page 19

68 6 0
                                    

NIMA MATARSA CE
                    NA
  HÀBIBA ABUBAKAR IMAM
    ( YAR GIDAN IMAM )
  BABI NA GOMA SHA TARA
                 **********
    Daker ya Mike ya bita cikin dakin , ya zauna bakin madubi duk yadda ya so ya shawo kanta, ya Kuma wanke Kansa to fa mujaheeda ta ki sauraron Shi. Ta Kuma ki daina kukan da take yi. Hakan yasa dole ya tattara yabar gidan.
   Ita Kam mujaheeda ta rasa inda zatasa kanta , sosai take Jin azuciyar ta cewa Taufiq ya daina Sonta ko Kuma Dama tun farko baya Sonta.domin tayi Imanin Wanda kake so ba zaka taba zarginsa ba balle har kayi tunanin sa da wannan mugun abun.
   Amma tabbas yau Taufiq yayi matukar bata Mata rai ya jefata cikin túnani da bakinciki.
                ***********
     Hajara dai tana ta jinya, gami da Shan magunguna Amma dai har yanzu hannunta Bai dawo dai dai ba Yana motsi amma bai iya yin komai.
   Hakanne yasa duk wani wahalar aikin gidan ya dawo Kan muhseena, ita take yin komai tun daga Kan girki da gyara gida da Kula da dabbobin Ande Dije.
   Mallam Umar da Kansa ya hanata daukar talla domin Baisan da wanne zata ji ba. Dole tasa awannan Karon Ande Dije ta yarda da hukuncin Mallam Umar,Amma ba don ranta ya so ba.
    Mallam Umar ya maida Hajara asibiti kusan sau uku tana Kara ganin likita.kuma likita kasim ya tabbatar musu da cewa Kada su damu hannunta zai dawo dai dai amma Shi Kansa baisan wane lokaci zai dauka kafin ya dawo dai dai ba, tunda komai na Allah ne.
     Wannan hidima da Mallam Umar yake yi na asibitin Hajara ya Kara dorama Ande Dije haushi da tsanar Hajara, domin Saita uni ta kwana ba tare data leka dakinta ba tayi Mata sannu.
   Muhseena ta rasa dalilin irin wannan tsanar da kakarta tayi musu ita da mahaifiyarta.
  Sau tari Kuma tana son ta gasgata abinda mutane suke fada da Wanda ita kanta Ande Dije take fada na cewa ita ba kakarta bace.saboda dabi'un da take nuna musu kwarai zai iya yuwuwa ba kakarta bace.
   To idan ba kakarta bace wacece ita agareta da mahaifinta.
   Don dai ta riga tasa ma kanta yarda da tabbatar da cewa mallam Umar mahaifinta ne shine ya kawota duniya duk wani Kuma surutan mutane na batanci bazai taba Sawa ta aminta da cewa bashi bane ya haifeta.
     Amma tabbas tana matukar bukatar Jin amsoshin tambayoyinta daga bakin mahaifiyarta Wanda tasan sune tambayoyi marasa dadi agareta Wanda Kuma ko kadan bata son tayi Mata tambayoyin. Ya zatayi dole haka zata cigaba da Zama da kuna da radadi acikin zuciyarta amma tana rokon Allah sassauci.
   Yau jikin Hajara akwai sauki sosai harta fito tsakar gida ta zauna a shimfidar da muhseena tayi mata, muhseena tana cike da farincikin ganin irin saukin da mahaifiyarta ta samu.
   Dai dai lokacin mallam Umar ya shigo , shima yajidadin ganin Hajara a waje cikin sauki.yadda yake nuna murnarsa yasa Ande Dije dake gefen dakinta a zaune ta saki tsaki, ji take kamar ta fisgo Shi ta shake Shi.
   Mallam Umar ya dubi muhseena yace " Alhamdulillah yau dai naje makarantar islamiyar Ku na biya duk bashin da ake Bina, saboda haka dazaran Hajara ta Kara Samun sauki zaki koma islamiyar kinji KO". Wani irin dadi ya kama muhseena ta daga hannu sama tana yima Allah godiya sannan tana yima mahaifinta godiya kullum adduar ta bata wuce Allah yasa ta samu ta koma islamiyya yau dai Allah ya amshi adduarta.
