chptr 31-50

3.9K 99 0
                                    


31-32

  Su Anty Hadiza ma suka taya ta gaskiya bai kamata ba, ka kira Suleiman din ya tafi da ita kaga mu sai mu zauna kawai. Sadiya da take labe a bayan sa tana kuka duk haushin su take ji, Abba ya juya da ita zuwa dakin sa ya daga wayan sa ya kira Suleiman akan neman sa yake da ya sauke wayan ya dubi time har tara da rabi ya kusa. Witten 15min. ya isoshi gidan yayi sallama ya shiga falon Abba da mama ne suka sa yar su a gaba suka sauna sai nasiha suke mata shima din Suleiman ya shigo wa ya samu waje ya zauna akasa kusa da Abba. Abba ya dafa kafadan sa kaga 'dana abun da nake so dakai  ga matar ka Ku tashi Ku tafi gida yanzu Allah yayi muku albarka, ya baku zuri'a dayyiba. Ameen abba mungode. Babu wani bata locaci ya mike zai fita sai kuma ya juya yana kallonta. Sam babu alaman zata tashi, mama da ta lura da taurin kan yar nata ta mike ta dago ta suka yi waje.
 

   Inda yayi parking motarsa suka dosa Abba ma ya biyosu. Suleiman yayi sauri ya bude mata front door seat sai da tazo zata shiga kuma ta juya da gudu tayo kan mama tana kuka, itama mama sai da zuciyarta ya karaya tana tausayin yar nata Abba ya zo ya jata zuwa motar ya shigar da ita rike rigarsa tayi wai bazai tafi ba. Yayi kokari ya kwace rigar sa ya tura mata kofar ya kulle ta kai hannu zata bude Suleiman yayi saurin danna central lock takasa bude shi sai ta kukan ta take. Abba ya daga musu hannu Suleiman ya ja motar suka fita daga harabar gidan. Haka ta hakura da kukan dan kanta tayi shiru. A bakin titi yasamu ya sauka ya siya musu kaji da drinks masu sanyi suka nufi hanyar gidan su.

   Suna isa gate  man ya bude musu suka shiga yayi parking ya sauko itama ya bude mata kofar ya na jiran ta fito amma taki ya mikar da hannun sa ya kamo nata, warce hannun ta tayi daga rikon da yayi mata ta dauke kanta daga direction dinsa. Durkusa wa yayi a gabanta yana kallon ta, Sadiya ban dauka zaki kini a matsayin mijin ki ba. Zaman da mukayi da shakuwan mu a baya kina nufin ba komai bane a wajen ki, kisani fa ni masoyin kine, bazan so miki abunda babu alkhairi a cikin ta ba ni nadace da ke. Yanzu ki tashi muje daga ciki. Kallon sa tayi ta danka masa harara murmishi yayi ya kada kansa ya mike ya tsaya kallon ta yana jiran ta fito yayi gefe yana mata nuni da hannu alamar ta fito still tana zaunan ta da ya lura fa bata locacin sa za tayi ya sun kuya yakai hannunsa zai dagota ta ture shi. Sai da yayi dabara yasamu ya dankota ya rike ta mai kyau ya dagata cak ya nufi cikin gidan da ita, shure shure ta ke tayi ni ka sauke ni bana son iskanci shi dariya ma ta basa tana tayin masifar ta har suka ido cikin dakin ta direct kan gadon ta ya duro ta tana huci sai kace ita tayi wahalan dauko sa.  

Ajiye ledojin hannun sa yayi akan chess of drawer ya sunkuya ya kama kafanta jikinta ya fara rawa atake ta rikice tana jan kafan baya ya dago yana kallon ta da mama ki kamar yayi dariya sai kuma ya danne, tana ganin sa ya fara yaye mata kasan skirt runtse idanunta tayi da karfi zata fizge kafan ya rike ta ki tasya mana, ya danko kafafun dukka biyu ahankali ya cire mata half shoe dinta ya ajiye a gefe ya yatsura ido wa tafin kafan da ya sha zanan lalle yashafa su da hannun sa yace tabarakalla nagode wa ma halicci da ya mallaka mun mai wannan halittun kafa masu kyau sai gashi an masa ado da lalle ya kara masa kyau da haske, wannan adon duk ni akayi wa. Bude idanunta tayi ta sauke su cikin nasa, ni dai kafafu na ba naka bane ta fizgo su. Toh ai nima ba wai nace nawa bane cewa nayi mallakamun su Allah yayi ko ba mallakina bane ke, dauke kanta tayi ta matsa gefe daya. Wai da kin dauka mezan miki ne takalmi nazo cire miki fa dariya ya mata ya tashi ya cire hulan sa ya mika mata, kin karba tayi ta tsaya kallon sa, karba ki ajiye ki samu lada man kauda kanta tayi. Murmishi kawai yayi ya ajiye hulan gefen gado ya nufi toilet dan ya dauro alwala. Da yafito haka ya sameta inda take kamar yadda ya barta. Je kiyi alwala muyi sallah, ni nayi sallah na a gida, eh nasani nafila zamuyi, toh bana sallan baki ya sake yana kallon ta sai kuma taji kunya, ba don sallar ibada bane da har ga Allah ba tayi niyar yi ba ta miki ta shiga bayin. Kafin ta fito har ya shimfida musu sallaya ya zauna jiran ta.

  Nade laffaya a jikinta tayi ta tsaya abayansa ya jasu sukayi raka'a biyu ya musu adduo'i yace da ita zo na shafa miki addu'an kin kula sa tayi kaman bata ji sa ba. Tashi yayi ya fice daga dakin dan dauko musu cups da plate a kitchen. Da ya dauko yazo shi zai bude kofar dakin ya jita gagam akulle ha'a sadia kwankwasa wa yayi sadia kina jina bude kofar mana knocking ya kuma yi nan ma shiru. Fitarsa tayi locking kofar, ta dauko night gown dinta daga akwati ta saka ba a jera kayanta cikin wardrobe ba tukunna. Kan gado ta haye tayi kwanciyar ta. Sadia bude kofar mana wai lafiar ki, daga muryanta tayi yanda zaiji lafia ta kalau barci zanyi sai da safe. Daskarewa yayi dan bai zaci za tayi hakan ba, toh haka zaki kwanta da yunwa baki ci komai ba plate fa naje ni dauko mana a kitchen, bude ki karba idan kika ci sai ki kwanta. Manna masa tayi haka ya gaji ya bar kofan ta ya wuce dakin sa.

Banaji Bana Gani Where stories live. Discover now