Part 2 chapter 2

157 6 0
                                    

Daga qarshe ta ce su shiga cikin kwaryarsu su kwanta  suka shiga suka kwanta luf.
      Sannan ta dube ni ta ce in sauko sun yi bacci. Na sauko yayin da hannuwana da qafafuwana dukka sun kunbura sun yi jajawur.
     Ta ce in shiga bandaki in yi alwallah in yi sallah, ga shi har la'asar ta yi ita hutun sallah take, kada alhakin rashin sallata ya kamata.
     Na ce nima bana salla hutu nake. Saboda fatana ta bude min qofa in fita kawai.
     Ta girgiza kai ta ce "mafita daya ki yi duk abinda na ce ki yi, idan kina yi min gardama wallahi sai na cika falon nan da mucizai ga su can cikin daki. Na san kina sallah ki wuce ban dakin falo ki yi alwallah ga sallaya da hijab ki yi sallah sai mu dora daga inda muka tsaya."
     Na tafi qafafuwanta sun kasa tsayuwa waje daya sai rawa suke saboda jigata. Na leqa bandakin na ga babu muciji, daman fitsari ya cika min mara na yi ta addua sannan na tsugunna na kama ruwa, na yi alwalla ban sani ba ma ko na yi daidai oho. Na fito ta bani hijab na saka na fara salla ina yi ina waiwaye dan kada ta sakar min miciji.
   Raka'oin ma ban kirga ba ina ta yi ina sakewa har sai da ta ce min sun isa. Na daga hannu sama ina ta karanto "la'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalumin" a bayyane ita kuwa  tana amsa min da Amin. Muka shafa.
     Na sake zuwa gefenta amma daga nesa nesa durqusa ina magiya akan ta bar ni in tafi gidana.
      Ta ce komai ya wuce amma bata da 'yan taya hira nice zan taya ta zama. Kuma tana jin yunwa abincin data dafa, ni na sa ya qone dazu dan haka in shiga kicin mu yi girki tare.
      Na fasa kuka na ce "wallahi ban iya girki ba"
       Ta ce zata koya min yadda ake farfesu da naman miciji. Na kula duk wata kalma da zata tayar min da hankali ita take fada min in ba haka ba ai ta sani ta tayaya zan ci naman miciji. Na tabbatar matar nan yau ba zata bari in tafi ba sai na saddaqar da cewa kiyamata ta zo dan haka na yi sabuwar kalmar shahada na dora da istigfari.
      Fargaba daya ita ce zan mutu mijina yana fushi da ni. Kuma ban yi masa sallama ba ban yi sallama da yarana ba. Na san ko da na fito daga gidan nan a raye, da alama a haukace zan fito ba zan qara yin hankali ba kuma. Na ga abinda ido bai taba gani ba, an kai ni inda bil-adama bai taba zuwa ba.
      Da alama wannan matar ko a cikin matsafan ma babba ce, kungiyarsu ba a qasar nan kadai ta tsaya ba ta hada da matsafan turai da china da India.
      A gaba ta sakani muka shiga kicin ta bani kayan miya da albasa ta ce in gyara mata, hannuna na rawa ina yankawa, dan rainin hankali wai hira take yi min, har da dafa kafadata tana min magana mai dadi.    Ta ce " Fatiti shin sanda na zo ganin gidan nan ni da Bar. Ibrahim abokina ba ke ce kika dage akan sai na zauna a sama kusa da ke ba? Safiya ta dage sai na zauna a qasa tare da ita, kika jawo hannuna muka hau sama kika ce anan zan zauna ba?"
    Na gyada kai na ce " an yi haka."
    Ta ce "me yasa daga baya kika tsane ni, kika min qazafi, kika harhada min tuggu, har ki na fatan in tashi?"
    Na yi shiru wannan karon wata qatuwar wuqa naga ta daga sama kamar zata caka min kamar kuma zata yanka naman da ke hannunta.
    Na zabura na ce "na dauka ke matar aure ce wannan mutumin mijinki ne, shine na so ki zauna kusa da ni ki koya min yadda zan yi tattalin mijina dan na ganki a waye. Daga baya na gane baki da aure sai hankalina ya tashi."
    Ta gyada kai ta ce "na zargi hakan nima. Amma me yasa za ki tsani mace dan bata da miji? Allah ne  bai bata ba. Ita bata taba nuna alamar tana son mijinki ba kuma. Shin baki yarda da kanki ba ne kina ganin zai fi sonta da ne?"
      Na yi wuqi-wuqi da ido na kasa amsa mata. Ta bani balander ta ce in markada kayan miya sannan ta hada ni da yankan tafarnuwa, gashi bana son warin tafarnuwa haka dai na dinga yunkurin amai na dage sai da na kammala.
    Ta na jero min tambayoyi akan Usman wadanda ban isa in qi amsawa ba, idan na yi shiru sai ta kalli kwaryar mucizan nan da suke falo daga nan sai in bude baki.
