BABI NA DAYA

691 18 0
                                    

. . . . . . ⚜  ❣    ⚜  ❣       ⚜                                                                                                  ⚜❣❣ ⚜❣❣ ⚜ ❣                                                                                                                  ⚜  ❣     ⚜  ❣       ⚜

                  ⚜
         ❣ ⚜ ⚜❣
                  ⚜               
  *❣RABUWA CE  SANADI❣* 
                      
*_⚜BY QUEEN MEEMI_*⚜
                ❣1❣                   

            

*©Mymounerh Basheer*

*®NWA*




*Queenmeemi.WordPress.com*

***************

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

  *_k'aramar hukumar bunkure,dake jihar kano_*
 
 
Babban titin dake garin bunkure wanda ya cika da d'aukacin jama'a kowanne ka kalli fuskar sa arazane yake wasu kuma gudu suke ci,ga wasu a kwance dai-dai kusa da wata Babbar mota na gano yarinya
Yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniyaba a zaune kusa da wata mota sai ihu take,Jikinta sai karkarwa yake kukan natan  Sam baya fitowa sabili da taci kukan harta k'oshi.

       Daamm!!!  k'ara  ce ta kuma tashi, take mutane suka hau guje-guje yarinyar da Bacci ya fara d'ibanta ta tashi firgigit ta k'wala k'ara ba wanda yasan tanayi gudu ta hauyi irin Na yara bawanda ke  Kula taa kowa ta kansa yake ,ke sai kiran momy take da dady ,wata mota ta gano gurin tayi aguje
taje aguje tana bubbugawa dady! dady! neman iyayenta take Amma ko alamarsu Babu ga wajen ya hargitse kowa takansa yake Saboda tashin bomb din da akaji wanda yazamo tamkar wata jaraba gun wani mutumi ta yi ta baya da gudu tayi wajensa tana dady.
juyowa yayi a tsorace yayi arba da ita , yana  shirin magana k'arar bindiga ce tafara tashi tas! tas! tas!  tas! kakeji nan da nan waje ya kuma hark'ewa hayak'i ko ta ina.
yarinyar da duk Jikinta yajike da fitsari ga bakinta Na jini ,mutumin nan ya falfala yafara gudu ,yarinyar tabiyoshi dady! dady! sojojine suka tawo aguje suna harbi nan da  nan mutumin yai wata kwana yarinyar tabishi tana ihu inda ya b'uya taje ta tsaya ta dafa shi "dady momma"  hankad'eta yayi  yace "Yau naga jaraba ke ina iyayenki? ana wann nan  tashin hankalin  don sakaci", tureta yayi  yace ta bar wajen, tafiya tayi da gudu tayi wani waje  tai kwana tana  sangal-tangal  saboda ciwo dataji  a k'afa wani yaro ne ya arto yana haki yai ciki da ita ta fad'i k'asa d'agowar da Zatai akai harbi Allah ya taimaketa ba aharbeta ba Amma tsoro yasa ta suma ganin hakan tausayi yakama mutumin ya fito Daga mab'uyar sa ,yazo ya  d'auketa ya
runtuma  aguje yana gudu seda yayi nisa yaje motar sa dake ajiye  ya ajiye ta agaban mortar  dayake motar d'aukan kayace  yara su hud'u ya ganni  a bayan motar sai ihu suke ya kallesu yace " ina  iyayenku"? D'aya ne mai wayo yace "nan mukazo muka b'uya",Sauran kwa ba wanda yayi magana sai kuka duk jikinsu k'ura da d'an Jini-jini ajikin su,jin- jina kai yayi kawai ya shiga motar.


     
************
     *K'auyen mangalu*
                           
Jan motar yayi ya fafara aguje nan yiyi hanyar k'auyensu tafiyar awa d'aya da rabi ya kaishi k'auyen mangalu wanda yake a k'ark'ashin k'aramar hukumar bunkuren, Bayan yaje k'auyen nasu su, take bai zarce ko ina ba sai tasha,ya bud'e motar ya fita yaran yad'ebo, ya sauke su gaban motar yaje don d'auko yarinyar wayam ya nemi yarinyar ya rasa neman duniya yayi bega yarinyar  ba mamaki k'arara  afuskarsa "kode aljana ce tsuka yaja inajin Aljana ce
sede ko sauka tayi",nan yayi ta dubawa bai ganta ba
Sarkin kasuwa ne yazo aguje  "Malam lado me nakeji ne agari wai cikin gari bomb ya tashi da Gaske ne kuwa"?

"Tabbas! hakane Sarkin kasuwa Ni kaina wallahi abun yaban  tsoro, lodi fa nake zan kai kaya kasuwa kawai mukaji k'arar tashin bomb ai Wallahi munga tashin hankali don an mutu agun ,dak'yar Na sha,kaga kuwa abin tausayi harda wata yarinya dana gani
agun  sai karakaina take tana neman iyayenta kawai sai yarinya  ta dinga bina tausayinta yasa Na d'auketa abin mamaki munzo nan Daga sauka din na sauke  yaran can na duba bangan taba".

"Allahu Akbar Allah ya k'ara kiyayewa" sarkin kasuwa  yafad'a Yaran nan su hud'u malan lado ya mik'awa Sarkin kasuwa da  bashi dubu d'aya kan akaisu Police station da ke cikin garin bunkuren ko za asamu iyayensu , sarkin kasuwa yace wa wani d'ahiru ya rik'e yaran ya basu abinci shida MLM lado suka hau dube-duben neman yarinyar nan ,Amma basu ganta ba ,nan suka dawo lokacin yaran Sunci Sun sha MLM lado ya deb'e su sarkin kasuwama ya shiga motar .
   
Sun fita titi caraf idon sarkin kasuwa ya gano masa yarinyar nan gefen titi da Rabin bread a hannu tana ci tana kuka,yace "hala dai ita ce waccan"?  Malam lado yace "ita ce" direct motar ta tsaya suka fita abin tausayi jikinta zafi zau suka d'auketa,sunje police station suka bada yaran kan b'atansu a dalilin tashin bomb d'in ,sunayensu a ka d'auka da hotuna,da yake gidan sarkin kasuwa anan yake yasa aka bar yaran a gidan nasa,su kuma 'yan sanda suka hau sanarwar neman iyayensu. malam lado ma ya tafi kan duk yanda akai  Skasuwa  ya Sanar mai.
   
   
    *by Queen meemi*

RABUWA CE SANADITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang