jidmal

5 1 0
                                    

👩‍🦼👩‍🦽👩‍🦼👩‍🦼👩‍🦼👩‍🦽👩‍🦼👩‍🦼😭😭😭😭😭😭😭😭
        *WATA SAKAYYAR*
          (  SAI ALAHIRA )
👩‍🦼👩‍🦽👩‍🦼👩‍🦽👩‍🦼👩‍🦽👩‍🦼👩‍🦽😭😭😭😭😭😭😭😭

*By NUSAIBA ALKAMAWA*

    *PROFICIENT*   
                        *WRITERS*
                    *ASSOCIATION*

*Page 32*

*****

____________indai nice uwarsa wacce ta shayar DASHI, to wllh sai aminu ya auri Rabi'atul Badawiya" ni kuwa indai nice Hassana to ni da kishiya har abada sai dai naga anayi wa wasu, tsohuwar banxa kawaii ai abinda kuka yiwa Hafsat ne yake biyayyar ku ni dalla fice min a gida.

"cikin nadama hajiya inna tabaro gidan Hassana idanunta cike da hawaye, inama Abdullahi da hafsat suna duniyar da tanemi yafiyarsu tagane kuskuren ta, wacce take so ce gashi kuma yanxu ita take bata wahala, kuyafeni yayan albarka, ni yanxu ma ko hauwa'u nagani na nemi yafiyar ta  amman saidai kash!! Hassana taki barina nashiga nagano ta, wai ita da gidan dan ta aikuwa xata nuna mata ita tahaifi Aminullah takarashe maganar tana me xub da hawaye.

________Washe gari jiddah da wuri tatashi tayi dan aikace-aikacen ta.

Sannan tashiga dakin Dan mama, tarar dashi tayi akeken kaddararshi lumshe idanunta tayi tana matukar tausaya masa akan wheelchair din nan sbd yafaru a kanta tasan gajiyar zama aciki, gaishe shi tayi amman ko kurarta bai kalla ba, cikin rashin jin dadin hakan, ta gyara masa dakinsa tsaf sannan taje ta dauko masa abinci ta kawo masa, nuna mata hannu kawaii yayi alamar tafita, tashi tayi cikin mutuwar jiki tafito, dakin momy tashiga ta tarar da ita tana waya da Alama kuma wayar mai mahimmanci ce ganin momy ta nutsu tana saurara, bayan sun kare wayar ta kalleta tace sannu 'yata yau kinsha aiki ko? to Allah yayi albarka, yaudai yusra xata dawo kinga ta debe miki kewa, murmushi nayi cike da jindadi ko ba komai idan da mutum akusa dani xan rage shiga damuwa.

*Jamal*

"Waya rike ahannunsa ya karata akunne, amma muhsen kana ganin Khalid din xai iya rike asibitin kafin kaje kadawo? kasan fa yana da sakaci.

" adayan bangaren a kace, insha Allahu Dr jamal, khaleed baxai bamu wata matsala ba, ai baxan dade ba dan dema inaso naje ayi agabana ne sbd kar a samu wata matsala kasan mutanen mu ba kowane mai tsoron Allah ba, xasuje su cucekane kuma kaga abun nan amana aka bani ta marayu ce shiyasa nake kara damke amanar a hannun na, baifi nayi kwana biyu bama nadawo.

"To shikkenan muhsen Allah yakaika lpy amen Dr jamal
kaima Allah yabaka lpy Amen muhsen.

" Trolly din ta take Ja harta karaso cikin main parlour dakinta ta wuce ta ajjiye trolley din ta sannan ta shiga dakin momy, yusra kenan kanwar Dr jamal.

"rungume ta momy tayi tace oyoyo my daughter urwelcome, Dan bata fuska tayi tace momy ai babu ruwana dake wai harnaxo Amman akasa xuwa adaukoni a airport sai  uncle shuaib nayi masa waya shine fa yaje ya daukoni.

" Affuwan mah baby abinda yasaka banje ba akwai wani babban dalili Amman baxan fada miki ba, sai kinci abinci kin shirya yanxu dai tashi kiyi wanka, manna mata pick tayi agoshi sannan ta tashi.

_________tana shiga dakinta tacire kayan tashiga wanka tana fitowa ta shirya cikin tsadadden less din ta aikuwa tayi  matukar yin kyau.

"knocking taji anyi yes come in, shigowa  jiddah tayi hannunta na rike da kayan abinci, yusra tana zaune hannun ta rike da waya da alama chart take har jiddah tashigo ta ajjiye bata dago ido ta dubeta ba, ganin haka yasa jiddah ta koma ta rufo mata dakin ta, dakin doctor jamal tashiga taganshi akan wani sabon wheelchair cike da mamaki takarasa shiga, aikuwa bata gama mamakin ba saida taga Dan mama yadan na wani Abu a jikin keken taga yana tafiya, kee jeki dauko min ruwa kuma saura kidade, cikin sauri ta tafi domin tana son taje tadawo domin takarasa ganin wannan sabon Al'amarin daya daure mata kai wato masu kudi dai sun huta ji yacce yake sarrafa keken nan ta yar da yake so, dama gaskiya tana mugun tausayin shi da d'ayan keken sbd itama taxauna shekaru da shekaru aciki taji rashin dadin keken da wahalar da takesha gaskiya tayi masa murna.