     Ta na tambayata ne wanne dadin zama na ji da mijin da yake marina da har nake kishinsa? Saboda fari ne tas? Dan gayu? Dan boko?"
    A dole na ce mata "eh hakan ne yasa?"
    Ta sake maimaitawa ta ce "sai dai ni baya burge ni kuma ma na ji na tsane shi saboda yana da girman kai da ji da kai."
     "Hamdala na yi a cikin zuciyata, na ji hankalina ya kwanta.
      Ta dafa mana fried rice, na ce ba zan ci ba ta ce ai dole ne ba roqona take yi ba. Muka hau kan dining table muna ci gami da juice da yankakkun fruits. Yayi dadi abinci amma na kasa tantance me nake turawa ma, daman akwai tsohuwar yunwa a jikina tun ta jiya. Kuma ta tabbatar min sai na cinye tas idan ina so in bar gidanta.
      Ta na ci tana kallona fuskarta cike da murmushi, ta sa hannu ta shafa gefen kumatuna ta ce Allah sarki duk kin kode, fuskarki ta yi jajawur saboda kuka.  Ki na tsoron mutuwa ne? Na zaci kin sadaukar da rankin gaba daya wajen yaqin kwatar mijinki. Ga ki mai kyau dake amma ki na ta zalumtar rayuwarki, kin qi ki hutawa zuciyarka. Kin san da cewa tunda na ganki farkon ganina da ke na ji ina so mu yi qawance da ke? Saboda  kina da fara'a da wayo da iya hira da Jan mutum a jiki. Sai daga baya na ga ashe duk ba haka kike ba. Na shaqu da yaranki ina sonsu, Haidar in ya ganni sai ya kwanta a jikina yayi shiru in rungume shi sai in ji sanyi a raina amma gaba daya kika raba mu. Fatiti ki na nufin zan yafe miki yadda kika cutar da zuciyata akan abinda take so?"
   Na quara mata ido ba tare da na san amsar da zan bata ba, tabbas ta nuna min qauna ni da yarana a dole na   bar ta.
     Ta surnanao da hawaye ta ce "da kin san labarina da za ki gane cewa a cikin tsarina bana qawance da bil-adama saboda irin wannan matsalar ta ku."
     Kawai na ji na kware saboda firgice, sai ta taso ta dafa ni tana dukan bayana ta bani ruwa na sha.
      Ni dai gaba daya na sake firgita dan na ji tana ambaton bil-adama kuma  tana killace kanta daga mu.
     Na tamabaya cikin gigita "ke mutum ce ko aljana? A ina nake yanzu?  A bayan duniya ko a cikin duniya?"
    Ta yi dariya har da kyakyawa ta ce " a ada ni ba mutum.ba ce ina tunanin yanzu na zama mutum. Dazu bakya cikin duniya amma yanzu kin dawo cikinta."
     Na fada a bayyane "innalillahi wa inna ilaihi rajuun Ya Rabbi ka dauki raina akan in ci gaba da rayuwa a cikin aljanu. Mufidah ba ki da tausayi ne? Dan Allah ki bar ni in tafi cikin 'yan uwana bil-adama. Na ce na tuba, na daina damunki.
     Ta yi dariya ta ce " ba ni na kawo ki ba fa ke kika shigo ko iso ban yi miki ba, babu sallama kika bangaje ni kika shigo.Wallahi mai fitar da ke daga gidan nan sai ya shirya ki ci gaba da addua kawai."
    Na sake fitar da rai daga sake ci gaba da rayuwa, na fashe da kuka ina sharce majina da tulin tissue din da ta kawo min har katan daya.
    Ta na cin abincinta a nutse tana yi min hira da alama tana cikin nishadi irin wanda ban taba ganinta a ciki ba.Tabbas na san yau ranar daukar fansa ce a wajenta ni kuma a wajena ranar da nake girbar abinda na shuka ne.
     Ta kalle ni ta yi murmushi ta ce " na san kin tsane ni ada, a yau kin sake jin tsana ta amma ba komai daman bana buqatar soyayya daga wajen mutanen da basu san darajarta ba. Kuma ko mahaifiyata na soya na ba ki ba za ki so ni ba, kin cusawa mijinki hakan a ransa.
     Gashi ba ni da niyyar tashi daga kusa da ku kamar yadda ba ku da niyyar tashi ku bar ni kenan mutu ka raba ni da ku.
   Da farko har ga Allah gidan nan bai yi min ba saboda bana son zama ya wuce flats 2, na ga nan har mu hudu ke kika dinga roqata a dole na yarda musamman da na ganki da 'yan yara, gani da son yara na ce zasu dauke min kewa amma daga qarshe kika gudu kika bar ni kamar marainiya, ba ki bar ni da takaicin ma kadai ba, kika hada da tsana da sharri."
    Na sunkuyar da kai dan na fara jin nauyin maganar da take fada, kuma na gasgata an yi.
     Da na ga babu sarki sai Allah babu wata mafita banda in zauna mu yi hirar ko Allah zai sa idan ta gaji da surutun zata bar ni in tafi.
