MATAR FAYROUZ. P1-5

5.5K 235 5
                                    

( _*MATAR FAYROUZ*_ 👸🏼)

'  ̄ ̄🐬 ̄O  ̄. ̄ ̄ ̄

🐳 。 o 🐟 *


_Written by *Asy Khaleel*_ 👄


_The Whole Book Is Dedicated To *YA HAJJA CE* Ke Kikafi kowa Chanchanta, banda abun biyanki sedai dubin addua tare da fatan alkhairi agareki da zuriarki_

_The whole book tukwici ne agareku iyaye nagari *Aunty Sis N Aunty Maijidda Musa* Asy'nku na godia da soyayyrku agareni, ngd sosai_

*HASKE WRITERS ASS...* 💡
_Gaisuwa ga y'an kungiyarmu_

*7th OCTOBER, 2017*
*Birthday r nature' s way of telling u 2 eat more cake. Birthday r lyk boogers. d more u have d harder it is to breathe anoder year older, none d wiser. Bday r jst finger posts on d road of getting old. I was born wit a gift of awesomeness I'm jst a year older I'm also a year beta n prettier. I knw u r jealous. I'd lyk 2 thank my mom 4 making dis miracle possible. ITS MY BDAY*.

*BOOOOOM, yes💃2day is my bday. Therefore I will treated lyk a QUEEEEEEEN* 👸🏼

_Ya Allah ka bani ikon Fara wannan takaitaccen littafin tare DA kammalawa lfy_.

بسم اله الرحمن الرجم

1⃣-5⃣

SHIMFI'DA

AGEGE - LAGOS STATE

*J*ahar Lagos gari ne mai girman gaske wanda yake cikin sahun farko a Nigerian, Wanda a da yake matsayin headquarter d'in Nageria gaba d'aya wanda har yanzu tana ci gaba da haskawa kasan cewar gari ne na cibiyar kasuwanci tare da yalwar mutane daban-daban daga garuruwa wanda ya had'a da y'an Arewa. Domin garine na neman kud'i ba dare ba rana.

***

Aiki take yi sauri sauri dan ta k'agu ta gama mahaifiyar ta tace
"Afshaan Saurin me kike yi ne haka da baxa ki min aiki a tsanake ba?"
Afshaan cikin kumbure-kumbure take magana,
"mama na gama fa kuma nace miki xani gidan su Najmah."
Mahaifiyar tata tace,
"wai ke kullum ne se kinje gidan su Najmah kamar ibada ne? to ba inda zaki je."
Afshaan tayi narai-narai da Ido dan tasan ba karamin aikin Maman ta bane ta hana ta zuwa gidan su Najmah, tana magana cikin sigar tausayi tana rokan mama dan ta bar ta taje, mama tace,
"to shikenan Saura ki dad'e."
A guje Afshaan tayi hanyar d'aki ta d'auko gyalenta,
"Mama sai na dawo."
mama tace "a dawo lafiya saura ki kai dare kamar yanda kika saba."
Afshaan kuwa tuni tayi hanyar waje bata saurari me Mama tace ba.

_Sauri-sauri take tafiya dan ta kagu ta isa gidan su Najmah duk da ba wani ta zara ba ne dan layi d'aya ne a tsakanin su, Afshaan ta shiga da sallama,
"Umma ina yini?"
Wanda aka k'ira da Umma ta amsa da,
"lafiya qalau Afshaan ya maman ki?"
Afshaan tace "tana lafiya tana ma gaida ki"
Cikin fara'a umma ta amsa da "Ina amsawa." Afshaan tace.
"Umma ina mutuniyar tawa tana nan kuwa?" Umma tace "eh tana ciki."
Afshaan tayi murmushi tace "umma bari na shiga"
umma tace "toh."

Afshaan ta shiga d'akin da sallaman ta ta samu mutuniyar tata ta dukufa sai chatting take baji ba gani bata san ma Afshaan ta shigo ba, se ji tayi an fisge wayar ta, a fusace ta juya xata fara masifa sai taga Afshaan.
"oh Afshaan kece dallah can ban waya ta."
Afshaan tace, "ke dai da chatting sai a slow." Najmah tace "baki san dad'in ta bane shi yasa bani wayar kiga abunda nake yi" Afshaan ta mika mata wayar ta zauna kusa da Najmah, Najmah tace,
"kinga wannan ankon?"
Afshaan tace "kai amma yayi kyau ankon waye?"
Najmah ta galla mata hararar wasa
"oh baki da labarin Alhaj Shehu zai kara aure?" Ga shi maganar auran sa ya bi gari ko ina kaje maganar auran sa ake yi. Abunka da masu hannu da shuni."

_Afshaan ta washe baki tare da cewa, "to ina kuwa zanji yaushe ne bikin?" Najmah tace "next week ne, ke ai dole ne muje bikin dan kuwa har da ankon zamu yi muma" cewar Najmah, "kai har nawa ne naga Babban less ne fa?" cewar Afshaan, Najmah ta ta6e baki tare da cewa. "20k kin san bikin manya Sai da ankon." ido kwala-kwala Afshaan ta fiddo waje "ina zamu samu 40k nida ke?" Najmah tayi dan guntun tsakin takaici tace,
"Ni fa dad'i na da ke saurin karaya, bashi zamu ciyo mu siya kwalliya zata biya kud'in sabulu a gurin bikin."
"shegiyas..!! suka tafa "kanki na wuta fa" cewar Afshaan. Najmah tace "zauna tunda baki san dawar garin ba." Afshaan tace.
"tunda ina tare dake hankali na kwance."
"ah to"
Cewar Najmah.

_Afshaan ce ta nisa sannan tace "to Najmah ina zamu ciyo bashin kayan?" Hankali kwance Najmah tace shagon Afreen zamu ba zata rasa ba dan jia naga an kara lodo wasu lesikan.",
Afshaan tace "kai kai Najmah kin manta tace ba zata kara bamu bashi ba wancan da yaya muka biya nikam ban san ta kara mana tijara irin na kwanaki."
Najmah taja dogan tsaki "kar Allah yasa ta bada waye becin bashi, ai yanzu ba'a fushi da customas, Muje shagon Hajia Xoxo ai mun kwana biyu ba muje ba."
"kan bala'ee walahi ba dani ba ai gwanda Muje shagon Afreen d'in, dan Hajia Xoxo ba ta da Mutunci.

_Dallah can tashi Muje uwar tsoro kawai." .......cewar Najmah_




*domin samun next page ba tare da 6ata lkcn ba, maza garzawa wattpad* @asykhaleel

MATAR FAYROUZ ??Where stories live. Discover now