page 3&4

4 2 0
                                    

*AL'AMARINMU*

           *Na*
*AMINA ABUBAKAR YANDOMA*
     ( _Meenart A Yandoma_)

Wattpad: Meenat_A_Yandoma
ArewaBooks: Meenatyandoma

*Labari ne wanda ban taba tabo irin wannan jigon ba, labari ne daya banbanta da sauran kada in cika ku da labari domin hausawa sun ce gani ya kori ji muje zuwa.*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*

______________________________
    *TSOKACI!*
*LITTAFINA NA KUƊI NE AKAN FARASHI 300 ZAKI RURO KATIN WAYA MTN KO KUMA KI TURO TA ACCOUNT AISHA ABUBAKAR 2151366600 U.B.A BANK, DAN ALLAH IDAN BAKI SHIRYA BA KADA KI TABONI🙏🏻*

*TALLAH*
Albishirnku mata munzo maku da magani na gargajiya wanda zai saukarmaki da ni,ima yaqara maki lfy yawanke miki dattin mara daduk wani sanyi dake damunki,
Ina amare dake shirin yin aure kafin kifara shan komai yakamata kifara da mgnn sanyi domin matuqar bakishaba kayan ni,ima bazasuyi tasiri ajikinkiba,
Ina masu jego gadama tazo,Atafasa asa lipton da sugar da mada asha 2 times Muna katsina muna tura kaya ko ina yankatsina free deliver ne 1500 zaimiki 1month Ku tuntube mu akan wannan number  0903 641 3535 🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️
Typing...✍🏽
10/1/2023
@2023 January

*PAGE 3️⃣&4️⃣*
...A hankali ta fara ƙoƙarin buɗe idanunta lokaci ɗaya wani irin raɗaɗi ya ziyarci fatar jikinta.
"Manahil! Yaya Manahil kina ina"?.
Rizwana ta hau kwala mata kira.
Abinda Rizwana bata sani ba shine Manahil duk suna nan kusa da ita ganin tane dai bata samu damar yi ba sakamakon matsanancin duhu daya mamaye wurin.

Ƙarar ƙarfe suka ji alamun ana ƙoƙarin buɗe wurin, wani abu me kamar ƙofa amma girman shi bazai wuce ƴar ƙaramar Window ba aka buɗe haske ne ya mamaye wurin tamkar duhu bai taba wanzuwa ba, gaban Rizwana ne yayi mummunar faɗuwa sakamakon mutane da ta gani kusan mutum biyar in hada yayyanta zasu kai su Sha biyar a cikin ɗakin.
Kowanen su ɗaure yake da wata gwaggwabar sarka wadda aka yi masu ɗaurin huhun goro da ita.

Kallo ɗaya tayi ma mutunen mace ukun sai maza biyu,  a rame suke duk sun jigata fatar jikinsu tayi matsananciyar dauɗa tamkar basu taba ganin ruwa ba.

Tamkar waɗan da aka tayar miƙewa suka yi lokaci ɗaya tare da fara kallon juna domin sunsan a cikin mota suke to me ya kawo su cikin waɗan nan mutanen? Babban abinda ya fi tayar masu da hankali shine yadda jikinsu ke ɗaure da sarƙa tamkar wasu dabbobi.
"Yaya Manahil ki taimaka ki kwance ni."
Rizwana ta faɗa hawaye nabin fuskarta.
"Manahil tsoro nike ji meya kawo mu nan"?.
Ridwana ta faɗa tare da bin mutanen da kallo.

"Kun faɗo hannun mugaye wanda fitarku a wufin nan sai Allah, muma nan da kuke ganin mu sato mu suka yi suna halakar damu ɗaya bayan ɗaya."
Wata mace daga cikin su ta faɗa.
"Ban fahimceki ba me kike son faɗa."
Maysara ya jefa mata tambayar.
"Ina nufin kun faɗo gidan da ba zaku taba fita ba a ciki ajalinku yake wannan ita ce ƙaddararku."
"Me kike nufi da ba zamu fita ba, kina nufin anan zamu mutu"?.
Cewar Ra'id.
"Ƙarya ne! Dole mu fita mubar gidan nan kota halin ƙaƙa."
Rashdan ya faɗa a fusace domin shi irin mazan nan ne da basu ɗaukar raini.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un! Yaya kashe mu zasu yi mun kawo kan mu ga halaka shikenan munyi gudun gara mun afka gidan zago wayyo Allah na."
Rizwana ta ƙarasa maganar hawaye nabin fuskarta.
Ran Rashdan sake baci ya domin ya tsani yaga hawaye a fuskar Rizwana.
"Dan Allah ku sanar damu meye nufin waɗan nan mutanen a kanmu."
Manahil ta faɗa muryar ta na kyarma tamkar zata fashe da kuka.

Wadda tayi magana ɗazu ita ce ta sake magana dan da alamu tafi sauran ƙwari.
"Ni dai Suna na Murja Kamar yadda aka kawo ku muma buɗe ido muka yi muka tsinci kanmu a haka, mutanen da suka kawo mu gidan nan sun kasance MAYU ne kuma Matsafa, ko alama babu Allah a cikin zuciyar su a gaban idanmu suke mana tsinci ɗai-ɗai suna yankawa babu yadda muka iya domin muma mun san wa'adin mu ya kusa cika mutuwa na gaf da riskarmu, ban damu da mutuwar da zanyi ba domin dama can rayuwata bata da amfani rayuwata abar kyamace, damuwa ta ɗaya ce ina ma zan sake tozali da mahaifiyata in nemi gafarar ta kafin numfashina na ƙarshe ya fita."
Kukan da yaci karfinta ne ya saka ta kasa ƙarasa maganar.
Ta kusa da ita ce ta amshe maganar hawaye nabin fuskar ta.
"Murya taki me sauƙi ce ni haƙƙin iyaye da mijina ga kuma ƴa'ƴana kaɗai ya isheni, ya Allah ka gafarta mani."
Jikin su Manahil sanyi yayi cike da alhini tare da zallar tashin hankalin abinda suka ji an faɗa masu ya saka su fara hawaye in banda su Maysara da suka kasance maza.
"Kuna nufin, munshigo inda ba zamu taba fita ba"?.
"Ƙwarai kuwadomin a tarihin wannan gidan babu wanda ya shigo ya fita sai mutum ɗaya, shima shuwagabannin gidan najin labarin tserewar shi suka bazama yin sulkulle sai da suka maidoshi a gaban idonmu suka yi ma shi kisan wulaƙanci."
Namijin dake gefen Maysara ya bashi labari.
Ɗaki yayi tsit bakajin motsin komi sai sautin kukan matan.
"Kuka ba zai fishshemu ba ku daina kukan nan mu nemi mafita domin ba zamu zuba ido a kashe mu a banza ba."
Ra'id ya faɗa.
"Maysara anya bamu tafka kurkureba, anya munyima iyayenmu adalci"?.
"Kin ga babu wani rashin adalci cikin wannan maganar domin ƙoƙarin rusa mana rayuwa suke mu kuma muka baro su."
Maysara ya ƙarasa maganar.
Ƙarar buɗe ƙofa da suka ji nan jikin su ya fa ra ciri.

Wani zabgegen mutumi ne tsaye a gabansu, kallo ɗaya zaka yi ma shi ka gane babu ɗigon imani a zuciyarshi wani rubabben abinci ne a hannunshi, watsa masu shi yayi.
"Ku gaggauta cinye shi domin nan da ƴan daƙiƙu kaɗan zamu ɗauki mutum biyu."
Yana ƙarasa maganar ya fice daga ɗakin tare da mayar da ƙofa ya rufe.
"Wannan Rubabben abincin shi zamu ci"?.
Manahil ta faɗa cike da mamaki.
"Shi zaku ci domin in ma baku ci ba zaku mutu da yunwa."
"Da inci wannan abinci ƙara na mutu da yunwa."
Ridwana ta faɗa tana kuka.
"Hmm! Muma da haka muka fa ra sai da muka ji yunwa na ƙoƙarin illata mu sannan muka rufe ido muke ci a duk sadda aka bamu."
"Ni da ɗan uwana nasan mune akan layin mutuwa domin duk wanda kuka zo tare a tare suke haɗaku su kashe, ɗan uwana ga wani gyara da zanyi maka kafin in bar duniya naji ka yi wani kuskure kwatankwacin wanda nayi kace iyayenku na ƙoƙarin ruguza maku rayuwa abinda baku sani ba shine duk abinda mahaifanka zasu yi maka rayuwarka suke gyarawa bawai ruguza maka rayuwa ba in kayi biyayya a gaba zaka ga alfanun abun, domin ni bijire masu da nayi nida ɗan uwana shine abinda yaa jefa mu cikin wannan halin da kuka gammu a ciki."
Kallon shi kawai Maysara yayi domin gani yake har yanzu shine bisa gaskiya iyayenshi sune masu laifi.
A gaban idanunsu maza da matan da suka iske a wurin suka cinye abincin nan tass! Ba tare da sun bar ko kaɗan ba.
Rizwana da Ridwana riƙe suke da yayarsu Manahil domin gani suke kamar sune na kan layin mutuwa.
Babu jimawa wasu daka-dakan ƙarti suka shigo tare da jan ƙafar mazan nan guda biyu, suna ihu suna neman taimako haka aka janye su aka fice da su.