    Sai na tambaye ta na ce  "bani labarinki. Ina so in san ko ke wacece?"
Kallona ta yi ta yi murmushi ta ce "anya kwakwalwarki zata iya daukar labarin Mufidah? Akwai tsoro sosai da firgice a cikin labarina fa.
      Ko da yake duk duniya ke kadai kika taba sanin wani abu daga cikin yadda rayuwata take dan haka ke ce babbar aminiyata bani da kamarki yanzu.
    Ko Murjanatu Bibi bata taba sanin abinda kika sani ba dan ke ganau ce ba jiya ba."
    Na gyada kai na ce "tabbas ni ganau ce ba jiyau ba ce, na ga abinda na gani, na ga abinda ban taba gani ba."
      Sai ta kwashe da dariya tana tafa hannu amma fa dariyar ba irin ta hankali ba ce, kuma ba irin ta mutane ba ce.Tun ina ganin ba damuwa ba ce har ta fi qarfin tunanina.
     Na razana na miqe tsaye zan nemo mafaka, sai ta damqo ni ta mayar da ni ta zaunar.
    Wannan karon gumi ne ya keto min na tabbatar ba gumi ne na haka kawai ba saboda A.c a kunne take kuma ta dauki sanyi, na fi zaton gumin daukar rai ne ya tunkaro ni.
[7/24, 5:16 PM] Jamila Umar Tanko: 17

      LABARIN MUFIDAH     
      Sunana Mufida Hamza, mahaifina dan asalin garin Bauchi, bahaushe ne. Sunan mahaifiyata Khadija 'yar qasar Habasha ce wato Ethiopia.
     Wani aiki na shekaru biyu ya kai mahaifina qasar. Ya hadu da ita tana qarama, ya aure ta. Acan su ka fara zama, da zai dawo ya taho da ita a lokacin an haifi yayana Imam Malik.   
      Daman ashe yana da wata matar anan Nigeria amma ya boyewa mata da ita da danganta domin ya san idan ya fada ba zasu bashi aurenta ba kuma ba zasu yarda ya taho da ita ba.
      Sunan matarsa Hafsat, sun dade tare har ma a lokacin su na da yara hudu dukka maza, yaran su na kiranta da Mummy.
     A lokacin shi da iyalansa su na zama a Lagos anan yake aiki matarsa ma Mummy tana aiki anan tana koyarwa a jami'ar Lagos. Babbar mace ce mai ilimi dan a lokacin da suka yi aure ma ita da mahaifina sa'anni ne, kuma a shekara daya su ka gama karatu.
    Gida daya ya kawo mahaifiyata ya hada su kasancewar babban gida ne mai bangarori daban-daban. Hakan bai hana Mummy neman rigima ba saboda baqin kishi wanda ya wuce misali.
      Da farko ta fara fada akan ya boye mata auren da yayi ya ci amanarta, na biyu ya auro yarinya qarama 'yar cikinta, na uku kyakykyawa ce irin kyawun nan na gani na fada. Abin ya sake ninkuwa da ta ga yadda yake   tsananin qaunar mahaifiyata fiye da kowa da komai.
     Shi kuma bayanin da yake yi shine Khadija tana bashi tausayi ne saboda ya kawo ta qasar da  bata san kowa ba sai shi mijinta kadai ta sani dole ya kula da ita. Ko Hausa ba ta iya ba sai dai  turanci da yaren na 'yan Habasha.
    Idan daddy ya fita wajen  aiki, sai Mummy ta je bangaren Khadija ta yi ta masifa, bayan zagi har da duka, wataran ma har da yaranta suke haduwa su yi mata duka
   Mahaifina yana daukar mataki amma fada kawai yake yi da gargadi, gobe ma zasu sake.
      Mamana ta sake samun cikin yayana Umar sai ta ce a qasarsu take so ta je ta haihu. Shima ya san babu mai kula da ita anan, dan haka sai ya amince ya dauke ta ya kai ta gida. Ya bar mata komai da komai da zata buqata na haihuwa, ya dawo Nigeria.
   Bayan ta haihu ta yi arba'in sai ya je zai dauko ta su dawo, nan fa ta ce ba zata bi shi ba. Sai a lokacin ta fadawa danginta cewa yana da wata matar har da yara guda shida, kullum duka take yi mata.   
     Su ma suka goyi da bayanta su ka ce ba zata dawo ba. Shekara da shekaru ya dinga sintirin zuwa yana ta magiya akan ayi haquri ta dawo zai canja mata gida ta zauna ita kadai, amma suka ce ba zata  dawo ba.
    A zuwan da yake yi ne tunda da akwai igiyoyin aure  a tsaninsu, sai cikina ya bayyana dan haka aka harhado ta aka dawo Nigeria da ita dole.
