1

83 2 0
                                    

*Karamci Writers Associations*
   [Karamci shi ne tushen mu'amala tagari.]

Vote @ wattpad khairi_muhd.

*MUGUN MIJI*
_(rayuwar Aurena)_

_wannan labarin kirkirarran labari ne, ban yi dan labarin wata ko wani ba._

_Gajeren Labari._

Yan kasuwa ga babbar dama a gareku,ku zo ku tallata hajarku ko group dinku na kasuwanci a cikin farashi mai rahusa. Ku tuntubi wannan number 👇👇👇👇👇

_09065856251. Domin more wa garabasar ta ku._

           _1_

_____________________

Yanayi na hadari da ya had'u a lokaci guda had'e da iska mai karfi da ke tashi ya sa yawancin masu tafiya da k'afa d'aga kafa har ma da masu hadawa da gudu_gudu domin karasawa gida don tsoron saukar ruwan a kawunansu. Masu yar karamar treda ma na kokarin harhada kayansu don kulle shagunansu.

Can gefe kuwa na hango wata mata da yara biyu a rakube jikin bangon wani gida suna rawar d'ari gefensu kuma jaka ce da gani ta kaya ce.

A iya yanayin su zaka san cewa babu wuya a jikinsu ko wahala sai dai koma meye ya fito dasu a wannan yanayin ba karami ba ne ba domin sutturar jikinsu ma mai tsada ce da tsafta.

Matashiyar zata iya kai wa shekara ashirin da biyu zuwa da uku , yayin da yaran mata guda biyu masu tsananin kama da ganinsu ka ga yan'biyu (Twins) zasu kai shekaru takwas a duniya cikin shiga iri daya tun daga sama har k'asa daidai da takalmansu ma iri guda ne kamar tasu ta 'baci haka yasa ma na gano identical twins ne. Farare ne kyawawa dasu Ma Sha Allah.

Yayyafi ne ya fara sauk'a hakan yasa ta kuma kama yaranta ta rungumesu a jikinta tsam kamar za a kwace mata su ji take yi ina ma ruwan zai sauka a iya kanta ne ba tare da ya taba mata yaranta ba.

"Mummy mu tafi gidan gun Daddy dan Allah kin ga fa ruwa za ayi kuma kin ga Afra bata son ruwan sama ya taba ta."

"No Mummy! Ni ba zan je gun Daddy ba bayan Daddy baya son mu ya kore mu daga gidanmu ba saboda wannan matar ba? Ni dai Mummy bana son Daddy mu ma yace baya son mu."

Wasu hawaye ne suka zubo mata a fuskarta. Hawaye ne da suke nuna tsantsar tashin hankali had'e da danasani da tausayin kansu gaba d'ayansu. Ina ma zata dawo da hannun agogo baya ina ma zata iya cire babin rayuwarta da ta......"  Jijjigata Afra tayi ta na kuka "Mummy fitsari zan yi."

Juye_juye ta soma yi dan neman inda zata sa Afra tayi fitsari saidai bata ga ko ina ba. Da kyar tace da Afra "ki bi ta nan kiyi a cab gurin Amra kiyi covering dinta tayi fitsarin." Ta dauko water bottle ta basu "kiyi tsarki in kin gama."

"To Mummy."

Cikin mintuna da basu wuce goma ba ruwan ta sauka da karfin shi kamar da bakin k'warya hankalin ta ya kuma tashi wani irin tsoro ya lullubeta saboda duhun da gari ya fara ga yaranta basa son duhu "kaicona" shi ne abin da ta fad'a a fil.

A hankali motar ke shigowa cikin layin hasken fitilar ce ta galle mata idanuwanta. Hannunta ta saka ta kare fuskarta.

"Dear kamar mutane a kofar gidanmu."

"Yes na gani Habibty sai dai anya kuwa lafiya?."

"Dan Allah mu shigar dasu ciki kalli kamar ita da yara ne garin ba dadi kar su samu wata cutar."

"Shi kenan bari mu shiga sai Alaza yazo ya shigo dasu ciki."

"Ok Dear."

Bayan maigadin ya bude musu sun shiga ya umarce shi da ya kira mutanen da ya gani a bakin gate.

MUGUN MIJI. (LABARIN AYSHATUL_IMILI).Where stories live. Discover now