1, Ɗanɗano

386 13 3
                                    

♡WA ZAN KARE..??

NA; AYSHA JB

®
FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION📚
[Ƙungiya Domin wayar da kan Al'umma. Farin Jini Writer's domin ci gaban Al'umma]

        ★F. W. A★📚
https://www.facebook.com/profile.php?id=61554021072796

_Alhamdulilah! Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Tsira da aminci su ƙara tabbata ga fiyayyen halitta Manzon tsira Annabi Rahama Muhammadu (S.A.W) Ɗan Abdullahi. Ina Ƙara godiya Ga Allah daya sake ara min rai da lafiya ya kuma bani iko da damar fara wannan rubutun, Allah na roƙe ka da kayi riƙo da hannayena gurin rubuta daidai. Allah ka bani ikon rubuta Abin da Al'umma zasuyi Amfana dashi. Godiya ga dukkan masoyan JB, Allah ya ƙaunace ku kamar yadda kuke Ƙaunata, Na gode matuƙa da nuna kulawa._
    *Wannan shafin sadaukarwa ne ga Ƙungiyata, Farin Jini Writer's Allahu ya bar Ƙauna tsakaninmu*
  
*Ɗanɗano* 01

Cike da ɗunbin farinciki take saukowa daga matakalan benen jirgin fuska ɗauke da fara'a ta ke  gyaɗa kanta tana jin wani irin nutsuwa na sa ke samun matsunguni a cikin ƙarƙashin zuciyarta. Fara ce sol irin farin nan mai sheƙi da ɗaukan ido, Tana sanye  da baƙin doguwar riga yayinda ta yane kanta da ɗan mayafin rigar kyakkyawan doguwan fuskanta na maƙale da farin madubi buɗe hannayenta duka biyu tayi tana jin yadda Ni'imar Allah ke kaɗawa haɗe da ta shin ƙamshin ƙasa alamar yanzun haka ana ruwa  a wani wurin ido kawai abokan tafiyar na ta suka zuba mata ganin yadda ta wurgo musu jakanta tare da sauka da gudu tana zagaye Airport ɗin cike da jin daɗi “Ah! Lallai dole ki nuna farinciki fiye ma da haka kasancewar burin ki na son zama barrister ya cika bayan ɗaukan shekaru da dama yau gashi kin dawo ƙasar ki zakiyi mata aiki ina fatan kin dawo lafiya Habibty?” Waigowa tayi tare da sakin murmushi tana gyaɗa ma sa kai ba tare da tace komai ba. Da ɗan gudu ta ƙarasa ga mahaifinta tare da rumgume shi tana ihun murna “Wayyo Allah  nayi kewar ku sosai Abba Ina Mimi da Hajiya Mama?” Ta ƙarasa maganar tana waigawa ko zatayi arangama dasu sai dai haƙanta bai cimma ruwa ba, Domin haka ta gama baza idanuwa ba tare da taga ɗaya daga cikin waɗanda ta ambata ba, Kwaɓa fuska tayi idanunta na ƙoƙarin kawo ruwan hawaye  cikin lallashi mahaifinta ya fara magana “Yi haƙuri Shalele kowa na cikin ƙoshin lafiya naji matuƙar daɗi ganin yadda Allah ya cika miki burin ki, Ubangiji yasa rai a kayiwa” kafun ta amsa addu'ar ta sa taji an rumgumeta ta baya sassanyar ƙamshin turaren ta ne yasa ta fahimtar Mimi ce “You're highly welcom back daughter, Cike da farin ciki nake taya ɗiyata murnan kammala karatun ta na zama cikakkiyar lauya fatana kuma roƙon da nake yiwa Allah bai wuce a ce kin zama jajirtacciya mai faɗar gaskiya da tsayawa a kanta ba, Sunan ki Barrister Na'ima I Nasir” Ta ƙarasa maganar tana tuna  lokacin ƙuruciyar ta domin da zaran an tambayi sunan ta faɗi ta ke “Ni ce Barrister Na'ima ɗiyar Isma'ila jikar Nasir” Dariya dukkan su sukayi kafin suka ƙarasa zuwa ga jerin gwanon motocin su. Daga baya Amru ne ke biye da ita riƙe da sauran tarkacen ta.

