SAUYIN RAYUWA(BA YADDA BATA ZUWA)

BY

UMMKULTHUM AHMAD

AKA AUNTY DIVAA

(9)

_______________

✨✨✨✨✨✨
💕💕💕💕💕💕
✨✨✨✨✨✨

Bayan dogon kuka da jinyar zuciya ta bawa kanta hakuri Dan ba yau farau ba ,shekara nawa ana Abu daya kullum ba sauyi?

Se sauyin da ita ya same ta?

Kuna mamakin inda iyayen Abida suke da duk kaunar dake tsakanin su,da suka bar yar su tana ta wahala a gidan Hashim?

Ku biyo ni cikin wannan labarin na sauyin rayuwa,zaku ga yadda komai ze dafi .

Cikin Abida ya samu watannin shi bakwai .Kuma a har lokacin C's ake mata .shi yasa ma likitoci sun bata zabin hutu daga wannan haihuwa tata saboda gudun matsala.

Sannan a har yau Babu abunda ya chanja daga rashin kula da lafiyar ta daga wajen Baban Abul.

Shi yasa ma har yanzu ba ko yaushe take zuwa antenatal ba,se sanda ya ga dama ya Bada kudin Mai Tai zuba a motar ta.

Mai har na dari uku  zuba Baban Abul ya bayar ta zuba a mota.yarinyar da ta Saba yawo da full tank a cikin gata ga askafuna.

Yanzu kuwa ana Saka Mai na dari uku da dari biyar Yaya za'a kunna wata Ac?,da taci sa'a ake bata na Mai ma ai se ta gode wa Allah..

✨✨✨✨✨

Tana kwance a dakin ta tana ta Jin kwadayi a ranta..kwanaki dama da suka je gidan Hajiya ne fa suka hadu da yaya () wan  su Hashim shine ya ba wa Yara dubu hudu.

Duk suka bata suka ce basa so,hatta Nabila bata nata tayi.

Kawai se ta ce bari na fara gwada yin meat pie me suna chofe Wanda ake yin shi fale fale da naman shi kamar hanjin bera din nan me garas garas ..

Bata hi shawara da Baban Abul ba domin shi Kuma Wani Hali nashi ko dubu miliyan zata samu baya taba dora idon shi a Kai ,kunga dai in mutum yayi a fada.ko da ta gaya masa an bawa su Abul kowa dubu guda ba abunda ya shade shi.

Shidai nashi ne baze bayar ba.

A cikin unguwa aka siyo mata komai na bukata ta fara chofe,dake akwai Yara a anguwar rututu tunda akwai Yan gargajiya sosai a anguwar ,se ta bawa Sarauniya ta Kai islamiyya ta ajje a kofa.shi kenan ta fara cinikin chofe

Hashim na gani ya hau masifa da bala'i yace tana zubar Mai da kima a cikin unguwa ta wulakanta shi ace duk girman gidan nan da kudin shi da komai,Kuma se tayi Wani Sana'a?

Ba dan ranta yaso ba dole ta Daina ,dama shi baya so ana zuwa Mai gida bare wasu Yan unguwa .

Dan sau daya aka Kai islamiyya shikenan da an tambaya se suce a gidan su ne ,dama ta bayar an Kai islamiyya ne dan mutane su gani..toh Malam Hashim dai yayi Karan tsaye ya Hana .

Allah ya sawwake..

💞💞💞💞💞💞💞

Saudatu wato proff na daya daga cikin daliban da ake ji dasu a primary five saboda kwazon ta .

Wannan dalilin yasa sanda suka zo zana entrance examination aka Saka sunan ta a jerin sunayen mutum biyar na makarantar su da aka zaba zasu zana scholarship exams

Abul Akai wa wannan bayanin sukai ta murna ance musu Indai suka ci za'a dauki nauyin karatun su ..

Ko da suka zo gida da wannan bayanin ba karamin dadi Abida taji ba.

SAUYIN RAYUWA ✅Where stories live. Discover now