KWANAKIN MAKO!

16 1 0
                                    

*MAYAFIN SHARRI*

7️⃣ Kwanakin Mako!

©️Hassana Ɗanlarabawa.

     EXQUISITE WRITERS FORUM

Ina nishi da numfarfashin ɓacin rai suka ja ni suka fitar da ni daga ajin zuwa ofishin malamai, idanuwana jajir zuciyata na bugawa tamkar za ta tsago ƙirjina ta fito, gani nake yi Salma ta gama cuta ta tunda ƙazamin bakinta ya furta yana so na.

Tsabar ɓacin rai ma kasa magana na yi a lokacin da shugaban makarantar ke tambayata abin da ya faru, da zarar na yi yunƙurin magana sai na ji tamkar zan amayo zuciyata, tilas na yi gum da bakina na saka fuskata cikin tafukan hannayena ina sakin ajiyar zuciya.

Da suka ga na kasa magana tilas suka kirawo mutum biyu daga cikin ɗaliban ajina suka tambaye su abin da ya faru, su kuma suka zayyane musu komai. In da ran shugaban makarantar ya ɓaci, a take ya yi furucin ya kori Salma daga makarantar, don daman ya sha korarta yayanta yana dawo da ita yana bayar da haƙuri, amma wannan ita ce kora ta ƙarshe babu dawowa, domin ya ce zamanta tare da ɗalibai haɗari ne, za ta iya ɓata tarbiyyar ɗaliban makarantar.

Wannan shi ya ɓata ran Salma sosai, ganin dukan da na yi mata wanda sai da na farfasa mata jiki, sannan kuma aka haɗa ta da kora. Ban san abin da ta gaya wa yayanta ba, kawai dai a washegarin faruwar lamarin da safe ina yanke wa Babana farce na ji ana sallama a ƙofar gida. Na ajiye rezar a gefe na dubi Baba na ce.

"Baba na ji sallama ne, bari na je na duba."

"To je ka ka duba Habibu." Baba ya ba ni umarni.

Na miƙe na zura silifas ɗina na tunkari zauren gidanmu. A ƙofar gida na hangi Saleh yayan Salma da turɓunanniyar fuskarsa tamkar baƙin hadari, ina zuwa na yi masa sallama tare da miƙa masa hannu don mu gaisa, ya zabga mini wata irin harara kamar idanuwansa za su faɗo ƙasa, a fusace ya fara magana.

"Kai ƙaramin mara kunya, ba gaisawa na zo mu yi ba, na zo ne domin na ji dalilin da ya sa ka mayar mini da ƙanwa tamkar jaka."

Na yi ƙaramin murmushi na ba shi amsa.

      "To da farko dai ba sunana ƙaramin mara kunya ba kamar yadda ka ambata, sunana Habibullah kuma na san ka san hakan, kusancin da ke tsakanin ka da ƙanwarka kuma ai ya fi wanda ke tsakanina da kai, me ya sa ka tsallake ta ba ka tambaye ta dalilin ba ka zo wajena?"

Saleh ya ƙara fusata sosai kamar ya kai mini mangari, jiki na rawa yake nuna ni da yatsansa yana rattaba mini kashedi.

"Kalle ni da kyau ni ba sakarai ba ne da za ka raina wa hankali, kuma ina so ka sani wallahi ba ka ci bulus ba, wahalar da ka ba wa Salma a jiya ina maka albishir sai ka sha ninkin ba ninkin ɗin ta, don haka ka shirya, sai na gigita rayuwarka da duniyarka, sai na yafa maka mayafin sharrin da ba za ka iya yayewa ba."

Na fara kokawa da ɓacin ran da ke neman taso mini daga zuciyata, domin na binne shi kar ya bayyana a fuskata, na saki murmushin takaici. Na dube shi sai faman huci yake kamar wani kumurcin maciji, a nutse babu hargowa na mayar masa da raddin maganarsa.

"Kar fa ka manta shi sharrin da kake iƙirari ɗan aike ne, kuma yana koma wa wanda ya turo shi ne, ni a sauƙaƙe ma ina ba ka shawara ka canja wata hanyar da za ka taɗe ƙafafuwana, domin wannan ka riga ka kasata a faifai ka kassara lagonta. Zan kai ƙarar ka wurin Ubangijina Ya yi mini tsari da duk wani sharrin ka."

Da alamun jikinsa ya yi sanyi da jin raddina, ganin yadda ya ƙure ni da idanu numfarfashin da yake yi na raguwa, amma don kar ya ba wa mara ɗa kunya sai ya kaɗa kai ya bi ni da kuri.

"Dattin talauci da ƙuruciya ne suke damun ka, har suke zuga ka kake ganin karanka ya kai tsaikon da za ka iya jerawa da kafaɗata ka furta mini wasu banzayen maganganu, ka bar kumburi da ƙafafar kaurara zaton za ka haɗa ni da Ubangiji, tunda Shi ɗin  ba naka ba ne kai kaɗai na kowa ne, don haka bari murna karenka ya kama zaki, ka shirya domin wasan yanzu aka fara, sai na ga bayan ka Habibu."

MAYAFIN SHARRIWhere stories live. Discover now