Sauke gilashin motar tayi tana kallon yadda titin yake nan shuru babu zirga zirgan ababen hawa gurin yai tsit waigowa tayi tare da kallon Mimi tana faɗin “Lafiya ƙasar nan take kuwa? garin ya yi shuru tamkar wadda babu rai a cikin sa yanayi na cunkoson ababen hawa na garin Abuja bai kamata a ce garin ya zauna haka ba...” bata gama rufe bakinta taji maganar da ya kusan sumar da ita sa ke kasa kunnuwanta tayi tana sauraron gidan rediyon da Amru ya ka mo inda ake sanar da abinda ke faruwa a ƙasar na sace-sacen yara matasa da ƙananu ƴan ƴan shekara biyar zuwa bakwai, “Innalillahi wa'inna ilaihi rajiun wannan wacce irin masifan ce? Abinda  ke faruwa a ƙasashen ƙetare ne ya shigo har nan Abba! Shi ya sa garin ya zama kamar kufayi babu alamar motsin rai, A matsayin ka na ɗan siyayasa wani irin mataki ku ka ɗauka? Ji nayi ana faɗar harda gawarwakin yara ake tsinta an cire wani Sassa na jikin su” Ta faɗa hankali a tashe  tare da zuba mishi idanuwanta da suka rine saboda tsananin ɓacin rai “Mai ya sa zaki ɗaga hankali a kan ɗan wannan abin Habibty? Abba sunyi iya bakin ƙoƙarin su gashi dai an saka dokar hana fita kowa na gidajensa. Dan Allah karki ɗaura wannan damuwar a ran ki bare har ya ɗauke miki farincikin da kika dawo dashi”
“Maiyasa zan ɗaga hankali fa kace? Amru anya kan ka ɗaya kuwa? wani irin zancen banza ne haka! Ta ya ya za'a dakatar da kai komo na jama'a kun kullesu a gida kun hanasu fita niman abinda zasu ci su ciyar da iyalansu anya wannan adalci ne? Ta haka ne zaku shawo kan matsalar? Tsakani da Allah ba wannan matakin ya kamata a ɗauka ba, bai kama ta...” “Ta wannan hanyar ne kaɗai zamu bi domin kare jama'ar mu, In ba muyi haka ba ai ɓarnan zai yawaita” ɗauke kanta tayi daga kallon Abban nata tana jin babu daɗi cikin ran ta a haka suka ƙarasa danƙareren gidan su dake Sabon wuse  rai a ɓace ta fito ba tare da ta kalli kowa ba ta nufi cikin gida “Barka Barr..” Bata ƙarasa maganar ba Na'ima ta dakatar da ita ta hanyar faɗin “Karki ce min komai abu ɗaya zakiyi wadda zai sa ni farinciki a yanzun” Hajiya Mama tace “Me kenan?” harɗe hannuwa  Na'ima tayi tare da Juyowa tana kallon mahaifinta kana ta ɗauke kan ta, tana ƙoƙarin cire a gogon hannunta ta fara magana fuska a murtuƙe muryanta kuwa kaman zata fashe da kuka domin ita haka Allah ya yi ta, Idan tana magana zaka ɗauka kuka zatayi kasancewarta mai siririyar murya mara amo sannan muryan har wani rawa-rawa ya ke yi, Ga shegen zaƙi da taushi.
“Ki faɗawa Ministar wannan matakin da aka ɗauka bai dace ba, Domin ƙutatawa al'umma kawai za a yi  maimakon haka, Kamata ya yi a tsawaita bincike dan gano Ina matsalar take, Ya kamata su saka ƙwararrun jami'ai waɗanda suka yarda da ƙwarewar su ta fannin aiki domin kamo bakin zaren a sake Jama'a tare da basu taimakon abinda ya  dace na daga dangin su, Abinci da kuɗi  saboda an zalunce su ta hanyar hanasu fita niman abinda zasu ciyar da iyalansu sannan a watsa jama'ai dan lura da lafiyar jama'a”