     A garin Lagos ne amma da sharadin zai canja mata gida. Bayan wasu watanni aka haife ni, ni ce kadai macen da aka fara haifa a cikin maza takwas. Mummy na da yara maza shida na mamana maza biyu. Masha Allah zo ka ga murna a wajen mahaifana.
     Cikin ikon Allah gaba daya yaran gidan kakaf da mahaifinmu muka yi kama.Ya dauki son duniya ya dora min fiye da sauran 'ya'yansa, nan fa Mummy ta saka baqar lamba akaina duk duniya babu wacce ta tsana irina.
     Gidan kowa daban amma sai ta taso ta zo neman rigima gidanmu, duk da an yi rubutu a tsakaninsu cewa kada ta sake takowa in da take balle ta doke ta amma fa sai ta zo din.
      Da mamana za ta je garinsu ganin gida ya ce ba zata tafi ba, dan in ta tafi ba zata dawo ba.Ta ce sai ta tafi dan haka sai ya dauke ni ni da Yayana Imam Malik ya boye, its kuma ta tafi da Umar. 
      Ashe wannan tafiyar ta tafi kenan, qarshen auren ya zo. Shima ya yi fushi bai bi ta ba, su ma basu yi magana ba.
     Tun ana waya aka daina, sai ya tura mata da takardar sakinta bayan wasu shekaru. Ina da shekaru uku a lokacin  ya mayar da mu wajen matarsa, anan suka dinga gana mana azaba. Ya san da haka dan haka da aka tura shi wani aiki na shekaru  garin Jalingo sai ya ga ba zai iya barina ba. Ya dauke ni ya tafi da ni ba tare da ya san yadda zai yi da ni ba amma ya bar Imam malik a gidan. Duk wata wahala da azaba ta duniyaan ganawa yaron nan, wato mummy da yaranta. Amma akwai Allah.
    Mufidah ta yi shiru yayin da idanuwanta suka cika da hawaye.Ta dago ta dube ni na buga tagumi ina jinjina irin wannan badaqalar rayuwa.
    Ta qura min ido tana kallo, kallo irin na su na mayu.
     Ta ce "shiyasa gaba daya kike bani haushi saboda irin kishinki ya yi kama da na matar Ubana. Baqin kishi, baqin hali, baqin zargi, hayaniya, zage-zage. Kullum a haka take, mahaifina baya hutawa kamar yadda Usman dinki baya hutawa. Kun mayar da kanku kamar mahaukata, kun zubar da imaninku gaba daya, dan komai za ku iya yi akan mijinku."
    Na sake nutsuwa don kada ta hada ni da baqin mijici. Na yi kalar tausayi da nuna alamar nadama. Amma na matsu na ji ci gaban labarin nan ta yadda ta rayu da uba da yadda ta koma rayuwa a cikin aljanu.
     Mufida ta kurbi lemo ta dube ni ta yi murmushi ta ci gaba da cewa "rayuwa daga ni sai ubana a garin da babu dangi akwai wahala. Shi yake yi min wanka, ya dafa min abinci, ya yi wasa da ni. Ya saka ni a mota mu je wajen aiki tare.
     Idan zai je Lagos wajen iyalansa sai ya taho da ni amma a garin Ibadan yake ajiye ni a gidan qanwarsa, ba ya yarda ya qaraso da ni gidan. Saboda tsabar tsanar da Mummy ta yi min, abin ya baci kuma ta koyawa yaranta irin wannan hali. Ko Imam Malik ma makarantar  firamare da sakandire ce a hade amma ta kwana ya kai shi saboda zaman gidan ya gagare shi. 
      Mun fi shekara a haka, damarmaki da dama sun zo masa a wajen aiki, haka yake haqura da kudin da zai samu saboda ni ba zai iya yin tafiye-tafiye ba, kuma bai san in da zai kai ni ya ajiye ba.
    Shekaruna biyar a lokacin, ina matuqar neman qawayen da zamu yi wasa tare dan haka kullum ina leqe ta windo ina kallon yara masu wucewa, su na ta bani sha'awa. Gidan da muke akwai bishiyoyin kwakwar manja da yawa har guda casa'in da shida, sun gazaye gidan gaba da baya.
     Bishiyoyin cike suke da 'ya'yan itatuwan kwakwar manja bukuru-bukuru. Amma kuma mucizan da suke jikinsu sun linka yawan bishiyoyin sau dari, 'ya'yansu da jikokinsu.Tun ina tsoron miciji har na daina, kana tsaye a bandaki za ka ganshi ta windo, watarana ka ga wani a kicin, in baa rufe qofa ba har cikin falo. In yi ta ihu ada har na saba da su, su kalle ni in kalle su, su wuce.
     Ba a raba gidanmu da yara 'yan makaranta masu tsintar kwakwar da suke faduwa musamman a ranar da aka yi ruwa da iska, sannan akwai himilin tsuntsayen da su ka qauro kan bishiyoyin su na ci su na zubarwa qasa. Reshen kwakwar kuwa shima su na dauka,  su na ferewa su yi tsintsiyar kwakwa.
