Chapter 1

2.3K 151 16
                                    

TAMBARIN SHAHARA..🌹
  
          001
Destiny#
بسم الله الرحمن الرحيم
Mafia City
   
  Gari ne na farko da yake cikin jamhuriyar Afrika, ta arewa gari ne da ya kunshi manyan jigajigan kangararrun mutane marasa imani da tsoron Allah, wad'ansu irin mutane ne da babu ruwan su da Addinin mutum ibadar mutum, asalima abin da suka sani kudi, kisa, bakar siyasa da bakar kasuwa. Asalin kungiyar ta yan tadda kayar baya ne, kuma suna da karfi a gwamnatin kowacce kasa, domin suna samar da mahaukatar kudi a cikin kungiyar su. A matakin kasa kuwa suna juya shuwagabannin kasashen da na duniya domin suna da karfin iko, sarrafa makamai, sojojin haya, yan ta'adda masu tadda bama-bamai. Ba ruwan su da rayuwar mutum matukar kana cikin su ko kayi aure ko kar kayi aure abu daya ne baka isa barin cikin su ba. The worse part nasu kenan ba zaka tab'a barin su ba domin kayi rantsu da rayuwar ka ita ce abin da zaka basu.

      Mutane dayawa both musulmai da Kirista sun rasa rayuwar su, a wannan ƙungiyar, domin suna ganin matukar ka bar su kamar ka fito da asirin su ne idanun duniya ta san su waye su.

Ranar Alhamis
1989
   Dasuka town
"Tinah ke da Brown ku tafi bakin ruwa, akwai jirgin ruwan da zai..."
"Tussss" kar'ar harbi ya cika gidan, juyawa magidanci yayi yana kallon kofar falon shi. Wasu mutane ne sanye da bakaken kaya suka shigo cikin gidan, sanye da manyan rigunan ruwa.
"Imran cin amana haka? Bayan ka kai matsayin da ake bukata sai ka juya mana baya" mutumin ya fada yana murmushi.
"Paul na zabi nayi rayuwar da addini na ta umarce ni ne, na gaji da wanke hannuna cikin jini male-male, please na hakura da dukiyar da kome ku bar ni na rayu da Yarona." Ya fada yana zuba gwiwar shi a gaban mutanen. Dariya Paul yayi yana sosa kan shi." Ajwaad shi ne matsalar ka? Tow idan muka kashe shi fa?" Duk da kwarjini irin na Imran da sauri ya rarrafa yana me rike kafar Paul. "Na zabi mutuwa da naga gawar shi don Allah kar ku kashe min shi na samu ko bana raye ya min addu'a ku kashe ni kawai." Ya fada yana kuka. Tab'e baki Paul yayi ya ce mishi, "ok ku daure shi a bankawa gidan wuta. Ku kashe sauran employees din shi, ku tafi Crown Academy ku dauko Ajwaad ya binne gawar mahaifin shi amma sai kun kona gidan tukun da shi." "Paul na baka amanar shi for my child sake " duk da ya tsani Imran kamar ya mutu amma wannan damar ya sa ka jin zai rike Ajwaad ya zame mishi tsanin hawa kowacce mataki, ai nasara a jinin ahalin imran take.  Kamar yadda yayi umarnin haka aka kashe kowa na gidan tare da bankawa gidan wuta. Suka fita. Wannan shi ne hukuncin da suke, sai da gidan ya kone murus kasancewar mansion ne babba me kyau kamar castle. Sannan aka kira yan sanda da fire service suka zo aka kashe wutar.