      “Allahu akbar kaji madarar basira lallai ba a yi karatun banza ba, Kin bada shawarar da ta dace domin kuwa tun farko haka ya kamata ayi Allah yasa dai a daddage a kotu kamar yadda ki ke ta ƙoƙari ka'in da Na'in dan ganin Al'umma sun samu sauƙin rayuwa ina yiwa ƙanwata Habibty fatan nasara”
Murmushi tayi tare da faɗin “Na gode Yaya Farfesa!” tana gama faɗar haka ta Nufi part ɗin ta da gudu domin ta san halin shi na tsare mutane da surutu ita kam bata jin Son magana ɗan farincikin da ta zo dashi duk ya kau sakamakon yanda ta samu garin shuru, Banɗaki ta shiga tare da yin wanka haɗe da alwala babban towel ta ɗauro tana fitowa ta tsaya turus tana kallon Amru domin ta sha'afa tare da shi aka je Airport ɗin “Dan Allah Amru maiyasa kake min irin haka? Na ce maka bana so ka dinga shigo min ɗaki ba tare da niman izini ba” ta faɗa tare da ƙoƙarin juyawa dan komawa toilet ɗin, Taku ɗaya ya yi, Ya riƙo hannunta yana faɗin “Wai me nayi ne da ki ke ta share ni? Shi kenan dan nayi ƙoƙarin rumgumeki  sai ki ɗauki zafi wallahi na fara gajiya da wannan halin da kike nuna min na shariya tunda kika bar ƙasan nan na rasa gane kan ki ina soyayyar ta ke?” a fusace ta juyo tana sake ƙanƙame towel ɗin da ke jikinta hannunta ta fisge tare da sharara mishi mari “Fita min a ɗaki na ce!” Gyara tsayuwar shi ya yi tare da zuba hannayenshi duka cikin Aljihu yana bin ta da kallo tun daga ƙasa har sama Lumshe ido ya yi tare da jan numfashi kafun ya fara mata magana murya a raunane kaman zai fashe mata da kuka “Habibty wallahi na gaji! tunda kin kammala karatun gaskiya maganar Aure za'ayi domin haƙuri na ya kusan ƙarewa bazan iya zuba ido ina kallon ki kina min ƙwalele ba”
Kallon da sauran hankalin ka, tayi mishi kafun ta koma toilet ɗin tare da jingina a kofar tana sauke ajiyan zuciya Lallai tasan tunda ya fara maganar Auren su yanzun to fa za'ayi shi, Dole zata lallaɓa shi ko zuwa nan da Shekara uku ne haka dan akwai abubuwa da yawa a gabanta bai dace ta ɗauko wani maganar Aure yanzun ba “Shi kenan zanje in samu Mommy da batun shurun ki na nuni da amincewar ki..” Dakatar dashi tayi ta hanyar kiran Sunan shi sai dai bai tsaya sauraronta ba ya fita a ɗakin.
Zama ya yi kusa da Yaya Farfesa yana kallon yanda yake cin abinci hankali kwance tsaki Amru ya ja tare da buga table ɗin ido kawai Yaya Farfesa ya tsura mishi na wasu daƙiƙu yana karantar yanayinsa zuwa can yace “Ka ji ɗan isaka zai hanani saƙat nifa bana son wannan halin naku daga dawowarta har kun fara raba hali” Tsaki Amru ya ja tare da cusa hannuwanshi cikin gashin kanshi yana faɗin “Wallahi bro Na'ima zata kashe ni!” Miƙewa Yaya Farfesa ya yi tare da ƙwalawa Hajiya Mama kira fitowa tayi hankali a tashe sakamakon yanda ya buɗe murya yana kiran sunanta tsaban tashin hankali ma zaninta har kwancewa ya yi ƙarshe riƙe