    A haka na saba da yara da yawa, su na daga waje ina cikin gida ta jikin windo nake kwalla musu kira. Watarana ma in debo musu kwakwa ina basu don masu gadinmu su na tara min kwakwar su bani da yawa har in rasa yadda zan yi da su.
    Na shaqu da wata irinta Janet duk da ta fi ni girma sosai shekarunta zai kai goma sha uku a lokacin amma tana da kirki. Janet mai aiki ce ko kuma in ce 'yar uwar maqawabtanmu ce da aka dauko daga qauye, tana yi musu bauta amma sun saka ta a makarantar boko.
     Kullum ta so daga makaranta sai ta siyo min kayan dadi irin su alawar madara, kafi tsire, alewa da biskit sai ta miqo min ta windo sannan ta wuce gida.  Mahaifina ya na yawan zama tare da ni a gida idan ta kama zai fita sai ya tafi da ni in da ba zai iya tafiya da ni ba kuma sai ya rufe ni ta baya ya ce yanzu zai dawo.
       Daga baya kuma ya fara bari na a farfajiyar gidan tunda akwai mai gadi ya ce in yi wasa amma kada in tafi yawo. Daman kuma gidan baa katange shi ba a bude yake wanwar, sai dai akwai tazara tsakaninmu da maqwabta. A farfajiyar gidan nake wasa na musamman idan yana jin bacci na hana shi ko karatun jarida, sai ya ce in fita in yi wasa.
      Idan Janet ta hango ni sai ta zo mu yi ta wasa, tana jin Hausa kadan-kadan bata jin turanci sai dai yarenta. Ni kuma turanci da Hausa kadai na iya a haka dai muke gane yaren junanmu, har na fara bin ta gidansu, tun tana boye ni har matar gidan ta ganni rannan.
       Ta daka mana tsawa daga ni har Janet din, ta ce daga ina nake? Kuka na barke, yayin da Janet ta hau karkarwa tana bayani. Sai na ga ta yi dariya ta shafa min kai ta kira ni da yarinya mai kyau.
    Mata mai kirki itama tana da kyauta, kullum tana bani manyan kyauta kamar su kek da alewa, da yake bata da qananan yara yaranta duk sun girma su na jami'a.
    Sunanta madam Beatrice, babbar ma'aikaciya ce a kurkuku, ita ce babba a gaba daya kurkukun garin.
     Watarana ta kamo hannu ta shigo gidanmu don ta gaisa da mahaifiyata, sai ta iske babu mata a gidan sai mahaifina ashe kuma ma sun san juna a sanadiyyar kamancecceniya ta aikinsu, ita a prison shi kuma lauya a kotu.
    Ya fada mata gaskiyar lamari cewa daga shi sai ni dan haka ta qara tausaya min. Ta yarda in Janet ta dawo daga makaranta ta dinga zuwa tana daukana muna yini a gidanta. Ya ji dadi da hakan.
      Sai in ji zaman kadaici ya ishe ni kafin Janet ta dawo sai in ji ina son kallon mucizai, dan haka gaba gadi nake tafiya matattararsu in saka su a gaba ina kallo. Wasu farare, wasu baqaqe wasu jajaye, wasu koraye. Na san inda suke taruwa da yawa a wasu lunguna ne a cikin dawa a nesa da gidan, dan haka da sassafe nake sulalewa in kai musu ziyara wasu a cikin ruwa wasu sun kanannade bishiya. Tun ina kallonsu daga nesa-nesa har na fara daukar sanda ina shuna musu, sai su kai cafka koma su kanannade sandar. Ina son 'yan yaransu qanana abin sha'awa.
     Har ta kai ta kawo idan ina bacci ina mafarkinsu muna wasa, haka zan yi ta qyaqyata dariya a cikin bacci, sai dai kawai in ji  mahaifina yana ta girgiza ni yana tambaya ta dariyar me nake yi? Ban fada masa komai ba, ni dai daga gari ya waye sai in tafi da gudu wajensu. Mun yi shaquwar da na fara jin yarensu su ka fara jin nawa.
     Madam Beatrice ta fara saka ni a mota ta na tafiya da ni cikin prison anan ofishinta yake, daga ofishinsa sai in shaga bangaren daurarru maza.  Nan ma na yi abokai da dama, ina zama mu yi hira da su kuma in saurari hirarsu. Babban abokina a cikin daurarrrun sunansa Cindo, ya na da kirki kullum sai ya daga ni sama ya cilla ni. Ni kuma sai in yi masa alqawarin zan kawo masa kwakwar manja da yawa.
      Ba na fitowa daga tsakar gidansu, sai Madam ta tashi daga aiki sannan ta sa a nemo ni mu tafi. Abincinsu ma na koyi ci tare da su har nake taya su kashe kwarkwata. Nake tambayarsu me yasa suke yin kwarkwata? Su ka ce basu da omon wanki da sabulu dan haka idan na tashi zuwa nake kwaso musu na gidanmu in kawo musu.
