complete book 🥺

29 2 0
                                    

*ABUNDA YAKE RAINA*

Fitowa nayi a harabar Makarantar bokonmu Dan zuwa ajin k'annena  Mira Shahida da Shukura, dan sunzo ajinmu Malaminmu ya koresu, shine na fito Dan zuwa wurinsu inji meya kawosu gurina dazu, hangen su danayi zaune a k'ofar makaranta yasa ni zuwa inda suke, Shahida na ganina tabtaso da sauri sauri gudu gudu tana kuka tana cewa wayyo "Anti kaina yana ciyo", ganin  Shahida ta rik'eni sosai Kuma tana hawaye, yasa Dasauri na tambayi su Meera hala me akayi mata ?, cikin rawar murya da tsoro Mira ke magana, tace, "anti wllhy maciji mugani nida Shahida abayi", "maciji Kuma"!!!? na maimaita cikin tsoro, Mira tace, "munje bayi Shahida na kan toilet sai maciji ya fito da kanshi, munzo guduwa ina a gaba nariga Shahida fita, kawai sai naji kan Shahida ya daki bangon bayin saina na rik'o hannunta muka fito, shine kanta yake ciyo", nace "me yasa bakuzo na rakaku ba"?, Shukura dake kusa dasu tace, "aimunzo malaminku ya koremu ni sai na wuce aji, sukuma sukaje bayin",  innalillahi wa Inna ilaihi raju'un, shine abunda bakina ke furtawa!!, "Wayyo!!  yanzu na gane dalilin zuwansu gurina",  muna cikin haka da su saiga Abba Najeeb kanin Walid babanmu yazo daukar su dansu nursery suke 12pm suke tashi, Nan na fad'awa Abbah duk abunda ya faru dasu, yayi ta'ajibin abun sosai ya rarrashi Shahida, suka wuce gida, ni Kuma na wuce ajinmu, kafin 1:30 pm yayi atashemu inbawa sauran 'yan uwana labarin abunda ya faru da su Shahida, ana tashi makaranta duk na basu Ummi labari kowa yaji tsoron faruwar abun, sai muka shiga school bus zuwa gida, na sauka a inda na saba sauka kullum, domin ni ba'a gidan Walid nake rayuwa  ba, tun ina k'arama Walid yabawa yayarshi ni, kasancewar ita bata haihuwa, Amma duk da haka nasaba da kowa na gidan Walid, domin a cikin gidan muke islamiyya,, washe gari muka hadu a inda muke shiga bus, nake tambayar su Ummi Shahida taji sauk'i?, Anan ne nake Jin labarin wai ashe Shahida taji ciyo a kafadar hannunta saboda buguwar, Kuma kanta bedaina ciyoba, ta cigaba da fadar yauma za'a kaita asibiti a duba ta, Jin haka yasa yau bayan muntashi makaran, na sauka a inda su Ummi ke sauka domin inje ta gidan Walid induba Shahida, zamu shiga layin gidan Walid kenan, saiga mijin yayar babana Dake rik'ona akan mashin, dukammu muka gaidashi, sai yace "Hadiza muje in wuce dake", a tunaninshi gidan shi zanje, Dan akwai tafiya zuwa gidan, ni Kuma inajin kunyar cewa ba can zanje ba, ba yadda na iya, sai kawai nacema su Ummi su tafi zan dawo yanzunnan, nahau mashin d'in muka tafi, ina shiga gidan , kayan makarantana na cire nasaka na gida, nafito da sauri duk tunanina shahida, dan Koda na dawo ban iske maman Hadiza ba wadda ke rik'ona, Kuma na tambayi yaran gidan tana inane?, sai suke fadamani ai tun dazu bayan na tafi makaranta hajiya kakarmu ta kirata tazo da sauri shahida ba lafiya, zan fita kenan sai kishiyar maman Hadiza ta fito daga dakinta, "Hadiza ina zaki"?, Nafad'a mata Shahida nakeso naje na duba bata lafiya, sai tace gaskiya sai kinyi shara dan yau kece dayi, kasancewar mu ukune 'yan mata agidan, idan wanna ta gyara gida yau wanna tayi gobe, na rok'eta data barni na tafi Idan na dawo sai nayi, tace bata yardaba dole sai nayi, ba yadda na iya haka na fara yin sharan inafushi Kuma ina sauri Shahida ce kawai a raina, saiga almajirin gidan Walid