008

124 18 1
                                    

_BINTUN BATUUL_

Top-notch season 3

Ayshatuuu

008

Rasuwar iyaye Rashi ne da duk abin da zaka samu a duniya ba zai maye maka gurbin su ba, idan ka rasa iyaye hakika ka rasa wani bngare na rayuwar ka, Haka babu Wanda zai fahimci ciwon da yake a rashin iyaye se Wanda ta faru akan shi! Ina adduar Allah ya jikan iyayen mu da Wanda suka rasu da Wanda suke da Rai, yasa aljanna ce makomar su, ya Kuma kyautata namu zuwan! Amin

Rasuwar Mr Fahad, ba karamin girgiza dukka kasar tayi ba Amma Kuma mussamman tilon diyar shi Zainab, wadda da farko kasa amincewa tayi da cewar Wai mahaifin nata ya rasu, ta dinga fadawa kakarta da ta haifi mahaifiyar ta cewar tace a duba shi fa, dogon Suma yayi saboda Bai ci abinci ba, wannan maganar da tayi ta Kara dagula lissafin kakar, tare da saka ta kuka sosae

" Jadda! Bai mutu ba, jadda ki fada musu Bai mutu ba"

Haka tayi ta maimaitawa har safiya lokacin da zaa tafi da shi makwancin shi, tunda aka fito da gawar Zainab ta yanke jikin ta ta Fadi, Wanda baa samu ta dawo hayyacin ta ba se da aka Kai ta asibiti, lokacin da ta farka taga kanwar mahaifiyar ta Raziya se ta sake fashe wa da kuka, ta dinga Yi Babu kakkautawa har se da aka Mata allura da ta saka ta bacci kafin Kuma dakin yayi shiru!

A takaice Zainab ta rayu cikin maraici na rashin uwa da uba, se wannan jadda wato kakar ta, da tun rasuwar mahaifiyar ta, Mr Fahad ya role ta Kan ta dawo gidan ta zauna da Zainab, shi din bashi da kowa,na shi iyayen sun Jima da rasuwa, to yanzun ma jadda kawai ta rage Mata. Kunsan mutum yayi coping da irin wannan rashin Abu ne ba Mai sauki ba.

Kafin rasuwar mahaifin ta, ta samu gurbin karatu a daya daga cikin manyan jami'oi dake kasar America, wannan rasuwar ce ta kawo tsaikon tafiyar tata, bayan wajen wata da rasuwar jadda ta lallaba ta ta wuce America.

Zuwan ta America, se taji sabuwar rayuwa, taji ta daban cikin wata duniya wadda ba irin wadda ta tashi a ciki ba, Amma yau da gobe se ta Fara coping, har ma tayi kawa da wadda suke aji daya da ita wadda baturiya ce daga kasar America, course daya suke shi ne ya kawo shakuwa a tare da su. Zainab ta kasance nutsatsiya wadda ko a tafiyar ta zaka san wannan halitta a nutse take, maganar ta, al'amuran ta da komai nata, she's too gentle and beautiful!

Shekaran farko Babu Wanda ya lura da ita, kamar yadda Bata shiga harkar kowa ban da Lily, ko da akai hutu na session se tace da jadda ba zata koma Qatar ba saboda tana tunanin yadda zata koma ba tare da taga mahaifin ta ba. Wani lokaci ta fito daga class a matukar gajiye, ga yunwa ga Kuma zafi da ake yi dukda baa Jima da dauke ruwan sama ba, Wanda ya samu ya kwanta a wasu wurare cikin makarantar, tafiya take Yi a hankali zuwa gate din makaranta Dan ta tsallaka ta Shiga taci abinci a eatery din da ta saba. Tana tafe sanye cikin bakar Abaya wadda tayi Mata kyau, ta yane Kan ta da mayafin abayar Baki, Wanda ya sake fito da asalin fatar larabawan da take da shi, tafiya take a nutse, Wanda ga masu wucewa gani suke yanga take, Amma a zahiri Haka tafiyar tata take, wani lokacin Alan tsayar da mota tare da yi Mata tayin free ride, Amma se ta girgiza Kan ta tare da godiya, ta kusa zuwa gate wata bakar sport car ta taho da mahaukacin gudu tamkar zai buge ta, har se da ta tsorata, Amma kafin ta matsa daga wajen se ji tayi ruwa tun daga Kan ta har cikin brown leather loafers din kafarta, cak ta tsaya tana kallon motar da ta wuce kamar me tukin Bai San ya watsa Mata ruwa ba, tayi shiru tana kallon jikin ta, kawai se taji hawaye ya Fara sauka saman kuncin ta, ta juyar da kanta tana kuka me ciwo, dama me neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki!

Cikin motar wani bature ne me suna Charles, a gefen shi wani bakin African ne me suna Imam, kana kallon shi kasan Dan Africa ne, idan kayi bincike da yawa zaka iya fahimtar shi din Dan Nigeria ne, idan kana neman yaran da basa Jin magana cikin entire campus dinnan to idan ka samu clique din su Imam ka gama, kowa ya San su saboda yawan su, da Kuma sun hadu ne daga various departments.