     Ina jin dadin sauraren hirarsu sannan hirar ta yin tasiri a cikin zuciyata.   Maganar dai ita ce fada, caka wuqa, kai sara da adda, duka ,sata, rashin tausayi da rashin adalci. Ba da ni suke yi ba amma ina nade duk abinda suka ce dan haka na tashi da wata irin zuciya mai tauri bana tsoro bana tausayi.
    Su Cindo su na yawan zuwa gidan Madam akai-akai su na yi mata aiki kamar noma da wanki. Anan ma tare nake yini fa su, sai su qaraso har gidanmu su na tsinci kwakwa tare da ma'aikacin da yake kula da su, ake zuwa da yake ga gida ga gida ne babu ko katangar da ta raba mu.
      Babban tashin hankali da na fara gani shine ranar da Cindo ya hau bishiyar kwakwa zai tsinko sai da ya kai qarshe sannan ya ga qaton miciji ya fasa kai zai sare shi, anan ya fado ya kakkarye.
       Na ga masifa, qato yana kuka yana ihu nima ina kuka ina ihu, sauran firsinoni su na kuka. Aka kira madam ta zo a gigice aka garzaya da shi asibiti daga nan ban sake ganinsa ba sai bayan shekaru masu yawa. Ya zo takanas saboda ya ganni, ya zama gurgu da sanduna biyu, muka sha murna da ganin juna har wa'adinsa ya qare na gidan yari a kwanciyar da yayi a asibiti dan haka garinsu ya zarce. Na yi kawar mutumin da yake wasa da ni yake cilla ni sama.
     Babban rashin da na sake yi shine Janet mai sona wacce a kullum sai ta siyo min kayan dadi itama ashe sata take yiwa madam, dukka kudin nan da take yi min sayayya ba bata ake yi ba dauka take yi. Ranar da asirinta ya tonu aka yi mata dukan kawo wuqa aka sakata a mota zaa mayar da ita garinsu. Ina tsaye ina kallonta, tana kallona tana hawaye ina hawaye na ji gaba daya duniyar ta yi min zafi rashin ta a wajena babbar asara ce.
    "Da wa zan yi hira?  Da wa zan wasa? wacece za ta bani kayan dadi?" Tambayar da na yiwa zuciyata kenan.
     Na dade ina kukan rashinsu sai na ji garin ya fita a raina. Hankalina ya kama gaba daya wajen wasa da mucizai. Sai kuma na ga wani babban wajen bautar ahlul kitabu an bude shi sabo a kusa da gidanmu. Kullum ina  jiyo kida mai dadi kuma ina ganin yara sanye da riguna masu kyau da takalmi, an rufke kansu da ribon su na ta wucewa. Abin yana bani sha'awa sosai dan haka sai in tafi in tsaya ina kallonsu, har na fara zuwa bakin qofa ina leqawa daga nan na fara shiga ciki.
    Da Madam Beatrice ta ganni a ciki sai ta ji dadi dan haka bata hana ni ba, bata fadawa mahaifina ba kuma balle ya hana ni.
    Na kasance ina bautawa abinda suke bautawa, dan haka da wannan addini na budi ido kuma ya shiga cikin zuciyata sosai ina fahimtar abinda suke cewa kuma. Ina cikin yaran da aka zaba wadanda suka iya rawa dan haka ni ce a gaba.
    Mahaifina yana ta waqar zainsakamni a makarantar boko da ta islamiyya amma kuma yana tsoron ya kai ni makaranta in an tashi in bata. Bai tashi ankara ba sai da abu ya yi nisa sosai, gaba daya ya ga na canja halayyata, babu maganar tausayi,  jin qai a cikin lissafina, dan ina dukan yara kamar zan karya su idan suka zo tsintar kwakwa. Sannan ya ji kalamaina sun sauya daga maganar  kisa sai daba wuqa,  sai ya cika da mamaki da fargaba.
      Dan haka ya dauko min malami dan ya koya min karatun qur'ani, sai na qi na dinga tafka musu da su akan ni addinina ba haka ya ce ba. Su ka  ji wasu karatun da bai taba sanin a in da na koyo ba.
      Da ya ga yadda nake wasa da mucizai sai ya yi mamaki ya rasa a ina na saba da su haka, kuma ya tabbatar ina jin yarensu su na jin nawa. Ya tsorata matuqa kuma a lokacin ya zage dantse dan ceto rayuwata amma ina ai ya makara. Ga ni taurin kai, ga gardama ga rashin tsoro, tabbas ya tabbatar akwai matsala.
     Ya fadawa abokinsa halinda ake ciki sai ya bashi shawara akan ya auro matar da zata zauna da ni ta kula da ni, shine kadai mafita dan  in daina fita ko ina.
    Ya yarda da shawararsa ya auro wata bafillatana bazawara, amma fa muguwar gaske ce har ta fi Mummy tsana ta. Ta zo da wasu yaranta agololi guda uku, su suke shaqatawa a gidan ubana kuma abinda Daddy yake gudun dai shine ya faru ban sami wata kulawa ba, sai kyara.
