015

3 2 1
                                    

*WUƘA A ZUCIYA*

( _Bleeding Hearts)_

*015*

A fusace Umma saude ta miƙe tace

"Iyye Lallai Alhaji ka isa, shiyasa Kake Gaya Min Babu Sugar Tho zanga Wanda Ya Isa Ya Hana Auren Saleem Da Aisha "

Sosai Alhaji Naseer ya Tsorata da Ganin yanayin Matar tasa ,yana Tsoron kome zai Bata mata rai Amma har Ga Allah bayajin zai iya Aurama Ɗansa A'isha ba ,A'isha Itace Rayuwarsa Yana Tsananin Sonta Kamar yanda yake don rayuwarsa ,Yanajin koda Zai rasa Ransa ne bazai yarda wanin su ya Aure Ta ba, Ko Aareef Dinda yaba Izinin cigaba da neman ta ba hakanan ya barshi ba ,ya shirya masa Tsuggu kala-kala wadanda zaisa Ya fasa Aurenta da kanshi batareda ankai ruwa nesa ba.

Saita kansa yayi sannan Ya dubi matar tasa Daketa faman Xazzaga buhun bala'i yace

"Na Riga Na yanke hukunci idan Nine Mahaifin Saleem , Bazai Auri A'isha ba kuma na gama magana "

Dariya sosai Umma saude tayi harda tafa hannu

"Hhe Lallai Dr Ka Samu Courage,Ni zakay wa Gorin haihuwa?, da Alama Ka manta ko Ni wacece?, ka kuma manta matsayin Saaleem a gareka Ka kuma  manta deal Dinda ke tsakanin mu Akanshi You Forgot Every thing tho Idan Ka manta bari In Tuna maka.....!"

"Saudat....!"

Abba ya dakatar da ita da karfi, Ɗagowa tayi Ta kalli Cikin idanunsa da suka kaɗa sukayi jazir ,Shima kallonta yake da Rinnannun Idanunsa Da kallo ɗaya zakayi masa Ka fahimci sauyawan Launinsa Nada Alaƙa da Yunkurin rabasa da Ake Shirin Yi.

"Shekaru Talatin Kenan Da Muka Kulla wannan Yarjejeniyar a tsakanin mu,I have been Suffering on It for so long ,I can't Continue purnishing Myself On Something I don't Know ”

Dan Kauda kansa Yayi daga kallonta Yana dan cije Lips

"So Cancel the deal"

Matsowa Umma saudah tayi gab da dashi ta dafa kafaɗar sa  da hannaye biyu tadan matso Fuskar ta Gab da nasa cikin rada tace

"Ka fara Shirye Shiryen Auren Dan HUSSAINA da Ɗiyar Hassan ,If not Daga kai har almajirin dan Uwanka Hamza sai kunyi danasanin zuwanku duniya, Nasan komai ...!, so Have A nice day"

Ta qarashe zancen tana kalkadamata yatsu sannan ta fice A fusace

Binta da kallo yayi har ta fice sannan ya saki wani murmushin takaici wanda yafi kuka ciwo...

_Naseer Kaga abinda kaja ko? Kaga abinda kwadayinka da Son Zuciyarka yaja maka ko?_' Duk acikin zuciya take wannan zancen

Jingina yayi da bango yacigaba da juyawa ya maida idanunsa ya lumshe, zuciyarsa fall da baqinciki da Damuwa hadi da nadamar abinda ya aikata A shekarun baya da bai aikata Abinda za'a zarge shi ba da babu wanda Zai alaƙantasa da Mugun Abu, Har ya Bada 'ya'yansa Don Rufe Boyayyar Sirrin!, duk shi yaja ma kansa .

*Aareef*

Tun a hanya ya Fara Kashe Kudin da Aeesh ta bashi,  Kai tsaye Central Market ya nufa , Babban Shagon Siyarda Manyan Wayoyi ya Nufa ya bada Wayarsa Ƙirar iPhone 11pro max yayi ciko Aka bashi iPhone 13.

Yan Sauran Chanjin Da Suka Rage Kuma ya siyo Rabin Buhun Shinkafa da kayan Miya ya tari Adadaita Sahu ya kai masa Har gida,Cikin Kayan Abincin da ya siyo ya deba ma mahaifiyarsa Kadan Ya kaimata,Aikam Yasha sa Albarka Har saiDa Yayi kuka, Lallai mahaifiyarsa Na cikin wani hali yau Akalla Kwananki Uku kenan Bata samu tasa Wani abu a bakin ta ba, Sai ya kawo take samu taci ,Shi kadai Gareta batada Kowa, Gashi shi din in ya bar Gidan baya Dawowa Sai ya dauki akalla kwanaki Hudu ko biyar bai dawo ba ,Kafin nan Mahaifiyar tasa Ta gama Galabaita, Tsananin Yunwa Kesata fitowa Sometimes Tana Barar Abinda Zataci akan Titi, Gidan da take zaune Ƙaton Gida Ne sosai wanda Mahaifin Aareef ya bata Yace ta zauna tareda Danta ,bai yarda Wani bare Ko bako Ya shigar masa Gida ba dama Tun Lokacin aurensu Danginta suka Gujeta,ya kuma ce idan yaji labari sai ranta yayi mugun Ɓaci, Tasan Halinsa Shi yasa Bata Gayyatan Kowa, Shi kuma ɗan nata kwalli daya da Allah ya bata Yaji bazai Iya rayuwar Yunwa ba ,ya tattara inashi Ya koma Gidan abokai, Nan yake samun Naci, idan akayi Sa'a Ya samu Abu mai tsoka sai ya yankar mata nata rabon Ya kai mata .

Wuƙa A Zuciya 💔Where stories live. Discover now