4

22 0 0
                                    

https://www.facebook.com/110308337320465?referrer=whatsapp.

Yan kasuwa ga babbar dama a gareku,ku zo ku tallata hajarku ko group dinku na kasuwanci a cikin farashi mai rahusa. Ku tuntubi wannan number 👇👇👇👇👇

09065856251. Domin more wa garabasar ta ku.

Typing__________5.

Kwafa Hannar tayi ta koma kujera ta zauna a fusace ta dauko kwalin tabarta mai tsada ta dinga busawa nan da nan idanuwanta suka ji jajir dasu ta sha ya kai guda goma a wannan lokacin har sai da kawarta Asy ta kwace ta wullar tace mata "Ke meye haka?."

Ihun kuka ta saki ta ce "Baki ga abin da ya yi min ba ne? ." Jikinta sai rawa yake yi tamkar dai wata tababbiya haka ta koma musu da kyar Asy ta lallabata ta nutsu ta kwantar da hankalin ta wata allura ta dauko ta tsira a jijiyar hannun ta nan da nan duniyar ta dinga juya mata taji wani irin dadi tayi luff a kan kujerar sai barci ya dauke ta.

*

Isar shi dakin shi ke da wuya ya shige bandaki ya watsa ruwa yana fitowa ya yi tunanin cewa Hanna ta kawo mishi coffe din sai dai bai ga coffe balle Hanna, tsaki ya yi ya gama goge ruwan kan shi da jikin shi ya sa ka jallabiyarshi ya dauko laptop din shi.
Script din ya cigaba da dubawa dake script writer ne babba, kasa gane komai ya yi ya koma da baya ya kwanta a jikin gadon ya kulle idanuwan shi yana jin kan shi na cigaba da Sara mishi.

Kwana biyu kawai ya ji a jikin shi bai san da gaske Imili rayuwarshi bace ba sai yanzu da babu ita a tare dashi ya dauka da gaske zai iya rayuwa babu ita ,ya dauka da gaske baya bukatar ta din kamar yadda ya fada gashi yanzu duk ya bata komai me yasa ya biyewa Hanna har suka yi abin da suka yi din?, Me yasa bai cigaba da boye dangantakar sa da Hanna ba har ya bankadata ta ji ta gani kuma ya koreta bai taba tsamanin haka ba ya yi messing up.

Karfe goma na dare ya tashi ya sauka falon haske tar ga falon kace kaca da chips, robobin lemo da sauran tarkace dai, ko wacce kujera kuma da kawar Hanna a daya daga cikin kujerun kuma Hannar ce ga tullin karan sigari a kasa da yawa ga allurar drugs da take yi wa kan ta wani irin takaici ya kama shi ya daga goshin shi tambayar kan shi ya yi yace "Why?". Kitchen ya shiga ya dora karamar tukunya ya dafa indomie ya soya kwai ya hada coffe din ya tafi dinning sai da ya ci ya koshi sannan ya haura dakin shi yayi sallah ya kwanta saidai barcin bai dauke shi ba ya fada wani tunanin daban.

"Kai Mugu ne , ka yaudareni,ka rabani da kowa,ka hanani yin komai a rayuwata ni kuma saboda son da nake yi maka idona ya kulle na biye maka, duk abin da ka ke yi min bana damuwa ina cinyewa saboda ina son ka ashe ni kadai nake haukata abin da ka yi min Allah Ya yi maka Allah Ya isanmu ni da Yarana kai da farin ciki kun yi bankwana kai da kwanciyar hankali a rayuwarka har abada wannan daga can cikin kasan raina nayi maka wannan adduar,addua ce daga wurin uwar da aka cuci ya'yanta....."

Tashi ya yi firgit ya dafe goshin sa yana jin sanyi na shigar shi a karo na ba adadi ya kuma furta kalmar "Why?."

*

"Adda hankalina ya kasa kwanciya adadin yadda nake tunanin Imili ya yi yawa na san akwai matsala dan Allah ko za ki je min gidanta ki gani?."

"Haba Amma, wane irin inje gidan Imili ko kin manta bamu da wannan ikon kuma bamu da izini daga wurin Abbu ba? Tayaya kike so mu karya mishi doka? A matsayina na babba a gidan nan."

"Adda me yasa ba kwa mantuwa? Me yasa ba ku da imani ne? Me yasa ba ku da tausayi? Imili nawa take ? Shi kenan saboda kuskure daya tak sai a yanke alaka da ita? Shi kenan kuje kuyi yadda kuke so ni zan je da kaina ince dai karshen abun Uban ku ya sake ni to na yarda zan bar muku gidan ku in zauna da 'yata da jikokina." Ta karashe tana kuka.

"Innallillahi wa inna illahir rajun, Amma kiyi hak'uri dan Allah Wallahi ba nufi na kenan ba kiyi hak'uri zan kirata amma kin san abun da Abbu ya fada a kan duk wanda yaje gidan Imili ko ya nemeta kiyi min uzuri dan Allah."