Tun da suka taho idanun shi ke Kan Zainab, tafiyar ta kawai ita ce abar da ta Fara daukar hankalin shi, na biyu Kuma shigar ta, cikin Kamala da mutunci Wanda ba kowa ke daurawa daga tarbiyar da iyayen shi Suka bashi ba, Yana wannan tunanin tare da begen ganin fuskar ta kawai se gani yayi Charles yayi Mata feshin ruwan saman da ya kwanta, wani duka ya Kai Masa unconsciously tare da fadin

" Do you want to die? Are you crazy?"

Charles ya kalle shi Baki bude da Kuma mamaki, Dan kuwa ba karon farko da suka Fara yiwa Yan Mata Haka ba. Shima yace w

" What's wrong? Is just for fun"

Ya kara dukan shi a keya Wanda ya kusa saka steerer kwacewa daga hannun shi, yayi saurin dafewa tare da gritting hankoran shi in annoyance, cikin turanci Imam yace Masa se sun koma ya Bata hakuri, wannan shi ne karon farko da suka taba yin hakan tun haduwar su, Babu yadda Charles zaiyi ya koma cikin school inda Zainab ke tsaye tana sharbar kuka, yayin da Imam ya Fara Jin wani nervousness hade da uneasiness Yana addabar shi tun kafin ma yayi idanu biyu da ita.... Tirkashi

***



Na Jima a kitchen din kafin na fito na koma daki, Babu kowa duk sun tafi parlor kallon ka'ida, na kwanta nayi shiru Ina Jin ciki na yadda yake yi min ciwo, amma saboda Hali irin nawa se na hakura har aka Kira maghrib na tashi nayi sallah, sannan Batuul ta shigo da kwanon abinci, ta aje min a gaba na, kamar mayuwaciyar zakanya da ta ga nama Haka na dumfafi abincinnan Babu sadsauci, ban ma damu da zafin dake ciki ba, buri na na jishi a Baki na ya Kuma sauka a ciki na, se da na kona makogaro na kafin na sarara ya Dan Sha iska na cigaba da ci, Ina gamawa nayi gyatsa, Haka kurum naji ya kamata nace alhamdulillah! Na furta tare da Shiga toilet na wanke hannu na, na Tara Baki na a sink na Sha ruwa, Ina fadawa gado ko minti uku banyi ba bacci ya dauke ni, bansan me ya sake faruwa ba a gidan Dan lokacin da na tashi tsakiyar dare ne, kowa yayi bacci, Nima nayi juyi na cigaba da bacci. Da safe Dana tashi nayi wanka na saka uniform, dakin Mamaa naje na gaishe ta, sannan na wuce na Adda, ta Gama shiryawa cikin fararen Kaya na nurses, ni dai babban buri na a rayuwa ta a wannan lokacin idan na girma na Zama nurse, ba karamin burge ni suke ba, ban sani ba ko Dan kasancewar Adda nurse shi yasa nake son su?

"Adda Ina kwana?"

Ta kalle ni da kyau kafin tace

" Ni wallahi mantawa nake Dake a gidannan Bintu, jiya Ina Kika je har dare ban gan ki ba?"

Kun ga fa tun laasar ta dawo Bata ganni ba Amma Bata bada cigiya ta ba, nayi murmushi nace

" Adda idan na girma Zan Zama nurse kamar ki!"

Na fada Ina murmushi, ta tabe Baki tare da fadin

" Da wani brain din? Times table ma ana yaki dake balle Nursing, ke ai sede education!"

Lokacin naji kamar an sare min gwiwa ta, I began to think meye education? Nasan dai karatu ko ilimi I dunno how to put it, Amma su marasa kokari ne kenan? Se naji wani haushi ya Kama ni, ba tare da nace komai ba na juya Dan tafiya school. Ko Dana dawo daga school nan ma dai kamar jiya ne babu abinci, yau ko biscuits din ma ban rago ba se kawai na Sha ruwa na Yi assignment di na, idanu na kadai idan ka kalla kasan yunwa nake ji, Amma babu Wanda ya maida Kan shi Kai na, karshe ma a gaba na Batuul tazo da kwanon abincin ta taci, na dinga hadiyar yawu Amma ko mhmmm bance Mata ba, Dan nasan da gayya tayi hakan, idan nace Zan ci ta Hana ni yadda zanji haushi.

Anyi sati ana haka, na Fara galabaita Dan Haka na samu Adda a daki na fada Mata abin da yake faruwa, dukda nasan ba Wai zata canja bane ba, amma dai gwadawa ce na gani me zata ce. Ile kuwa se tace Wai decision din kawu ne nayi hakuri, Ni bana Jin jiki na yayi nauyi?

The top-notch writers are back again, wannan karon Gen Nasir Zaki ne na Azizat Hamza, NAZNEEN na Me Dambu da Kuma BINTUN BATUUL na Shatuuu, duk Akan farashi me sauki, N1300

Bintun BatuulWhere stories live. Discover now