shi tayi a hannu tana ƙoƙarin saka madubinta saboda matsalar ido da take fama da shi. Sa ke ware ƴan ƙananun idanunta tayi tana kallon Amru da ya yi kalar tausayi Yaya Farfesa kuwa yana riƙe da ƙugu kamar wata mace, Sadik dake zaune can gefe kaɗan ya rage ya fashe da dariya ganin yadda Hajiya Mama take kallon su, miƙewa shima ya yi yana kiran sunan Mimi ba ƙaƙƙautawa Mimi dake ƙoƙarin tada kabbaran sallah da sauri ta yanke ta fito hankali a tashe jin wannan uban kiran da Sadik ke mata turus ta tsaya ita ma tana kallon su kafin ta fara magana tana kallon Hajiya Mama “Me ke faruwa a nan?”
“Kai Sudaisu maiyafaru?” ɗauke kai Yaya Farfesa ya yi tare da jan kujeran daining ya zauna abincin shi ya ci gaba da ci yana faɗin “Ga ɗan iskan da zaku tambaya nan bansan abunda ya haɗusu da Little da yazo ya sa ni a gaba kamar ƙaramin yaro yana shirin fashewa da kuka ba..”
“Kai! Ƙundun ubanka na ce! Wannan wani irin iya shege ne? Kai ma Amuru ungo nan mangafuntun uwarka kaji ƴan tselen ƙaniya ko, ina ƙoƙarin sallah kun katse ni na ɗauka wani abun tashin hankali ne wallahi har zuciyata ta tsinke” Hajiya Mama ta faɗa tare da hararan su cikin takaicin halinsu Mimi tace “Amma wallahi Allah ya shirya ku yanzun saboda Allah Sudais ka kyauta kenan? Wallahi har na tada kabbaran sallah na yanke  na ɗauka wani abu ne ya faru da mama ashe akan wannan shashashun ne Allah ya kyauta!”
Wani mugun dariya Sadik ya saka tare da ficewa a falon ya nufi masallaci da harara Mimi ta raka shi “Kai kuma Me ya haɗa ku ? Daga dawowarta zaka fara ƙorafe ƙorafe yanzun zaku hana mutane saƙat kamar wasu thom da jere ake cewa ko Jeeri?” Saboda tsananin dariyar abinda tace har ƙwarewa sai da Sudais ya yi da gudu ya fita a falon domin Hajiya Mama zata iya kashe  mutum da mugun turancin nan nata.
“Dan Allah mama ni ki rabani da wannan mugun turancin naki,  Ki taimaka ki shawo min kan Habibty wallahi taƙi saurarona ni fa Ina ga zai fi a tsayar da lokacin bikin nan..” Gyaran murya Na'ima tayi tare da faɗin “Hajiya an fa idar da Sallah” Juyowa tayi tana kallon Na'ima dake tsaye tana gyara zaman agogon dake hannunta kamar zatayi magana sai ta fasa tare da yin ƙwafa ta nufi ɗakinta “Amru zo ka fice min Anan” zaiyi magana ta dakatar dashi ta hanyar nuna mishi lokaci tana faɗin “Maiyasa ba ka fahimta ne? Daga dawowata ko cikakken awa banyi ba ka tasa ni gaba da maganar Aure. Ai zaka min uzuri zuwa har na huta gajiyar hanya amma kazo kun haɗu da su Yaya Farfesa harda Sadik kuna ɗagawa mutane hankali, Wallahi ko da naji wannan kiraye-kirayen da kuke na ɗauka wani mugun Abu ne ya faru Dan Allah kaje gida kuma ka kwantar da hankalin ka tunda na dawo ai komai ma kamar anyi an gama ne” Gauron numfashi ya sauke kafun yace “Wallahi sai yanzun na ɗan ji sanyi cikin zuciyata Amma Habibty Please ki dai na min wannan halin Allah ina cutuwa da yawa” Ɗan murmushi tayi sannan tace “In Sha Allah za'a kiyaye ka miƙa gaisuwata zuwa ga Mima kafun na shigo”
