Rarrashi

44 7 0
                                    

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Ummulkhairi tana dawowa daga makaranta tayi sallah ta ci abinci sannan tayi sallama da su inna asabe da kawunta kawu ISA.
Inna asabe bata so tafiyar ta ba ko ba komai tana morar ta . Tana cin kudinta sannan kuma tana yin aikin gida daidai gwargodo.

Karfe 7:15 na dare suka iso kano, bata fadawa kowa zata dawo yau ba duk sunyi tunanin se washe gari.
Abba da ummanta na parlor suna cin abincin dare tayi sallama, ganinta sukayi ba zato ba tsammani ta shigo da dariya, ta fado kan umman ta da ke zaune ta kai lomar tuwo mamaki ya hana ta hadiye wa.

"Ji jairar yarinya daman kina hanya ne"
Dariyar ta cigaba da yi

"Daman na so  muku surprise ne umma, nasan zakuyi mamaki"

Abbanta da ke zaune shima yace
"Amma da kin jira se gobe kika taho bana son tafiyar yamman nan"

"Yi hakuri abba, ina ta Allah Allah nazo na ganku ne shiyasa ban jira se goben ba"

Suka kwashe da dariya.
Umma tace "to tashi kiyi sallah se ki ci abinci"

Ta shiga cikin gidan tayi wanka tayi sallah sannan ta zubo abinci ta dawo parlor suka ci gaba da hira ciki. Nishadi, suna cinkin hirar ne yan gidan su suka dawo, nan ma aka daura.
Family ne wanda suke son junan su, suna rayuwa cikin rifun asiri da tausaya juna, abun de gwanin sha'awa.

🍒🍒🍒🍒🍒

Bayan Abdulkareem ya bar gidan su khairi massalacin juma'a ya tafi yayi sallah sannan ya dawo office  kai tsaye. Ransa beyi masa dadi ba amma dole yayi hakuri. Ya shigo cikin building din ya tarar da taron maaikata a wajen reception ana dan hayaniya, ya karasa domin yaga abinda ke faruwa. Ganin jidda yayi a tsakiya tana ta kuka mutane sun rufe ta se bata hakuri sukeyi.

Yayi gyaran murya don ya sanar da su zuwan sa gurin, sannan hankalinsu ya dawo kan shi.
"Lafiya?, me ke faruwa a nan"

Ya tambaya yana kallon jidda da fuskarta ta baci ga hawaye ga makeup.
Jama'an da ke gurin ne suka fara bashi labari, har baya ganewa saboda surutu yayi yawa.  Okay kawai yace sannan ya kalli jidda

"Meet me in my office"
Sannan ya wuce sama zuwa office dinsa a bene na biyu. A hankali jidda ta tashi ta wuce toilet ya wanke fuskarta don tayi kyaun gani sannan ta nufi office din Ak .

Tana shiga ta ganshi a kan kujera yana danne danne a waya. Tayi sallama yace ta shigo, sannan yace ta janyo kujerar da aka tanada saboda baki . Ta janyo kujerar sannan  ta zauna.
Se da ya bari ta zauna ta nutsu sannan yayi magana

"Me ya faru ne jidda"

Jidda ta kwashe duk abunda ya faru da bakon da yazo ta fada mishi sannan ta daura da

"Yanzu bansan matsayin aiki na ba saboda shi kanshi director be ce komai ba. Ban san wanene mutumin ba......

bata kai karshen maganar da takeyi ba ta fashe da kuka. Ak ne ya tashi ya zagawo inda ta ke , ya zauna a dayar kujerar da ke kallonta ya fara aikin rarrashi.

" kiyi hakuri jidda kar ki damu, ai ba haka tsarin aiki yace ba, ba yadda zaayi a kore ki ba tare da wani dalili me karfi ba, balle ma kince wanda yayi koran ma bako ne. Bansan menene alakar sa da company nan ba. Amma koma wanene shi a kan aikin ki kikayi acting. Babu abun da ze faru"

"Amma... amma...  a gaban director ne kuma shima be ce komai ba"    Ta fada tana shashekar kuka

"Kar ki damu nace, zan yi ma director magana"
Ya ci gaba da rarrashin ta ita kuma se kara narkewa takeyi, abun nema ya samu me nakuda ta samu katifa.

Son da take masa ya karu ninkin ba nikin wanda tayi masa a baya. Rarrashin da yake mata ya nuna ya damu da ita kenan, kuma ya damu da zamanta a office din. Duk da bacin rai da wannan mutumin ya sa ta zuwan Ak yasa zuciyar ta tayi fess, farin ciki ya cika ta, kukan ma tana yi ne don ya ci gaba da rarrashin ta ba wai don ranta har yanzu a bace yake ba.

Ak yace mata ta je ta ci gaba da aikin ta zai yi ma director magana ranar monday. Sannan ranar monday tazo aikinta kamar yadda ta saba.

Ta tashi ba dan taso tafiya ba ta bar office din.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Alh ibrahim ne ya shigo cikin gidan a mota da gudu. Da sauri ya haura sama ya shiga dakin sa, gurin tsohon akwatin nan ya nufa ya bude. Abun da yake zargi ya tabbata. Umar ya kwashe wayoyin sa. Matarshi Aisha bata nan balle yace ita ta bashi kuma yasan haj binta ce kawai ke da mukullin dakinsa. Ya bata ne bayan tafiyar haj Aisha saboda yan gyare gyare.
Fitowa yayi da sauri ya nufi dakin haj binta. A zaune ya same ta tana kallo a dakin ta hankalin ta a kwance, tana daga kai ta ganshi fuskarsa a daure, da ihu yayi mata magana

"Wa yasa ki bawa umar wayoyinsa da laptop dinsa. Me yasa kika dauko masa"

Mikewa tayi tsaye sannan tace
"Menene lefi idan na bashi kayansa, ze zauna ne babu waya, duk zaman takurar da yakeyi a gidan nan se an kara kuntata masa. Ba'ayi masa adalci ba gaskiya"

Ta fada itama ta hade rai, dan kuwa se de ayi bala'in da zaayi

"Wacece ke da zaki yanke wannan hukunci, adalci da rashin adalci ba ke ya kamata ki yanke ba. Nine mahaifinsa kuma ni nasan me ya dace."

ya ci gaba da banbamin masifar sa bata tanka masa ba sannan daga karshe tace

"Aikin gama ya riga ya gama yaya, sai dai ayi hakuri"
Sannan ta kara daurawa da cewa
"Daman kana da hotunan zuhra?

Gabansa ne yayi mugun fadi, ya akayi ta ga hoton ta, me yasa binta take son shiga cikin lamuran sa ne.
Ba shiri ya bar dakin da sauri.
Haj binta tayi hakan ne domin ta kawar da magana umar. Ta gaji da masifar da yake mata, tasan wannan maganar ce zata sa yayi shiru. Kwalliya ta biya kudin sabulu domin bar mata dakin ma yayi

Yana fita dakin sa ya nufa ya janyo akwatin ya bude, hoton ta ne a sama  da shi zaka fara tozali, dazu da yake a cikin fishi yake be yi la'akari da hoton ba ma.
Ya sulale a kasa yayi zaman dabaro ya tsurawa hoton ido, hawaye ne suka dinga ziraro masa daya na bin daya kamar karamin yaro

"Zuhra ki yafe min"
"Ki yafe min"

yayi ta maimaitawa ba adadi.

🍒🍒🍒🍒🍒🍒🍒
Bintu. A
09034346763

SarkakiyaWhere stories live. Discover now