Tashi tayi daga falon gaba daya ta shige dakinta ta kulle tayi zaman dirshan a kan gado tana kuka. Wayarta ta dauko a karo na ba adadi ta danna number Imili ta dinga kira amma kamar ko yaushe *Switched off.*  "Ya Allah ka kare min 'yata a duk inda take , Ya Allah ka ga halin da nake ciki Allah ka kawo min dauki da sassauci a cikin wannan alamarin Ya Allah ka dubemu."

*

"Wallahi in kaga ka fita daga gidan nan kudina ks cake min tas a hannu na babu ragi babu dadi sai an biyani hakkina ehe,mutum kullum sai mak'on bala'i to yau baka isa ba tas sai ka bani kudi ne ko in da ayi maka dan buro'uban duka yau a gidan nan."

"Ni za ki tarawa mutane yau kuma? Harda duka ni din lallai wuyan ki ya isa yanka in ba ni ba waye zai kula ki? Jiki duk kin tsofe kin zama ba kyan gani a kan wasu yan kudi kike gaggaya min magana harda za ki sa a dakeni ni dai ni Alhaji Yahaya za ki sa a daka to kan a dake ni ni zan dake ki dan uwarki da ubanki da suka kasa baki tarbiya."

Ta sa hannu a baki tana bubugawa ya dinga bada sautin wulwululwu irin abin nan na yara "Shege ka fasa Yahaya , ko baka ji ba nace shege ka fasa dan uwar da ta kawo tsinane duniya marar albarka."

Nan fad'a ya kaure harda kulle kofa Saida suka timi juna sosai karshe ma dai Yahaya ya yi mata duka sosai duk ya fasa mata jiki har bata motsawa sannan ya dauko kudin ya watsa mata a fuska yace "Mayya akuya ." Yayi ficewarsa daga dakin ya barta a wurin tana nishi a hankali.

"Wallahi sai na ga karshen ka Yahaya."

*

"Tun da na fara aiki a gidan su Hajiya bani da matsalar abinci , kuma ban kuma ganin matar da tayi silar samun aikin nawa ba balle nayi mata godiya, kuma bana ganin kowa a gidan saboda asalin yan boko ne ko gilmawa basa yi. Sai dai Hajiya Babbar wani lokacin ma muna zama muyi hira ni da ita tana da barkwanci ni ke mata komai hatta gyaran dakinta da wankin bandaki Allah Ya had'a jininmu ni da ita sosai kuma ta yarda dani.

"Wai ko Sa'ada ke yar ina ce?."

Wannan tambayar ta fama min wani mik'i a zuciyata na ji ina son yin kuka sosai na dade ban ji wannan tambayar ba "shin wai wacece ni kuma daga ina nake?."

"Hajiya Babba kiyi hak'uri ki bani lokaci zan gaya miki wacece ni kuma da kuskuren da na tafka wanda har yau nake danasanin yin shi."

"Shi kenan na baki lokaci da dama Allah Ya kaimu da rai da lafiya."

"Amin Hajiya."

*

"Sunana Khadija Ibrahim . Yaya sunan ki?."

"Sunana Ayshatul_Imili Kabir."

"Yanzu mun dauki tsawon sati guda tare na tare da mun san komai a kan junanmu ba, dama na baki lokaci ne dan ki huta ki kuma nutsu kuma naga kamar yanzu ni da ke zamu iya yin magana da junanmu , tun da na ganki naji kin kwanta min a raina nake miki kallon kanwata, haka ma maigidans yayi min umarni da in taimake ki, bazan iya taimakonki ba har sai kin fad'a min wacece ke kuma me kike yi a nan? Wane irin abu ne ya sa kika bari gida da yaranki a cikin yanayin da na ganki."

Hawaye ne suka cigaba da yin sintiri a fuskata.

"Kar ki damu ba sai kin gaya min yanzu ba in ba kya son in sani amma ki sani bazan taba iya yi miki komai ba muddin ban san ainihin damuwarki ba ki yarda dani zan taimake ki ni cikakkiyar lauya ce me kari hakkin mata a karkashin hukumar Human rights."

Saurin kallon ta nayi ina mamaki , matar da ta taimakeni ta bani wuri bata san ni ba balle wani nawa ba ai ya kamata na gaya mata wacece ni.

"Zan gaya miki labarina domin ina son masu irin halina ya zama musu darasi a rayuwa.

Kamar yadda na gaya miki sunana Ayshatul_Imili Kabir ni haifaffiyar garin Kano ce..........

_A nan na kawo karshen free page na littafin Mugun Miji,daman na gaya muku gajeren labari ne da ke dauke da darasi kala_kala, domin samun naki ki biya naira dari biyun ki kacal #200._

*Littafin Mugun Miji na kudi ne. Ki biya naira dari biyun ki kacal ki samu shiga group din paid novel.*

*Za ki iya biyan kudin ki ta wannan account din.*

👇👇👇👇👇👇👇👇.

*2098372249*.
*Uba*.
*Sani Ummulkhairi panisau.*

*Ko kuma ki turo katin waya na mtn ta wannan layin.*

👇👇👇👇👇👇👇👇
07042058317.

*Za ki turo shaidar biya ta wannan layin.*

*09065856251.*

MUGUN MIJI. (LABARIN AYSHATUL_IMILI).Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