   Ande Dije ta Kara sakin tsaki tace a kausashe " haka zaka kare cikin bauta, ta Koma islamiya to ina makomar tallar da take daukar min na yamma"
Ya dubeta yace " Ande Dama talla ai ba hurumin muhseena bane,na Kuma sha gaya Miki kamar yadda nasha rokonki ki daina dora Mata talla."
     Ta watsa masa harara " to idan ban Dora Mata talla ba me kake son na dora Mata so kake tayi ta zaman banza agida ita ga yar gata, tana zube agida ita ba karatu ba ita ba aure ba , ni Kuma Saina tsaya kawai ina kallon tsawonta acikin gida".
   Ya juyo Yana kallonta yace " Bana son muna jayayya Akan muhseena domin baida wani amfani, muhseena yata ce duk wani nauyinta Yana Kaina, babu Kuma nauyinta daya fi komai nauyi akaina irin tarbiyyarta da karatunta, kin Kuma fi kowa sanin talla ba shine hanyar tarbiyyar ta gari don muhseena tayi girman da ya kamata ace tana killace waje daya idan bata makaranta to tana gida Amna Bai kamata a dinga ganinta a layin Yan talla ba, don haka ina rokonki don girman Allah kiyi hakuri da dorama muhseena talla tunda Allah bai nufi zatayi karatun boko Mai zurfi ba to abari ta je islamiyya ta Sami ilimin addininta Wanda shine Kan gaba arayuwa".
   Ande Dije ta jinjina Kai cike da takaici tace " AI baka ganin kowa sai su, ba damuwa nasa muku Ido tunda baka yarda da na Dora Mata talla ba, taje makaranta amma da sadaka Ka nemi wani Ka bashi kayi Mata aure da hakan yafi maku alheri Duka, don idan ba sadakarta Ka bayar ba babu yadda zaayi ta Sami Mijin aure ta dinga Zama agabanku kenan , kana dai gani duk sa'anninta sunyi sure wasu harda yaya Amna ita tana nan ko da sau daya ban taba Jin anyi sallama da ita da sunan sairayi ba".
   Mallam Umar ya dubi Hajara da muhseena yadda yaga damuwa da bacin ran magangsnun Ande Dije a fuskarsu yasa ya dawo da kallonsa ga mahaifiyarsa yace " don Allah kibar wannan maganar, Shi dai aure lokaci ne don haka idan Allah ya kawo Mata Miji zatayi aurenta, saboda haka kibar wannan maganar don Allah ".
   Ta Mike ta kakkabe zaninta tana kokarin dage labulen dakinta tace " magana ko nabarta, nace na barta ". Ta shige daki tana maganganu.
    Mallam Umar ya dawo da hankalinsa Kan matarsa da yarsa yace " Ku kwantar da hsnkalinku, duk abinda kuka ga ban Muku ba arayuwa to Bani da halin yi ne, na rantse ban hada sonku da komai ba , kullum Bani da wani tunani da ya wuce yadda zanyi na ingsnta rayuwar Ku na Kuma sa Ku farinciki.".
  Ahankali Hajara tace " na Sani mallam, Allah dai yayi maka budi na alher" muhseena tace " nasan ko zamu ji dadi ranar da Baba ya samu kudi hmmm" ta Karasa magana tana dariya sosai yajidadin hakan yace " kwarai kuwa muhseena zaku jidadi fiye da zatonki, don har makarantar boko Zan maida ke tunda nasan burinki Kenan Kuma tun daga aji uku na karamar sakandire na cireki saboda rashi, kinga ko ranar da duk na Sami kudi dole na matar da ke makaranta , saboda ni kadai nasan bakincikin da nake kwana nake tashi dashi akan ràshin cigaba da karatunki".
  Muhseena ta aje numfashi ahankali tace, " don Allah Baba kadaina wannan tunanin babu komai ".

NI MA MATARSA CE Where stories live. Discover now