NEEMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)

224 17 1
                                    

🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔

          *NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄

*YABO*
_Dukkan yabo da godiya ya tabbata ga Allah madaukakin tsarki daya bani ikon karadawowa a wani sbon littafina mai suna *MAJI MA GANI*_.

*GODIYA*
_Godiya ga masoyana wayanda basa gajiya da bani karfin gwiwa wajen rubutuna dabani shawarwari na kwarai banida kaman Ku kune ni nice Ku_.

*JINJINA*
_Jinjina ga marubuta OHW gaba daya kun chanchanci jinjina, tabbas a fadin yanar gizo kuna taka rawar Gani musamman wajen fadakar da masu karatu Allah ya hada kanmu gabaki data Amin_.

*INA KAUNARKU IYAYENA*
_Babu abunda zance saida fatan Allah yasa Ku gama da duniya lafya yakara muku lafya da wadatar zuci *HJY DIJE WADA MANZO da DR MB SHEHU*_

_FADAKARWA_
*_Wannan littafin k'agaggen labarine ba'ayishi don wani koh wata ba sbd hk aguji zargi Anyishi ne don ya isarda sako zuwaga masu karatu_*.

*January 2017*
1⃣

       Hantsi ne mai cikeda tsananin hazon daya mamaye dokacin garin dake gauraye da tsantsar sanyin dake ratsa b'argo tamkar zai daskarar da jini, Wannan sauyin yanayin yasanya ilahirin garin ya kasance tamkar farkon safiya, in banda alaman kewayayyen rana dake mak'ale a sararin samaniya tamkar tamaula haske zafin ranar Nada tsananin rangwame ta yadda ko hazo baya iya ketowa balle ya buwayi doron kasa.

Mutum zai iya kurawa hasken Ranan ido batareda yayi k'walla ba, Sadi yana tsaye da wata bakar kwat wadda farin wandon dayasa ya dace da rigar. Duk da rigar mai dumi ce sadi ya harde hannayensa alaman sanyi yakeji, jingine yake da bagon gdansa, dake unguwan gwamnati ta kabuga da aka ware musamman ga ma'aikata masu rangwamen karfi.

Tsayawa yayi yana hangen wata jar end of discussion datake dunfaro shi da alama yasan mai motar murmushi yakeyi har motar ta iso gareshi, da sauri ya matsa kusada motar yace "Abokina Salman Kaine da sassafe haka Allah yasa lafya yadda naga fuskarka babu alaman wasa a tattare da ita"?
Salman yace "Look my guy ba surutu yakawoni wajenka ba nazone akan maganar data shafeni".

Sadi daya gaji da mamaki atsaye meye
Dalilin Salman nazuwa da irinnan wannan halin, Wanda bansanshi dashi ba tambayar dayake yiwa kansa kenan kodame Salman yazo nasan ba alkhairi bane amma barina bashi Dama don yafadi zuciyarshi.

Dubinsa yakaiga Salman yace meke tafe dakai?
Salman ya gyara tsayuwarsa           "yace meye ke tsakaninka da NASRIN kanwata"?
Sadi ya kasa cewa komai da fari, daga baya ya tattara hankalinshi waje guda yace "Yanzu salman saboda wannan maganar ne kazomun har kofar gda da turbunanniyar fuska."

"Mene ne tsakaninka da ita kawai na tambaya ba dogon jawabi ba allaranma"
Yayi tunani nadan lokaci sannan ya kwantar da kai yace "budurwata ce in abinda kakeson ji kenan".
Salman ya zare ido yace
"Budurwarka ce?"
Cire Glass din dake idonsa yayi yace "Wato tsatsuniyar da nakeji yazama gaskiya kenan"?.

Sadi yace "Kwarai Nasrin budurwata ce kuma inasonta so na tsakani ga Allah baso na cin amana ba kona yaudara".
Salman yace
"Tsawon wani lokaci kuka kulla wannan alakar?"
Sadi yace "Mum kulla alaka tun alaka Dana dadii"
salman yace 
"Sadi ka cuceni ka ha'inceni kaci amanata yau dara taci gida Ashe duk abunda muk'ewa yayan mutane za'ayiwa kanwata uwa daya uba daya kuma abokina"?

Sadi yace "Look salman karfa ka fassarani ta hanyar dabashi bane yaza'ayi inci amanar Nasrin bayan itace farin cikina Wallahi akan Nasrin zan iya barin komai kuma nasan cewa Nasrin baxata juya mun bayaba saboda nasan tana sona kuma nima inasonta sona hak'ik'a",
Salman yace
"Wallahi karya kakeyi kayi kadan Wallahi *neesma'a wah nushuuf* ( maji ma gani) Sainayi komai don ganin na rabaka da Nasrin saboda bata dace da Humanizer ( manemin mata) irinka ba".


©ZAZZAU😘

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 24, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NEEMA'A WAH NUSHUUFWhere stories live. Discover now