Page Fifty Eight

599 75 33
                                    

👨‍✈️ *CAPTAIN MUZAMMIL* 👨‍✈️

Written by *Zeeneert*💕

Zeeneert@wattpad

*Page Fifty Eight*

Sadiq besamu yayi magana da Ammi aranar ba sanin cewa sundebo gajiyar hanya suna bukatar hutu. Akuma daren sarkin musulmi ya tabbatar da ganin wata inda yakama washegari Sallah. Sallan nan na daban ne agurin su Mami kasancewar zasuyishi cikin Yan uwa dasukayi shekara da shekaru basuyi ba and the Family were so happy to receive them back too. Khalil da Khalipha ma sundawo daga makaranta tun shekaran jiya inda jirginsu yasauka a Yola,the Family is full. Amira ce kawai batanan sabida finals dazasu fara immediately after sallah yasa Daddy yace tayi hakuri tayi zamanta kawai intagama gabadaya seta taho. Se Muzammil dake can Ummara segobe zaidawo

Tun sassafe suka tashi aka gyare gidan tasss akasa Turaren wuta tako ina da daka shigo compound din gidan kamshin dazaifara welcoming dinka kenan. Wanka sukayi suka shirya kowa yayi kyau gwanin ban sha'awaa in his new Eid attire sannan suka tafi Eid ground. Daga abinci har snacks kuwa bayarwa Mummy da Ummi sukayi amusu. Ko kafinsu dawo har anyi delivering abincin acan side din Hajiya Mami dankuwa every Eid sukazo Yola acan ake haduwa aci abincin sallah. Nany Ngozi da Ajidde wata new housemaid din Ummi ne sukaje suka hadu a sashin Hajiya Mamin sukayi setting komai a katon Family dining dinsu. Abincine varieties na yan gayu babu kalan wanda babu haka ma snacks. Ga bottle and can juices kala kala jibge wasu a fridge wasu kuma awaje.

Koda suka taso daga Eid ground din can suka wuce direct inda akaci, akasha,akayi raha akakuma yiyyi hotuna. Harta Amira ba abarta abaya ba dan seda suka kirata video call taga ganimar datayi missing aka kumayi gaisuwar sallah. Muzammil ne kawai basusamu ba,sunkira wayarsa akashe. Aikuwa dukda haka seda Fa'iza tayi blessing inbox dinsa da hotuna da videos din duka abubuwan dasuka wakana. Basu suka watseba se azahar inda kowa yakoma sashinsu dan hutawa.

Ammi is trying in every possible way to be acting normal kamar batada wani damuwa and tahowarsu Yola has helped alot kasancewar koda yaushe tana cikin Jama'a. Ashir kuwa tuni tajefa komai nashi a kwandon shara. She deleted his pictures,their chatss and every single thing regarding him,tayi blocking dinshi ta ko ina kafin daga karshe ta goge digits dinsa even though it's inscribed on her heart kamar yanda haryanzu soyayyarsa ke dawainiya da'ita.

Sadiq kuwa haryau takasa kiranshi suyi reconciling kamar yanda tayima kanta da Mami alkawari,wani irin tsananin kunyar sa da nauyinsa takeji yanzu. Sautari setayi yunkurin kira seta fasa dan batamasan ta ina zata fara conversation dinba. Aikuwa dan halak din sega kiransa yashigo wayarta. Wani irin wara idanu Ammi tayi hankali tashe ayayinda ta kifa wayar kan gado haryagama ringing bata dagaba. Ba ajima ba sega wani call din yasake shigowa. Wannan karan silencing wayar kawai tayi dan dukyanda taso tayi mastering courage tadaga kasawa tayi. Seda yamata missed calls kusan biyar sannan ya hakura.

Da yanma ma yasake kira shiru bata iya dagawa ba.

Sekawai yayi deciding yace Mami tahadasu. Aikuwa dadare bayan sungama shan hirar su irinta masoya yace tahada shi da Ammi. Mami kamar gaske curiosly tace "Waini shiri akafara da Ammin ne banida labari?" Dan ko jiya dadare dasuke waya yatambayeta ko Ammi tafada mata wani abu anma tanuna mai batasan komaiba

Cikin sigar zolaya Sadiq yace "ina ruwanki? Kuma damacan ce miki mukayi bamwa shiri?" Mami tayi dariya tace "Oh hakane abun? Niza ayiwa danwaken zagaye?" Sadiq dake dariyar shima yace "Eh din bakin zabi kigoyi bayan Kaninkiba? Tonima se a barni inshigar ma Kanwata" Mami tace "Toh Allah yasa kar Kanwar taka tabaka kunya kuma intayi tsamidai zamuji" Sadiq na dariya yace "Ba abunda zaiyi tsami insha Allahu. Nidai yanzu hadani da'ita muyi magana" Mami dake kwance kan gadon Mummy tashi tayi tafice a dakin zuwa dakinsu. Ammi dake kwance tareda Naaana suna sana'ar kallon cartoon kawai seji tayi Mami  tasaka mata waya a kunne. Da mamaki Ammi tacire wayar a kunne in a whispher tana tambayarta wayene anma bata samu amsarba sema cewa da Mamin tayi inta gama wayar tabama Naana wayar tamaido mata tana dakin Mummy.

CAPTAIN MUZAMMILWhere stories live. Discover now