Hurriya -05

651 32 1
                                    

“Akwai matukar mamaki ace duk son da Appan Hurriya yake miki ya sake ki, saki fa Iyami?”

Amma ta saka hannu biyu ta share hawayen fuskarta.

“Ni ma dai ganin nake kamar ba sakin ba ne, saboda ban saka ran ba mutuwa ce zata raba ba, har yanzu tunani nake ko dai boye min yayi? Wata kila na masa wani laifi ban sani ba”

“Bayan kin ce ya fada miki baki masa komai ba?”

“Hindu namiji na sakinka haka nan? Ai na ga sai da dalili”

“Dalili daya ne Iyami sa'ar da matansa suke nema sun samu, kin mata a cikin manyan mata kuma tsofin mata kike zaune? Matan da sun kusa sa'ar gwaggo? Wace ce warinki a cikinsu? Iyami babu kalar kazafi da kage da ba su miki ba duk dan saboda ki bar gidan amman burinsu be cika ba sai a yau, maganin ma na san sun gwada Allah dai ne be ba su sa'a ba sai yau”

“Hindu Waallahi ina son mijina, mijina kuma yana so na amman yau komai ya kare”

Amma ta fashe da kuka.

“Har sai kin fada? Ai kowa ya san yadda kuke zaune ya san mijinki yana sonki kuma ke ma kina sonsa, sakin ma da zai miki Iyami na musamman yayi wane namiji ne zai saki mace ya dauki dukiya ya danka mata? Ai sai zababbu cikin mata, kuma ko yanzu karki yanke kauna In Shaa Allah zaki koma dakinki ki cigaba da addu'a nima kuma zan taya ki kuma ki saka ayi miki a islamiyayo nima kuma zan zaka ayi miki”

Kasa cewa komai Amma ta yi sai kuka take kukan da da zaka iya rantsewa mutuwa aka yi mata, idan ta tuna da sakinta Appan Hurriya yayi sai ta ji zuciyarta ta narke ta rasa me ke mata dadi a duniyar nan  da ace mutuwa yayi sai ta dangana amman tunawa cewar yana raye kuma shi da kansa ya zabi rabuwa da ita ya fi komai daga mata hankali.

“Toh wai a can kika bar su Hurriya?”

“Ya ce zai rike su”

Ta amsa mata cikin kuka. Hindu bata wani dade a gidan ba ta mata sallama ta fita domin komawa nata gidam ta dora girki. Haka ta wuni a daki idan Gwaggo da jikokinta suka shigo sai ta boye fuskarta ta danne kukanta har sai idan ta kadaita ita kadai, tunanin yaranta ya tsaya mata a rai, tana ta auna lokacin dawowarsu makaranta da kuma irin abubuwan da suke idan sun dawo, da dare yayi sai ta kasa bacci domin wannan ne daren farko da zata kauna a gidansu tun bayan aurenta shekara goma sha shida. Ko biki ake a gidan ko wata hidima Appa baya barin ta kwana ko da kuwa ba girkinta. Daren sai ya zame mata wani dare na dabam da bacci ya gagara kusantar idonta ma balle har ya sace ta, kukan ma sai ta neme shi ta rasa wata zuciyar nata raya mata hanyoyin da zata bi ta shirya da mijinta sai ta saka zaren idan ta karshe sai ga ba hanya ce mai bullewa ba, dare ne da yayi mata tsawo fiye da sauran dararen da suka gabata, karfe biyu da rabi ta doro alwala ta fara raya daren da sallah nafila a haka aka kira sallah asuba akan idonta.

HURRIYA POV.

Da murna ta shigo dakin Appanta ta zauna kusa da shi a kasa kamar yadda ta saba, sai ya kai hannu ya shafa kanta zuwa bayanta yana murmushi irin murmushin nan dake dauke da so da kauna da kuma farincikin abun da idanuwa suka yi arba da su.

“Hurriya toh yaya?”

“Lafiya kalau Appa, ka dawo lafiya?”

“Lafiya Kalau, ina can gurin aiki zuciya na nan tare da ku sai tunaninku nake Ina Hamad”

“Shi ya ce ba zai zo ba?”

Ta amsa tana kai hannu ta gyara gilashin idonta. Hajiya Kaltume dake zaune kan carpet ta yi murmushi, irin murmushin nan da ya zame mata dole ne, domin ta kasa hadeye maganar da Appa yayi cewa yana gurin aiki zuciyarsa na gurin yayansa ta ce.

“Hamad ai ba zai zo ba, dazun ma dukanta yayi ya fasa mata gilashi sai da Yasir ya shiga tsakaninsu”

Appa ya kalli Hurriya cikin yanayin damuwa.

H U R I Y Y AWhere stories live. Discover now