    -----
Crown Academy school, makaranta ce ta yaran da iyayen su, suka kasance yan mafia. Ana bamban su ne da Yaran alumma domin su zama daban a cikin jama'a, ba ason su kasance masu sauki da sassauci su zama marasa imani da tausayin na kasa da su. Ajwaad fari ne siriri dan shekaru goma sha bakwai, dan aji shida, dogo ne mara yalwan jiki amma yana da sura me kyau da kuma yanayi na rashin tsoro. Bai da yawan hayaniya, amma yana da farin jini da mugun isa, shi kan shi Uban daba ne a cikin makarantar, Yara yan mata har fada suke akan shi, shi kuma ko a jikin shi. Bai da iyayi da rawan kai, bai da nuna halin suna da arzikn ko Uban shi wani jigo ne a kungiyar mafia, abin da ya sani adawa yake da Uban shi akan kungiyar mafia asalima ra'ayin shi uban shi ya bi na barin kungiyar dan yayi alƙawarin matukar ya gama karatu wallahi zai bar Mafia City duk abin da zai faru sai dai ya faru.  Kasancewar an haife shi wata bakwai ne kuma uwar shi ta mutu wurin haihuwarsa yasa Uban yake masifar kaunar shi. A hostel din su shi yana VIP hostel ne, domin duk wani jin dadi da more rayuwa akwai shi a ɓangaren, shi da Abraham dan gidan Paul da sai, sai Jabir. Su uku ne abokan junan su,.yana kwance a dakin su kasancewar sauran Abraham da Jabir suna falo inda suke shagali da Yara matasa maza da mata sa'oinsu. Mr Gayu mahaifin Jabir ya shigo tare da drive din su. "Dad me kazo yi a daren nan?" Jabir ya tambaye shi." ina Ajwaad?" Nuna mishi hanyar dakin suka yi, ya wuce a rikice. Yana kwance karatu yake kasancewar sun kusan fara mock. Kunna wutar dakin yayi, Ajwaad ya d'ago blue eyes din shi ya zuba mishi cikin murmushi me sanyi. "Dad!" "Zo muje" ya riko hannun shi, suka fita bai mishi musu ba, haka suka bar hostel din har cikin motar. Tunda ya fito da shi bai ce mishi kome ba, haka shima bai ce mishi kome ba, kasancewar idan mahaifin shi yana kewar shi haka yake sakawa a dauko shi a cikin dare a mai da shi, aiki da tsare-tsaren kungiyar su baya bashi damar zama da Ajwaad, dalilin da yasa Yaron ya taso da haushin uban kenan, tafiyar minti arba'in ya kai su, har dasuka town, lokacin dare ya kuma rabawa sosai, kamar me ciwon kafa haka yake d'aga kafar shi har zuwa kofar gidan su da ya kone murus. Lumshe idanun shi yayi, kafin ya ya juya inda motar ambulance suke tsaye. A hankali yake takawa jikin shi yana wani irin rawan sanyi, kasancewar kasan barci ne a jikin shi. Ya isa jikin motar kafin ya kai ga bude motar an bude mishi, gawar mahaifin shi ya hango hannun shi dauke da zoben shi. "Appa!!!!!!" Ya fada da karfi, da sauri Mr Paul ya rike hannun shi. "Don Allah ku bari na gan shi just once please Father" dake haka suke kiran Mr Paul. Kin barin shi yayi ya ga gawar, wani irin ajiyar zuciya yaja, ya zube a jikin Mr Paul. Shima haka suka saka shi a motar ambulance din aka nufi asibiti da shi.
           "Ba zan tab'a kashe burina ba, domin ina son na isa wannan matsayin dole a rufe kome kar a sake koda Yaran mu ne su san me ya faru a daren nan"
   Da wannan suka rufe babin Imran Nasara, shugaban kungiyar tambarin shahara, dake mafia City. Sai da aka kwashe awa ashirin da hudu kafin Ajwaad ya farka, aka samu yayi wanka ya shirya suka tafi jana'izar mahaifin shi, sai dai baya Humm baya huhhum, idanun shi yayi jajjur, yadda zaka fahimci shi din kukan zuci yake, haka suka samu wasu daga cikin talakawan da mahaifin shi yake taimakawa sun zo aka yi jana'izar mahaifin shi. Zama yayi a gaban kabarin uban yana sauke ajiyar zuciya. Sai da aka yi da gaske suka samu ya tashi aka dawo da shi gidan Mr Paul, ya sake komawa yanayin mara son hayaniya da cunkoson mutane, abincin da aka  shiga shi na safe haka za a fitar,wani irin kunci yake ji a ran shi domin yasan Appa ya mutu ne domin wannan shegiyar ƙungiyar tasu. Ya tsani kungiyar da members din su.

