D

186 40 2
                                    

🧕 UNAISA 🧕

*D*

✍️ Ayshatuuu

Ranar lahadi da sassafe na fito a wanka , na Gama shiryawa cikin doguwar riga coffee Ina yafa veil naji sallamar Mamaa, na amsa se gata ta shigo na gaishe da ita, ta zauna gefen gado sannan na zauna tace

" Har kin Gama shiryawa se tafiya kenan?"

Na gyada Kai na Ina Dan murmushi kadan

" Allah ya jikan honorable!"

Na amsa da Amin sannan tace

" Zaki dinga zuwa ko? Ko Dan Zan dinga zuwa Ina ganin ki. Ki kula da cikin jikin ki Dan Allah, kada ki Bari damuwa tayi Miki yawa, ki sani komai shiryayye ne daga gurin Allah, sannan kiyi hakuri abubuwan da suka faru a baya, bansan me yasa nayi Haka ba, bansani ba"

Nayi saurin riko hannun ta ganin idanun ta na cikowa da kwalla nace

" Ai ya wuce Mamaa, Inshaaa Allah Mamaa ya wuce, "

Ta aje min kudi tana min godiya, nayi saurin dubanta Ina girgiza Kai nace

" Mamaa inada kudi Dan Allah ki barshi"

Ta dube ni na Dan lokaci sannan tace

" Karki damu hakkin ki ne ai, kawo Mana akai kin manta"

Ban tuna ba kawai se na gyada Kiana na zura kudin a jaka Ina Mata godiya, tana murmushi tace

" Nagode da Kika zauna Dani na wajen kwanaki hamsin, nagode sosae duk abinda kike bukata ki sani hakkina ne na Nemo Miki shi, Allah ya jikan Honorable ya gafarta Masa ya kyautata namu zuwan"

Inada saurin kuka, wannan maganar tata tasa na fara kuka, ta rungume ni a jikinta tana lallashi, seda ta saka ni a gaba naci abinci sannan ta janyo akwatina na biyo ta da karamin da Kuma handbag dina. Suna zazzaune dukkan su a parlor suna breakfast. Ina shigowa Muhammad ya saki murmushi yace

" Anty Unaisa Ina kwana?"

Nace

" Lafiya Lau Yaya Muhammad, ya Islam?"

Ya dubi Islam Dake cinyar Maman ta yace

" Gata nan me kukan dare"

Nayi murmushi, Ahmad ma ya saki fuska sosae muka gaisa yace

" Babu matsala ko? Ba wani Abu?"

Na girgiza Kai nace

" Babu komai!"

Dan gaskiya nakan manta cewar ciki ne dani, bana laulayi ko kadan ko craves dinma ba nayi. Asiya ta dubeni muka gaisa na karbi Aarif a hannunta. Amma Bilkisu ko kallona batayi ba tana spreading chocolate spread akan slice bread a gaban ta. Idon Mamaa yasa nace

" Bilkisu Ina kwana!"

Muhammad ya kalleni sannan ya kalleta Bai ce komai ba, Mamaa tace

" Bilkisu kinada matsala da Unaisa ne? Na lura ko magana bakya mata"

Ta girgiza Kai Bata ce komai ba, Mamaa se tayi shiru, Ahmad ya Mike tareda Jan trolley na yace

" Anty Unaisa mu wuce ko?"

Na mike Ina gyara lullubi na na dubi Mamaa data mike nace

" Nagode Allah ya saka da alkhairi"

Ta rike hannuna muka fita harda Asiya me min kashedin na dinga cin abinci, se Dana shiga mota sannan Muhammad ya karaso mukai sallama dasu Mamaa na Mana Allah ya kiyaye Hanya. Tunda muka dauki hanya mukai shiru se karar radio Dake aiki har muka karasa kofar gidan mu, ya samu guri yayi parking yace

UNAISAUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum