Chapter 1

17 5 1
                                    

Friday 03/02/2023
9:14 PM

Kwance nake akan doguwar kujera Wani littafi nake karantawa Mai taken suna Forcefully Yours(Mafia Love Story). Takardar tayo mugun tafiya da ni ban Ankara ba kwatsam na ji abu na tafiya a jiki na,ɗagowar da zanyi, me zan gani? SPIDER! A take na wurgar da wayar da ke hannu na kwala ihu ina tsalle dan duk duniya ba abinda na tsana da tsoro sama da spider murya Anne ce da dariya Khalid su ka dawo da ni cikin hankali na Anne ta ce "ke yanzu da girman ki ki ke wa mutane ihu haka a gida? Ba ki da hankali ne?" Ni hankali na yana ga Khalid da har yanzu yake dariya ka sa ce ma ta komai nayi sai S ..s..spider? da na ambata ina nuna Khalid. Anne na ido hudu dashi yace shi yanzu zuwan shi bai san maye yake faruwa ba ta girgiza kanta ta ce "ku kuka sani,sam ba kwajin magana da girman ku kuke abu kamar yara " tsaki tayi tayi gaba abin ta.

Ni ko har yanzu idona na kansa sai wani murmushi irin na na ci nasara ɗin nan ya ke, muna hada ido dashi yayi sauri gyara murya kamar ba shiba ban masa magana ba na dau waya ta dake yashe a kasa wadda fuskan wayar duk ya fashe dan ba ƙaramin ƙasa ya sha ba, na girkiza kai na irin zan yi maganin kan na n nai hanyar daki. Ina jin shi yana kira na yana kiyi hakuri ko tanka sa ban yi ba na cigaba da takawa ji nayi ya kamo hannu na ya sha gaba na yana bani hakuri, " I'm sorry wallahi banyi zaton zaki ji tsoro ba ne" tsaye nayi ina kallon sa yayi wani kalan tausayi yana "pls I'm sorry..ehn haba my twiny "Is ok" na ce. Kallo na ya ci gaba da yi kamar bai yarda ba yace "kina nufin kin hakura?" cewa nai" ba komai ai,ya wuce " na sakar mishi murmushi a zuciya ta kuma ina mamakin sa ko ya dauka zai ci bullus ne dun ya bani hakuri kawai?ina zaman zamana ya sa min spider a jiki, a whole me! Spider?kuma yayi tunani na hakura Lallai kam!

Ina shiga daki farkon abun da na fara raya wa a rai na shine Revenge na san kuna tunanin me nayi masa da zai samin spider ko to bari kuji.

Each Friday muna zuwa family house na mu dan sada zumunta kowa da kowa na family kan hallara a can ba wanda yake so yayi missing wannan rana. To Ni kuma last Friday Kai na ke ɗan ciwo ba zan iya tafiya ba dan gidan da hayani sosai a irin ranan.Ba zan iya zama ina ganin shi ya tafi ba na roƙe sa da mu zauna saboda ba na son zaman kaɗai ci, ba yadda banyi ba fafur yaki ni ma gaskiya ina ji ina gani ba zan bari ya tafi ba tunda na roƙe sa ta arziki yaki sai kawai na hada sa da Anne na ce ai akwai assignment in da aka ba mu bai yi ba.Yace ai har yanzu akwai time dun weekend ne gobe shine dan na ce baya kokari a makaranta malamai sai ƙaran sa suke kan baya shiga aji bai da aiki sai bin frnds dinsa kuma kullum in na fada masa haka yake cewa"Akwai time ai gobe weekend ne" sai in mun je school kuma zaka ga bai yi ba yazo ya sani a gaba sai nayi masa. Ran Anne ba ƙaramin ɓaci yayi ba da taji cewa har malamai na kuka dashi dan ita sam ba ta san irin wannan abun shine ta hana shi zuwa weekend din to fa shi ne wai yake ta faman jin haushi na harda guts in samin spider 🥺a jiki

Na san ban mar dai dai ba amma he must be crazy to think I'm letting that slide

Du hast das Ende der veröffentlichten Teile erreicht.

⏰ Letzte Aktualisierung: Aug 16, 2023 ⏰

Füge diese Geschichte zu deiner Bibliothek hinzu, um über neue Kapitel informiert zu werden!

TWINYWo Geschichten leben. Entdecke jetzt