Manahil da ƙanen ta har ma dasu murja kuka suke domin suna jiyo ihun samarin nan kafin rai yayi halinshi.
"Manahil me ya ruɗemu muka baro gaban iyayenmu; ashe bala'in da zamu taras kenan wayyo Allah mun tuba ya Rabbi."
Ridwana ta ƙarasa maganar hawaye nabin fuskarta.
"Maysara tun kafin muje ko ina nadama ta lullube ilahirin jikina, ji nike ina ma ban baro gaban mahaifan mu ba."
"Wannan wace irin magana ce kike, bayan iyayenmu sune suka yi mana laifi."
Ganin har yanzu nadama bata fara shigar Maysara ba shiru Manahil tayi domin bakin alƙalami ya bushe.

"Kafin in bar duniya ina so in sanar daku labarina nida ƴar uwata bai fidda tsammani ba domin Allah me rahama ne me yiyuwa ya tsaretar da wasu daga cikin mu amma fitarmu mu duka daga gidan nan nasan ba abu bane me yiyuwa, Ni dai suna na Murjanatu Labarina bai da daɗin sauraro ko alama labari me cike da zallar bacin rai tattare da nadama.

Kallon ta suke cike da tausayin ta domin sun san duk munin labarinta bai kai nasu muni ba...
   
                     ***
...Ƙasurgumin jeji ne babu gida gaba irin jejin da ake kira ihunka banza kururuwarka a wohi, mutum ne tsaye hannunshi ɗauke da wata halitta  me kama da tantabara, yanayin shigar da yayi baka iya banbace shin mace ce ko kuma namiji hatta fuskar arufe take da wani baƙin yadi daya rufe ilahirin jikinshi dashi.

Tsuntsuwar dake hannunshi ya ɗaga sama tare da sakinta ta tashi firr! Wasu layu ya fiddo tare dayin rami ya binne su, wani baƙin abu me matuƙar yauƙi ya fiddo ya zuba shi saman ramin tare da mayar da ƙasa ya rufe, mota ya shige ya bar wurin.

"Za'eem."
Yaji an kira sunan shi, tamkar zautacce haka ya miƙe bai ɗauki komi ba sai kayan dake jikin shi ya fice daga gidan ba tare da kowa ya sani ba, duhun magriba daya fara mutane duk sun tafi masallaci shiya haddasa babu wanda ya lura da yanayin da Za'eem yake ciki domin ko takalmi babu a ƙafarshi.

Tafiya yake ba tare da sanin inda ya dosa ba abu ɗaya ne cikin zuciyarshi muddun baiyi nesa da garin ba bazai kwana a raye ba, tun yana wuce gidaje har ta kai ya iso inda babu mutane sai bishiyoyi, kwatsam yaga ansha gabanshi, da sauri ya ɗago jajayen idanunshi tare da kallonta.

Mace budurwa wadda ba zata wuce ƙanwarshi ba ya gani tsaye a gabanshi, babu wanda ya tanka ma wani a tsakanin su domin ita ma kallo ɗaya zaka yi mata ka fahimci bata cikin natsuwarta.

Rabawa yayi gefenta yayi ba tare daya ce mata uffan baa ya wuce, ganin ya barta tsaye ita ma mara ma shi baya tayi suka nausa cikin jejin.


*WASU HAR SUN FARA BIYA💃🏻 HAJIYA TA ME KIKE JIRI HANZARTO AYI WANNAN TAFIYA DAKE KADA A BARKI A BAYA.*

*MEENART..........*
08133562797

AL'AMARINMUWhere stories live. Discover now