  “Okay bye sai munyi waya ko?” Jin kaɗan tayi kafun daga bisani tace “Zanyi ƙoƙari na mayar da layi na kafun zuwa An jima” fita ya yi tare da yin Hamdala domin har hankalin shi ya fara tashi duk tunaninshi yafi raja'a akan tayi wani saurayin da yafi shi ne” Abinci ta ɗan tsakura kaɗan kana ta nufi ɗakin Mimi acan ta saka SIM ɗinta gyara zama tayi tare da sake ka sa kunni tana sauraron Jawabin da ake runtsa idanunta tayi da ƙarfi tana jin ɗaci a zuciyarta “Habibty Lafiya kike kuka?” Tv ta mata nuni dashi tana sake jin yanda hawaye ki zariya akan fuskanta “Mimi yarinyar da bata wuce shekara goma sha biyu ba akayiwa Fyaɗe Mimi kin tuna lokacin da irin haka ta kasance da...” Kasa ƙarasa maganar tayi sakamakon shaƙuwan data fara cikin tashin hankali Mimi tayi kanta tana faɗin “Innalillahi NA'IMA! Na shiga uku wannan wacce irin masifa ce daga dawowar yarinya za'a shiga razana min ita!” da gudu ta fito tana kiran Hajiya tare da Sadik domin Sudais ya tafi gidan shi a guje suka koma ɗakin Mimi nan suka iske Na'ima zaune lafiya ƙalau tana danne danne a wayar Mimi turus suka tsaya nan Hajiya da Sadik suka shiga kallon Mimi “Mariya kika ce Na'ima ta suma?” Gyaɗa kai Mimi ta shigayi tana sake yi mata nuni da Na'iman  “Eh ita ce mana kallon tv fa take daga haka naji tana maganar fya fya..” Ji tayi kamar an riƙe mata maƙoshinta tana ta ƙoƙarin ƙarasa maganar Amma ta kasa kalman fya fya kawai take faɗa Na'ima kuwa tsura mata ido tayi tana kallon bakin Mimi dake motsi domin gabaɗaya bata fahimci akan me suke magana ba.
    “Lafiya naga duk kun ruɗe kuna surutu akan abinda ban fahimta ba?”
Kama haɓa Hajiya Mama tayi tare da gyaɗa kai tana sake kallon Ni'ima “Allah ya kyauta” kawai Hajiya tace sannan ta fita a ɗakin jiki a sanyaye Mimi ta zauna kusa da Na'ima tana so tayi magana amma gabaɗaya  tsoro ne fal zuciyarta haka tayi shuru tana saƙa da warwara har wani gajeriyan barci ya yi nasaran ɗaukan ta.
  Ɗaukan wayarta tai tare da kiran Amru nan suka sha hira daga bisani ta fito a ɗakin ta nufi ɗakinta.
Washe gari da sassafe ta shirya saboda kiran gagawa da ƙawarta Na'ilah tayi mata akan wani case ɗin Fyaɗe da akayiwa matashiya ƴar shekara Goma sha biyar, “Mimi barka da safiya Hajiya ya jikin tsufa Yaya Sadik barka” Kallon ta Sadik yai yana faɗin “Barr daga dawowa har za'a fara aiki?” Ajiye cofin tea ɗin tayi tana girgiza mishi kai “Ba aiki bane zanje na naga ko zan samu tattauna da wacce abin ya faru akan ta”
  “Okay na fahimta Amma kunyi waya da Suhaiba kuwa? Dan tace min tana ta kiran wayar ki baki ɗauka ba”
“Ɗazun da Amru ya kira munyi magana da ita bari naje lokaci na tafiya har takwas tayi”