fuskarshi ba yabo ba fallasa, yace "Anti wai ummi tace kiyi sauri kizo shahida bata lafiya sosai kamarma zata rasu", Shima almajirin Yana magana sai hawaye yake, Jin haka yasa na saki abun sharar na ruga a guje sai kuka nakeyi inafar wayyoo Shahida karki  tafi kibarmu muna sonki, Koda na Isa an tafida ita asibiti, dan haka ban samu ganin ta ba, ji nake kamar nayi tsuntsuwa na ganni a asibitin, danni wllhy shekaran jiya nake tunawa da shahida tace dani, "Anti inayi dake saboda bakyaciyye mani abinci break",,, Shahida ce kawai nake gani tana yi mani gizo, kowa saikuka yakeyi agidan, ana haka saiga Kiran waya ana kuka sosai akace shahida ta rasu!!!!!!, kowammu kuka yake na tashin hankali, wasuma Suma sukayi tayi, ashema tunsuna a motar zuwa asibiti ta rasu Amma duk haka basu yadda ta rasuba, Saida suka karasa asibitin likita na gani yace ta rasu, suka binciki gawar anan akagane  sanadin rasuwar, likitoci bayan sunyi bincike bincike  sun tabbatar da cewa sanadin buguwar da Kanta yayi, Kashin kwakwalwarta ya tsage kwanyarta ta hade da jini, Koda ace Shahida ta rayu zatayi rayuwa mara dad'i, domin kanta yariga ya tab'u, jin wannan abu yasa iyayenmu  Jin takaicin rashin Kaita asibiti tun jiya lokacin da abun ya faru, kowansu ya tuna yarinyar dama fa tata fadar kanta yana ciyo Amma ba'a dauki abun da muhimmanci ba, tunaninsu normal ciyon Kaine da akasaba Ashe na ajaline!!!, daga nan suka dawo gida jiki ba kwari, da yawan mutane sai Suma suke, dan duk Wanda yaji shahida ta rasu abun na girgizashi, Domin yarinyar  nada shiga rai, ga hankali da tarbiyya da girmama na gaba, gata da son mutane, irin ya rannanne masu halin manya, gashi kwanaki goma suka rage muyi tafiya da Yan gidanmu duka zuwa senegal, Walid ya muna kayan tafiyan, Shahida na d'okin tafiyar sosai, duk Wanda tagani sai tace Walid yayi muna kayan zuwa Senegal cikin Jin dad'i da murna,, Ashe ba rabon taje,, bayan ankakawo gawar shahida aka wuce da ita dakin kakarmu mahaifiyar Walid hajiya, nikam khadija (anti) nakasa daurewa da rashin sake ganin shahida a raye, na shiga dakin ina kuka na rungumo gawar inafad'ar "Shahida tashi baki mutu ba", jin ba'a hayyacina nakeba yasa aka rika hanuna zuwa waje, muna zaune muna kallon iKon ALLAH saiga mutane sunfito da gawar shahida zuwa wurin Sallah zuwa mak'abarta, munji ciwon rashin ta Amma munsan ALLAH ya fimu sonta, bayan sati daya muka koma makarantar bokon da abun ya faru, kowa sai gaisuwar rashin 'yar uwarmu yake muna, Bayan Wani dan lokaci, da yake shugabannin makarantar sunsake daukar kwararan mataki akan malamai da masu kula da d'aliban makarantar nanis, Sannu ahankali har suka gane masukula da d'aliban nanis cutar da d'aliban suke, ta hanyar idan zasuyi masu tsarki suna tura masu yatsansu a gaba, suna Zane su da tsintsunya kafin su wanke masu kashi daidai sauran cutarwa daba'atunanin zasu iyayi,,, Wannan dalilin yasa iyayen tururuwar cire 'ya'yansu daga makarantar, Akarshe ma aka rufe makarantar saboda rashin kulawarsu,,, Da wannan nakejan hankalin iyayen yara Dan ALLAH akara kulawa sosai akan al'amarin yara.

Written by meeerarh
    A true life story🥺

Sadaukarwa ga 'yar uwata waleeda wacce narasa shekaru dadama dasuka wuce , Allah yasa me ceto ce , Allah yajikan magabata 😭I miss u so much my love , inasonki sosae Allah yahadamu a Aljanna

𝐴𝑏𝑢𝑛𝑑𝑎 𝑌𝑎𝑘𝑒 𝑅𝑎𝑖𝑛𝑎Donde viven las historias. Descúbrelo ahora