_______aikuwa cikin mintina kalilan takawo masa hade da wani glass cup, mika masa tayi yakarba, yafara sha, to saiki tafi ko, ta tsinkayi maganar shi fita tayi tashiga Dakinta tadauko naira dari biyu da inna asabe taba ta shin ta ina xan fara neman Dr jamal ne? Kuma tayaya xan fita daga cikin gidan nan? SANNAN idan Nafita bansan inda xani ba, Dan bansan hanya ba, to wace ma hanya xan sani nida bafita nakeba kullum ina gida ? Amman dai bari na gwada sa'a ta, fitowa tayi cikin sand'a Dan bata so ahanata fita, Dan da ahanata nemo Dr jamal gwara ace tabar aikin gidan ga baki daya gwara ace ta koma wajan umma hassana ta cigaba da karban ixayar da take mata, wanda yanxu yaxame mata jiki.

______ Bude kofa tayi tafita tazo daidai get maigadi yatsare ta, da tambayoyi, ya jiddah xatayi haka tayi masa karya wanda ba halin ta baneba tace hajiya ce ta aike ta, Bude mata gate yayi tafita cikin sauri, ita dai kawaii tafiya take Amman bata son inda xata dosa ba.

"Horn ake mata Amman ina tunanin ya tafi cen,  wani guri, bata ankaraba saiji tayi anyi sama da ita, bata kara sanin inda kanta yake ba.

" Salati khalid yake ta xabgawa,wanda ya dauko yasmen daukar ta yayi yanufi da ita asibiti badon yasmen taso ba da haka tace kawai su gudu yacce aa gwara sukaita asibiti su taimaketa .

______wajan 7 mint yusra na Knocking   Amman taji shuru shi kuwa Dr jamal, yayi tunanin wannan yar aikin ce shiyasa baiyi magana ba domin harga Allah haushinta yake ji, ita kuwa yusra wanda tagaji ta tsayuwa, ta tura kofar komai tafanjama fan jam domin tasan dokokin yayan nata, ba a shigowa dakinshi saka ka, yasha hukuntata akan haka.

Hamma jamal? Dago dara _daran idanunshi yayi ya kalli kanwar tashi abun sonshi, kamar bayason magana yacce, yusra yaushe kika sauka?

"Rungume Dan uwan
nata, tayi tace yaya jee bayan kamanta dani kuma kadaina sona ta fada cike da shagwaba ta turo Dan karamin bakinta, ina sonki mana yusra baki ga bani da lpy bane ai da kinsan ni xanje nadauko ki.

" lpy yaya me yafaru ta fada cike da tashin hankali, Dan sai a yanxu ne takula da yarame yayi baki, nan ya labar ta mata komai Dan baya taba boye mata wani Abu daya shafesa, kafin yagama bata labarin hawaye ya cika idanunta, yaya meyasa? Meyasa kabada lafiyar ka sbd wata banxa, kai yanxu gashi kana cikin wani hali wanda baxan iya jurar ganun ka aciki ba, wllh yaya har naji na tsani yarinyar nan, na tsane sosai idona Idonta wllh.


*Hajiya inna*

______Baba Malam inaso xuwa gobe adaura auren nan, cikin kakkausar muryarsa ta malunta yace hajiya dadai mun nemi ixinin aminu tukunna sai adaura auren, karmiyi Abu daka batare da yardar saba.

"yardar sa ta banxa ai saina nunawa hassana ni nahaifi aminu bawani cen ba, ni xan bada sadakin kuma tunda yarinyar ta a mince ba shikkenan ba, haka badon ran baba Malam ya so ba ya a mince da xa adaura auren gobe sbd yasan darun hajiya inna da kafiya akan Abu, to shikkenan Allah yakaimu goben amin, ta fada da Dan murna sbd kawaii hango halin da  hassana  xatashiga .

*JIDDAH*
Bude idanunta tayi wanda take ganin dishi _dishi maganar wani mutum ta tsinkayo, Sannu kintashi? Ware fararen idanunta tayi akan shi, wayyo khalid daskare wa yayi a wajan ganin tsantsar kyau a wajan baiwar Allah nan.

tunani tashiga shin a ina take kuma waye yakawo ta nan metake yi Anan?
Meyafaru da ita kamar fa tana gadon asibiti.

No editing

More comment more typing

*(¯'*•.¸,¤°'✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿'°¤,¸.•*'¯)*

Kokarin azawa akan tafarki,shi ne abu mafi muhimmanci da yakamata marubuta su kware akai,mu proficient writers association za mu yada wannan manufa.

https://www.facebook.com/profile.php?id=100086156706062

https://t.me/+R7IGS941_bg3NDI0

  https://chat.whatsapp.com/GK9uG1er0mUFsuS1s5JE9K

WATA SAKAYYAR( SAI ALAHIRA) Where stories live. Discover now