Mimi tace “Allah ya bada Sa'a” da murmushi ta amsa tana kallon Hajiya “Hajiya kinyi shuru baki ce komai ba” yatsina fuska Hajiya Mama tayi tare da faɗin “Kin ci ƙaniyar ki jiya ina miki maraba da zuwa ba gwale ni kikayi ba. Sai yanzun ne zaki min  magana” Harɗe hannuwa Na'ima tayi a ƙirji tana kallon Hajiya dake magana tana haɗa baki da hanci dariyan da take ta ƙoƙarin riƙewane ya ƙwace mata aikuwa nan ta riƙe ciki tana darawa “Sorry Mama wlh jiya naji babu daɗi ne akan abinda Dad ɗin Amru sukayi shiyasa farincikin na wa suka gushe Amma kiyi haƙuri Anjima zamuyi magana dan so nake ki bani tarihi da labarin wancan Uncle ɗina da har yanzun ba'ajin ɗuriyarshi ba..” tun bata dasa aya a maganarta ba Hajiya Mama ta fara fyace hanci tana mutsike idanunta. Miƙewa Sadik ya yi tare da jan tsaki yana jin takaicin haramta mishi Abinci da Hajiya tayi “Ungo nan ɗan tselen ƙaniya kasan kalan ƙazantar da kayi san da kake ƙarami? Kai lokacin da kake ƙoƙarin yin haƙori kashin ka ma sai da ka ci....” da gudu ya fita yana kakarin amai dan lokaci ɗaya zuciyarshi ya hautsine “Innalillahi Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri kin san halin Sadik da ƙyanƙyami gashi ɗan abinda ya ci zaki sa ya amayar dashi wlh kina da matsala wani lokaci”
Kallon Mimi Hajiya tayi tana faɗin “Ki shiga tsakani na da waɗannan ƴan nunusins ɗin” (Nonsense take nufi) hannuwa bibbiyu mimi tasa a baki tana ƙoƙarin tare dariyan da yazo mata kai kawai ta gyaɗa tana yiwa Na'ima nuni da ƙofa akan ta tafi “Dalla ki ƙyale mutane da wannan arnen turancin naki su waye Nonsense ɗin?” Sudais da ke tsaye a bakin ƙofa ya faɗa yana kallon Hajiya Mama “Kai Sudaisu Bi kwayet!” Ai ba shiri mimi ta tashi tare da kama hannun Sudais tana dariya ƙasa-ƙasa, “Dan Allah Sudais rufa min asiri kasan Hajiya sarai da ƙuluwa yanzun sai tace na koya muku rashin kunya” dariya ya yi tare da juyowa yace da Hajiya “Be quiet Grandma”
“Innalillahi! Ke mariya kina jin rashin kunyar da yarannan suke gwada min ko, Yanzun wani mugun zagi Sudaisu ya yi?” cike da jin Haushin Abinda ta mishi Sadik yace “Yana nufin zai ƙwamushe sauran ƙananun idanuwan da suka saura sannan zai sace bakin surutu..” “Kai Abbakar! Bana son shashanci Hajiyar Sa'arku ce da zaku dinga mata haka? Take care! Kar na sake jin wani magana a nan Dan Allah Hajiya kiyi haƙuri” miƙewa Hajiya tayi tana matsar ƙwalla domin sun gama da ita, gyara zaman madubinta tayi tana gyaɗa kai tafiya take tana faɗin “Ko menen fassaran mugun kalman Tiki cari da Mariya tace oho ni dai waɗannan yahudu da nasara basu kyauta min ba, Haka Sama'ila magana ɗaya biyu sai ya haɗa da kalman turancin nan, Bari Na'imatu ta dawo nasan ita ce mai ɗan nutsuwar da zata mini bayani yadda zan fahimta.

Ku tsumaye shi, Zai zo nan bada jimawa ba

08062715485

Follow me on Wattpad: ayshajb
Fallow me on Facebook: Ummi JB
Comments
Share
Fisabidillahi..

Maman Faruq

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Dec 19, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

WA ZAN KARE..?Where stories live. Discover now