    Aka saka ni a makarantar boko ina zuwa ina dawowa tare da yaranta, da yake babu nisa. Ba na dawowa gida da wuri daga can sai in shiga wajen bautarmu na ji wa'azi. Idan na dawo gida sai ta yi min duka, amma  gobe ma haka sai na tafi.
     Islamiyya kuwa bana zuwa ko an tura mu, sai dai sauran su je. A haka na tsinci rayuwata bana qaunar bil-adama sai wadannan mucizai. Su ne kadai farin cikina ko a cikin bacci tare da mu ke shawagi a duniyarmu.
       Babu wanda ya lura da cewa mucizan illa ne a tare da ni har sun zame min jiki, sun rikide sun zama aljanu sun shiga jikina. Kafin in gama firamare muka dawo Lagos aka saka ni a makarantar kwana ta firamare wacce yayana Imam Malik yake, a lokacin har ya kusa gama sakandire.
     Sai a lokacin Imam Malik ya kula ya gane halinda nake ciki, bayan na hadu da yara inyamurai matsafa, mu ka dinga fafatawa dan nawa sun fi na su qarfi. Na gagari duk wani mugu a mafarki ko a ido biyu, ta kai ta kawo har wata sarauta aka bani, har ma da manyan makarantar su na jin tsorona.  Sannan ya tabbatar ban taba shiga cikin musulmai ba ba na kiran kaina ma da musulma. Hankalinsa ya tashi ya tashin haiqan akaina baya raga min. Saboda tsoronsa ne ma na rage yin wasu abubuwan a makarantar na rashin ji da rashin tausayi da rashin Imani. Kin san waye shi?"  Ta tambaye ni.

    Na zabura na girgiza kai na ce " ban san shi ba." 
       Ta yi murmushi ta ce "shine mutumin nan da kika zo kika samu a kan teburin nan rannan, yana yi min tsawa. Shi kadai gare ni duk duniya, shine ya fi kowa damuwa da ni, ina na tafi ina na ke? Me na ci? Lafiyata da rashin lafiyata. Shine a kowanne hoto za ki ganmu tare, uwarmu daya ubanmu daya kuma kamarmu daya.   
         Ban dawo na gane musulumci ba sai da na gama sakandire lokacin yaya  Imam Malik ya gama jami'a, ya fita da first class Jami'a ta riqe shi ta bashi aiki.
      Da qarfin tsiya ya dauke ni ya kai ni qasar Sudan wata makarantar mata ta kwana, baa fita in ka shiga ka shiga kenan har tsawon shekaru biyu cur. Sai kin sauke, sauka mai tafe da hada, baa yin hutu, baa  zuwa ziyara. Ban fito ba sai da na haddace qur'ani kuma addinin ya shiga jikina sosai.
     Na so in dawo Nigeria in yi karatu amma ya qi amincewa ya zo ya nemo min jami'a ya ce in karanci shari'a law kasancewar karatun qur'anin da na yi zai taimaka min sosai wajen zama lauya a fanni musulumci."
    Na tambaye ta yaya maganar aure?"
    Ta harare ni, sai na ji gaba na ya fadi ta yi shiru zuwa wani lokaci mai tsawo sannan ta ci gaba da magana.
    Ta ce " maganar aure bata gabana tabbas ban taba ji zan iya yin aure ba. Da farko babu wanda ya damu amma da na gama jami'a aka ga bana kula kowa sai aka fara damuwa. Ga ni da farin jini sosai a wajen maza a wajen mata ne ma dai gaskiya bana shiri da su. 
     An yi ta surutu an ce aljani ne ya aure ni, in har da gaske aljanin ya aure ni toh gara ma haka. Rayuwata a haka na fi jin farin ciki."
      Na tambaya "Me ya kawo ki garin Bauchi kuma?"
       Ta yi murmushi ta ce "na zo Bauchi ne don yin bautar qasa amma kuma ina so in zauna kusa da dangin mahaifina, saboda zumuncin ya yanke shi yayi nesa sannan ya hadu da mata mararsa kirki basa son danginsa su je. Mu jinin sarauta ne garin namu ne.
     Wannan shine dalilin da ya sa kika ganni anan mahaifina da iyalansa dukka su na zaune a Abuja yanzu.
      Matansa biyu dukka basa sona daga su har yaransu, dan haka ban damu da sai na je wajensu ba, sai dai in ta kama dole idan na shiga Abuja in shiga a tsatstsaye, mu gaisa. Idan kuma bana so ma in je sai in sami mahaifina a ofis dinsa mu yi maganar in yi tafiyata in sauka a hotel ko a gidan Imam Malik ko su na nan ko basa nan ina da mukullina.
      Wannan shine labarin rayuwata."
    Sai na ji ta bani tausayi matuqa na yi tagumi ina saurarenta. Na sake tambayarta "yaya labarin mahaifiyarki da dan uwanki Umar?"