    Kwana goma da mutuwar mahaifin shi, ya fara shirin komawa makaranta, koda ya fito da shiri turus yayi ganin manyan Aminan mahaifin su, sun mike tare da sunkuya mishi suna mika mishi gaisuwar da suke yi wa kungiyar tambarin shahara.
"Long live King! Long life king." Wannan itace sauyin ƙaddara. Haka suka yi ta zuwa suna sumbatar hannun shi na dama. Yana kallon su idanun shi yayi jajjur har yana maikon alamar taruwan kwalla.
"Ajwaad Imran Nasara, muna maka fatan nasara kamar yadda tun daga kakanka har mahaifin ka suka jagoranci kungiyar tambarin shahara Muna fatan kafi karfin gaske da zaka rike mana kungiyar mu"
         Mai da hannun shi yayi ya nad'e a kirji, sannan yayi cikin wani deep voice ya ce. "Bana buƙatar kungiyar ku, ku bar ni nayi karatu don Allah."
"An baka damar kayi yadda kaso, daga nan har inda zaka shiga matukar zaka rike Sarki a kungiyar tambarin shahara mun baka damar kayi ai nasara a jinin ku take"
    A hankali ya wuce gaba, suna take mishi baya har inada aka ajiye wata sabuwar mota kal da ita, kafin ya isa an bude mishi.  Shiga yayi ya zauna yana lumshe idanun shi.  Wannan ita ce kaddaran da mahaifin shi ya zab'e mishi, baya so amma bayi da yadda zai yi, rufe motar aka yi suka nufi makarantar. Tafiyar minti arba'in ya kai su, yana shiga makarantar ya samu daliban makarantar sun fito domin taran shi da kuma mishi gaisuwar mutuwar da aka mishi. Koda suka isa kin motsawa yayi yana jin kamar ya gudu ya bar Mafia City baki daya yadda ba za a kuma jin shi ba. Ya share minti Talatin a motar kafin ya sako kafar shi ya fito.
"King Ajwaad Imran Nasara!!!!" Dalibai suka kira sunan shi da karfi, kafin su iso inda yake kartin maza bodyguard sun musu iyaka da shi, yadda yake tafiya kamar mara gaskiya haka suke kare shi, abin gwanin ban tausayi jikin shi sai rawa yake, domin bai tab'a sanin zai zama haka ba. Wani bangare can na hostel din makarantar aka kai shi, wani karamin plat ne wanda aka kewaye gidan da manyan jami'an tsaro. Kofar gidan an saka katon gate, suna nufa aka bude musu. Su kansu bodyguard din a wurin suka tsaya, masu kula da gidan suka raka shi har cikin gidan, Abraham da Jabir ya samu, suka mike domin tarban shi. Har dakin shi suka raka shi.  "I need privacy" ya fada muryan shi na rawa. "Ok king" suka fada a tare suna fita ya shige ban daki ya fashe da kuka. Wallahi bai san ya zai yi ba, ji yake kamar ya mutu ya wuta. Ya tsani kan shi me yasa sai shi? Babu sauran mutane ne? Me yasa zasu daura mishi masifa, kowa yana rayuwa cikin farin ciki me yasa shi sai shi dole sai shi din ne zai musu yadda suke so? Mahaifin shi ma ya gaza balle shi ne yasa sai shi? Me yasa kome yake zuwa mishi yadda bai zata ba. Da farko haihuwar shi cikin wata duniya na daban, na biyu rayuwar shi da mahaifin shi bai mori kome ba, sai haushi da rashin kauna. Yau kuma an wayi gari an dauko wani masifa an azza mishi a kan shi. Me yasa sai shi? Kuka yayi ta yi kamar yau mahaifin shi ya rasu domin wani irin kewar shi yake ji kamar kamar me.
     Haka ya cigaba da rayuwa cikin sanyi da sauyin ƙaddara, duk wani jin dadi na rayuwa yana samu, akwai abin da ya tsaya haka kawai za a turo Mr Gayu yazo ya dauke shi su tafi meeting a karancin shekaru irin nashi akwai abin da baya buƙatar ya sani domin tunanin shi bai girma haka ba, amma haka za a tula mishi wasu files ya cike su, domin bai san akan me ye ba, shi dai kawai abin da ake bukata saka hannun shi....✍🏽
    *😂🙆🏾‍♀️Allah nemar maganar yau kenan, so Update ba kullum ba wallahi 🙄🤣😹 Alqur'an ku tara kar wani ya tambaye ni daga farko domin FREE BOOK NE DON HAKA A SARARRA MIN*
#Mafialovestory
#Tambarinshahara
#Destiny
    Mai_Dambu

TAMBARIN SHAHARA....🌹Where stories live. Discover now