EPISODE 2

9 4 0
                                    

*ILLAR SO*

Labari/tsarawa: Auwalu Musa Sumaila(Rest)
WhatsApp number: 07045209303
Facebook: Auwalu Musa Umar

🌟🌙🌙🌙🌙🌙🌙🌟
*🌙✨MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION🌙✨*
https://m.facebook.com/Moonlight-writers-association-109698351308376/

*'''We are the moonlight writers we shine all over the world.''🌍'* ✍️✍️
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~💞💞~~~~~~~

Godiya

Ina mika godiya ta ga Allah ɗaya bani ikon fara rubuta wannan labari Allah ya kara bani ikon kammalawa ya kuma tsare ni da rubuta abun ki.

                           Gargadi
Wannan labari kirkirane kai tsaye daga marubuci dan haka ban yarda wani ko wata amfani da wani bangare daga ciki.
        

Episode 2

Garin Benin city.

........................Watan Disamba (December) watane da duk wani mabiyin kirista yakewa tanadi domin nuna farinciki sa ga ranar haihuwar yesu, hakan yasa kasuwanci yake garawa a duk wani yakin na kudanci Nigeria. Daruruwan hausawa ne ke jigilan kayan masarufi zuwa wannan yanki domin lokacin kayan abinci na shiga sosai, bama iya kayan abinci ba komai a wannan lokacin yana karbuwa sakamakon kiristoci na kokarin nuna farinciki su. Nura na daya daga cikin mutane da suka shigo kudanci kasa domin kawo kayan masarufi. Wannan bashi ne zuwan sa na farko ba, duk karshen shekara yana  biyo abokai na garinsu domin cin kasuwar kirsimat.

Wannan shine zuwan sa na farko Benin city, duk shekara akwai jahar da yake zuwa shekara ta uku kenan da fara hakan yaje Lagos, yaje Asaba sai yanzu da yazo Benin city.
Ko'ina ka duba mutane ne ke harkoki wasu na tura kaya cikin baro, wasu na tsaye a gaban tebura ana hada hada, masu siyar da kayan sawa na shewa kiran masu siya haka masu kayan abinci ke shewar kira ko ina ihu ke tashi sakamakon rana ce daga ita sai kirismeti. Nura ne tsaye a gefe guda dauke da shinkafa cikin baro yana kasuwa cikin murna da annashuwa haka abun ya kasance har karfe shida na yamma.

Misali karfe takwas na dare unguwa mafi daukar baki a garin Benin city Gangare kowa ka gani a unguwar dan cirani ne, hakan yasa hausawan dake garin ke kawo abinci irin namu na gargajiya suna siyarwa. Duk wani kalan abinci akwai shi hakan yasa unguwar ke daukar hausawa. Gefe guda Nura ne da wasu abokan sa suna hira irin tasu ta 'yan kasuwa kowa na tofa albarkacin bakinsa, suna cikin wannan halin ne Khadija ta karaso inda suke hannunta rike da robar abinci ajiye wa tayi sannan tabi su daya bayan daya tana mika musu kowa na karba, kusan tun zuwan su Nura itace ke kawo musu abinci. Khadija mai tuwo budurwa ce da ba tafi shekara sha biyar a duniya, saboda iya kula da masu siyan abincinta yasa bata wani jira abincinta yake karewa.

"Khadija bazan gaji da tambayarki Kawarki ba?" Nura ne yake tambayarta yana murmushi bayan ya jefa wata katuwar lomar tuwo bakinsa.

Murmushi tayi ta dube shi tace "gaskiya bazan boye maka tun ranar da kabani sako na bata gaskiya bana fadamata saboda ina guje maka rashin mutuncin kawata."

"Ok ! kina nufin sakona ko daya baije kunnanta ba ? " ya tambayi Khadija cikin mamaki.

Ajiyar zuciya tayi sannan tace "Nura ba naki bane halin kawata ne ya jawo hakan amma zan fadamaka dalilin dayasa bana so na fadamata sakon ka, bari na gama bada abinci zan sanar da kai dalilina" tashi tayi ta fice daga rumfar da su Nura ke zaune.

Misalin karfe tara na dare Khadija ta karaso rumfar su Nura rike da kudade a hannunta da dukkan alamu kudin abincinta take bi take hadawa.

"Nura zan iya baka shawara?" Ta tambaye shi

"Eh mana in kin tabbatar zatamin amfani" ya bata amsa ya wani irin murmushi.

"Zulaihat  inkiya ta mai gari tasamo sunan ta mai gari ne daga wajan mahaifiyarta dalilin kuwa sanya mata wannan suna shine, diyarta ba matar kananan mutane bace, sannan mahaifiyar Zulaihat itace wacce ta daura yarta akan akidar da take na cewa soyayya zaman bata lokaci ne inhar kana da mai kaunarka kamar Alhaji Sale mai kabeji.

Tun bayar rasuwar mahaifin Zulaihat Alhaji Sale shine komai na su tun daga abinci makaranta da biyan gidan haya shike biya musu bukatar su, tun kawata na yarinya yake dawainiya da ita da mahaifiyarta. Bayan ta girma ne Alhaji Sale ya bukaci auren ta wajan mahaifiyarta yaci sa'a ta amince kuma ta fahimtar da Zulaihat ta karbi Alhaji Sale a matsayin mijin dazata aura. Aikuwa ba karamin dadi Alhaji Sale yaji ba hakan yasa ya kara sakin hannunsa sosai, dama kuma bawani tsufa yayi ba matashine dan shekara hamsin matarsa daya ya'yansa biyu kuma anan yake zaune da iyalinsa.

Haka ya cigaba da jika ta da kudade wanda duk sati sai taje kanti KADA plaza siyayya, dalilin hakan yasa ta dau girman kai da shan kamshi ta daurawa kanta gani take tsayawa kula samari bata lokaci ne tunda dai tasamu abun da kowa ke fatan samu.

Akwai wani lokaci da wani yaro Kabiru ya tunkareta da maganar soyayya ta jamashi kunne amma yaki haka tasa Habu Malians yaci mutunci yaron da mutane garinsu Kabiru suka kai kara haka aka kori karar saboda yadda Alhaji Sale ya shiga gaba dan ganin Habu Malian yasamu fita. Abubuwa biyu ta tsana a rayuwarta kace kana son ta ko kace mata yaushe zasu je garin mahaifinsu." Da tazo nan a zancan ta Nura dashi da abokansa ne suka ja wani dogon numfashi yace "gaskiya yasa naga bata kula mutane?"
Dariya ta sakamashi tace

"ka ga sai gobe idan kana bukatar karin labari na baka, kaga har kasa Birabira ya gudu da kudin tuwo na kasan shi baya so ya biya kudi sai ya kwana."
Dariya sukai gaba dayan su, saboda halin Birabira ne kin biyan masu abinci, kullum haka masu siyar mashi da koko suke fama dashi hatta gidan wanka sai kaji a na cacar baki dashi, abun daya ne yasa ake ragamashi barkwancinsa.

............... Zaune take cikin wata irin shigar kayan barci masu kama da fatar maciji,tana kallo akwatin talabejin dake makale a bango, faranti abinci ne a gabanta tana ci tana daukar kofin lemo dake gefe tana sha cikin annashuwa, bayan ta kammala ne wata mata fara mai matsakainin shekaru ta shigo tana kallo budurwar dake zaune tana kallo wasan kwaikwayo.

" Ta mai gari kalo kike ?" ta tambaye tana mata wani irin kalo.
Cikin sauri budurwa yarinyar ta waigo ta saki wani murmushi ta amsa mata "Eh umma i dey watch izzar so" ba abun mamaki bane wajan hausawa da ake kira yan kasa a garin Benin city saboda yadda borokin inglish (pigin English) ya kama bakin su yasa baza su iya magana batare da sun karasa da borokin ba,wasu lokutan ma basa Hausa a junansu.

"Okay my pikin enjoy your life" ta ce da diyarta.

Okay my followers enjoy ILLAR SO.
Nagode ina godiya masoya.

Du hast das Ende der veröffentlichten Teile erreicht.

⏰ Letzte Aktualisierung: May 17, 2022 ⏰

Füge diese Geschichte zu deiner Bibliothek hinzu, um über neue Kapitel informiert zu werden!

ILLAR SOWo Geschichten leben. Entdecke jetzt