   Ta tabe baki ta ce "Dan uwana Umar ban taba haduwa da shi sai da na gama jami'a, haka ban ga mahaifiyata ba sai a lokacin su ka zo suka ganni daman shi Imam malik ya na zuwa . Umar yayi aure ya tara iyalai yayi karatu a turai kuma Daddy ne ya biya masa kudin  karatunsa tun yaba yaro har ya gama.
     Mamana ta sake yin aure acan har ta haifi wasu yaran da yawa. Ban damu da su ba, mahaifina kadai na sani shi kadai nake so.
      Ki fada min ta yaya zan yafewa mutumin da ya munana min? Ta yaya zan bar Mummy da Aunty amarya da suka azbtar da ni?  Kin san dole sai na rama, na yi musu irin abinda na yi miki naki ma nafila ne akan na su."
    Na zazzare ido ina kallonta a tsorace.
   Ta ci gaba da cewa " tun ina sakandire da aka yi hutu da qafafuwansu suka shigo har bangare na da zummar zasu yi min wulaqanci Hmmm sai da aka fitar da su.
     Fatiti ki na nufin yin kanki kika ne kika zo dazu? A' a ni na kira ki dan in koya miki darasi. Yanzu next target dina shine Usman dinki."
      Na zazzare ido na dafe qirji ina makerketa.
   Ta ci gaba da cewa " na dade ina bibiyarsa akan abinda yayi min rannan da safe da yasa har mota ta kusa kade ni. Ya zo rannan a ko? Har kin gan shi anan gidan ai amma ba ni ba ni na kira shi ba da kansa ya zo.
    Ya ce min ya zo ne akan ya bani haquri wai yana ta shiga bala'ai kala-kala shine yake ta tunanin shin wa ya taba zalumta, wa ya yiwa laifi ya batawa rai? Shine ya tuna da ni ya ce ya san ina gaba da shi kuma ya bata min rai, dan haka in yafe masa.Na yafe amma ba zan manta ba kuma sai na rama."
    Hankalina ya tashi na shiga yi mata magiya na ce ni dai ta yi min duk abinda zata yi min amma ta yafewa Usman kada ta yi masa komai.
     Ta yi dariya ta ce "yanzu fa na baki labarina, ban san soyayyar kowa ba tun ina yarinya sai mutane biyu yayana da babana. Mutane biyun da nake so ina yarinya ma tsautsayi ya hau kansu  sun tafi sun bar ni. Kin san tsakanin miciji da mutum babu wani alkhairi sai kisa ko? Toh haka nake tsakanina da duk wanda ya taba ni bana yafiya."
     Wasa-wasa matar nan ta riqe ni a gidanta anan na yi magruba da isha'i, bata bar ni na fito ba sai qarfe tara na dare bayan na barke mata da wani sabon babin kuka.
    Ta ce zata bar ni in tafi saboda Haidar mai shan nono amma akan sharadi daya, kada in sake in fadawa kowa wannan abinda ya faru .
     Na amince nan da nan babu musu, ta dauko mukulli ta bude, tana budewa na fito da gudu mayafina da takalma sai watso min ta yi ta mayar da qofarta ta rufe. Jikina yana rawa na sauko qasa gidan Safiya. Na samu qofar a bude kawai na fada cikin falon, a qasa akan kafet na fadi ina makerketa.
     Hankalin Safiya ya tashi ta rirriqe ni ta gan ni babu dankwali, babu takalma, na kasa daukowa acan na barsu. Na kasa fada mata komai sai kuka da ihu nake.
    Na ce mata wallahi yau ba zan iya kwana a gidana ba, tsoro nake ji a gidanta zan kwana.Ta dauka da wasa nake amma da ta tabbatar zazzabi ne a jikina ina kuka ina makerketa sai ta amince ta kai ni dakinta ni da yarana gaba daya hankalinsa ya tashi.
    Ta nemo lambar Usman wacce na kira shi jiya ta kira ya qi amsawa. Sai qarfe goma sha daya mai gidanta ya dawo, ta shaida masa halinda nake  ciki shine ya kira Usman din,  ya tabbatar masa gani a gidansa bani da lafiya. Ko a kai min wayar mu yi magana? Amma Usman  ya ce A ' a Allah Ya sawake ba sai mun yi magana ba a bar ni in huta in sha magani kawai.
     Na tabbatar Usman yanzu bai damu da ni ba ga shi har ya qi yarda mu yi magana kuma bani da lafiya. Gani yake hadin baki ne dan kawai muka yi dan ya dawo.
     Su na da magunguna kala-kala a gidan dan haka Dr.Isa ya bata magunguna ta kawo min, na karba na sha na kwanta. Na riqe hannun Safiya gam na ce kada ta tafi ta bar ni mutuwa zan yi.
      Safiya ta dinga lallaba ni har qarfe daya na dare tana tare da ni, daga nan ta sulale ta gudu wajen mijinta.

Kishin bal-balWhere stories live. Discover now