page 1

48 2 0
                                    

*KWARYA TABI KWARYA*

  🌹YAR ABUJA CE🌹

    ©️FATIMA ISAH
     ( Mrs Umar)

*GARGADI*
Wannan littafin ku sani ba gaskiya bane kirkirarren labari ne banyishi dan wani ko wata ba nayi shine kawai dan nishaɗi tare da amfani da abinda ke ciki. Dan haka idan halinka yazo iri daya da labarin sai mutum ya gyara rayuwarsa...

_Marubuciyar_
SON ZUCIYA
MATAR MUTUM
SAI KAYI NADAMA
MASOYINA HAR ABADA
MAZA DA MULKI
NADAMAR DA NAYI
TAWA KADDARAR KENAN
SABODA RAGON LAYYA
MATSALAR DANGIN MIJI
KE DAYA CE
DA BANSAN ASALINTA BA.
AND NOW
KWARYA TABI KWARYA

  1️⃣

A hankali take tafiya cikin isa da izza tamkar bata son taka kasa.
Yanda take yatsina kai kace ɗiyar wani shege ne wani ƙusan gwamnati mai faɗa aji.Sanye take da dogowar riga ta atamfa anyi mata aiki da wani dan yadi yellow haka shi ya bata dama ta saka takalmi yellow da gyale yellow haka ma jikar hannunta yellow ce sai ga wani glass ta dade fuskarta dashi kai kace duk duniya babu irinta ga yanda take jin kanta.
A haka ta iso cikin *FATJEED* wanda ya amsa sunanshi wajan shaƙatawa zan iya cewa duk cikin garin Abuja babu waji mai kyau da tsari irin wajan duk wadda ta amsa sunanta mace zakaji tana labarin wajan zan iya cewa rabi da kwata duk yan karya ke zuwa wajan dan asan kana dashi.
Sai da ta karewa wajan kallo ga baki ɗaya kafin ta yatsina fuska taja kujera can gefe inda babu kowa a kai ta zauna.
Bata jima da zama ba ta fitar da wayarta daga cikin jikarta ƙirar Company apple watau iphone13 kallo ɗaya zakayi mata kasan Yes ita din ɗiyar gidan masu shine.
Bata jima da zama ba waiter yazo ɗaue da wani dan book a hannun shi ya ce

  "Welcome Ma!"

  Kafin ta bashi amsa ya miqa mata littafin dake hannunshi amsa tayi cikin yatsina, ganin hoton abinci a kan littafin shi ya bata damar budewa ta cigaba da dubawa, har sai da tazo karshen bangon littafin kafin ta sake yatsina fuska ta mika mashi cikin isa ta ce.

  "Ayya kayi hakuri fa gaskiya duk nan babu abincin da yayi min kasan ni ba ko wane kalar abinci nake ci ba saboda ban saba rayuwar nan kasarmu ba, kasan ni ɗin girman kasar waje nayi dan haka gaskiya ku gyara tsarin wajanku"

  Baki ya buɗe cike da mamaki yana kallonta saboda akwai wanda suka fita wayewa duk suna zuwa wajan amma basu taɓa fadin wajansu bayi ba sai ita. Duk da haka murmushi yayi yace

  "Hajiya ki duba da kyau wajan nan babu irin colour food ɗin da bamu girkawa na kasashe da dama kamar irinsu Chinese food Indian pizza American chicken. Da dai sauran ƙasashe"

Ajiyar zuciya ta sauke mai karfi tare da cewa.

  "Duk bana bukatar su ka dai kawo min fanta guda ɗaya saboda ba ko wane irin lemu nake sha ba saboda likita ya hanani shan lemu"

Dariya kawai yayi ya wuce ya ɗauko mata.

Wani haɗadin gaye ne matashi mai jini a jika ya iso wajenta shima yana ji da kanshi hannunshi ɗaya a cikin aljihun wandonshi yayi sallama cikin tinqaho .
Can kasan makoshi ta amsashi ko ta ɗago kai ta kalle shi dariya yayi yace

  "Yan mata idan babu damuwa na zauna"

  "Fuska ta ɗago ta wani ɗan wurga mashi harara a wayance haɗi da faɗin.

"Baka bukatar neman izini a wajena domin kuwa tunda waje ne da kowa nada hurumin zama"

  "Gaskiya ne gimbiya amma yana da kyau naji daga bakinki anyway bari na zauna ko babu komi yau ni mai Sa'a ne"

  Kai dai ta maida wajen wayarta ta cigaba da dannawa tamkar bata san yanayi ba.
Ido ya ɗan lumshe tare da dan shafa sumar kanshi ya ce.

  Yan mata ya kamata ki saki jiki dani sannan ki gane ni ba irin mayaudaran mazan nan bane, idan ma kina tunanin haka to ki cire a ranki, tunda na shigo wajan nan idanuwa na dake sukayi tozali idan babu damuwa zan gabatar maki da kaina

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 06, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KWARYA TABI KWARYAWhere stories live. Discover now