2

964 55 17
                                    

*HANGEN DALA*..

*©Feenat Ja'afar*

4_"Biyu kawai za ki sha,in dai kinga jini toh ya fita,sai ki dawo a miki wankin ciki.
Kai ta kada tare da zungurar Esha halamun su tafi.
Suna fita ta tsaya ta amshi ruwa tare da balle magani guda biyu.
"Ki sha hudu,ta yadda zai yi saurin markado cikin..
Jim tayi tana kallon Rascon,kan daga bisani tabi umarnin Rasco ta ketare na likita,fatan ta cikin ya 6are ta huta zulumi.

Da kyar suka dawo gida sakamakon yadda mararta ta daure lokaci guda.
"Wayyo Allah..
Ita ce Kalmar da Baba Ladi ta fara ji lokacin da suka shigo parlor.
Da azama ta miki ganin yadda Eshan ta rike mara tamau tamkar zata cireta dan azaba.
"Mey ku ka yi Hajiya?
Harara Rasco ta kwada mata tare da fadin
"Ki bamu guri..

Kafa daya ta daga kamar mey koyar tata ta durkushe gun jin wani azababben ciwo.
"Innalillahi...mey zan gani? Kamar jini...
"Dalla malama ki kamata mu hau da ita sama,kin tsaya iyayi da fadi ba a tambayeki ba.
Cikin kallon takaici take kallon Rascon,tabbas bata ga fitarsu ba,ashe sai da suka je aka cire cikin nan?

"Zan mutu..
Da azama tai kanta tare da tallafota,kan kace mey tuni har ta baci,irin yadda ta zubar da jini shi ya nuna mata tabbas bari ne.
Taji jiki kam,kamin daga bisani ta dan watsake kwana biyu suka koma ga likita.
Haka tana ji tana gani akai mata HSG,wata sabuwar azabar.
Sati biyu kamar ba ai komai ba,dan ta wartsake sai abinda ba'a rasa ba,koma mey tunda burinta ya cika mey sauki ne.

"Sai ki kiyaye gaba,koh da ya dawo na fada miki kar ki fadi mishi komai, aja a lullube tunda ya fadi.
Kai ta kada tare da amsa Auntyn.
Jim tayi bayan sun gama wayar tana tunanin rayuwarta,sai dai ta gaza gano dai-dai take koh akasin haka,koma dai meye tasan a duniya yanzu bata da kamar Aunty da Rasco,dan su kadai ke iya fiddata duhu.

Sunayen kan wayarta take bi da kallo
"Swthrt" ta kamo,dan haka tuni ta hau tunanin yaushe rabon da ya kirata da sunan zai ji lafiyarta?
Sai dai ita ta kira.
Cigaba tayi har ta dira kan 'Umma'
Tsam tayi,kamar kar ta danna sai dai ta danna tuni har idonta ya cika da kwalla.
Har sai yaushe Ummanta za ta daina fushi da ita?
Hawayen ne ya tsalalo lokacin da ta fara ringing.
Tasan har ta katse ba dauka za tayi ba,sai dai hakan baya hana ta sake kira.

Zama ta gyara da mamakinta ganin an daga yau a karo na biyu tun bayan aurenta.

"Um Umma...

Murya na karkarwa ta hado sunan hawaye na kwarara.
"Tun yaushe zan fada miki ki nemi wata Umman bani ba?
Kuka ta fashe dashi tare da fara magiya
"Dan Allah Umma ki yafe min,wallahi bani da wata sama dake nasan nayi miki laifi amma..
Kit aka kashe wayar daga chan.
A hankali ta zame wayar daga kunnenta hawaye na zuba bisa screen din.

A dalilin Bilal ta saba da mutane ba dadi ta sani.
A dalilin kin auren Bilal da yawa sun yanke alaka da ita.
Mahaifiyarta
Kawarta
Danginta
Kai da duk wanda ke goyon bayan Bilal sai da tai hannun riga dashi.

"Yanzu da mey ki ka karu a aurenan?
Jim tayi tare da shiga tunanin shin mey ta tsinta a zaman shekara da tai a gidan Alhaji?
"Kudi da kece rainin da ki ke fata duk kin samu...
Hawaye ta goge tare da murmushin takaici jin amsar da zuciya ta bata.
Karshen rabuwarsu da Zahra ta tuna

_"Wallahi bazan halarci aurenki ba mudin ba da Bilal bane Humaira,da cin amana aciki cike da yaudara,ki tuna fa kawun Bilal ne,ki bude idonki kiga gaskiya_...
Ta tuna tsaki tayi,kamin ta hau bata zazzafar amsa
"Mtwss...
_"Allah ubangiji yasa Babanshi sai na aura..kuma dubunki zasu halarta in ke baki zo ba,hakan kuma shi zai nuna min kina bakin ciki da na samu miji kuma mai naira,dama ansha fada min bana yarda sai yau da ki ka firta da bakinki,dan haka Umma ta gaida Aysha aure ne nayi na kare_..

Da hannu ta nuna kanta idonta cike da kwalla.
_"Humaira..._
Kugu ta rike tare da juyar da kai gefe tare da kin amsawa,dan haka cike da bakin ciki hawayen idon Zahran ya gangaro kuncinta.
_"Dama da ranar da za tazo ki iya min wannan zaton?.._
Banza ta mata,dan haka sai ta kada kai tare da murmushin takaici hadi da goge kwallar.
_"Nasan za ki gane watan wataran,yanzu idonki a rufe suke ba zaki ta6a yarda da nasihata ba.._
_"Sai dai abu daya nake son ki sa a ranki Humaira, wallahi hakkin Bilal kadai bazai barki kiji dadin gidan aure ba...dole ne sai Allah ya mishi sakayya,na kuma gode da tukuicin abotarmu.._

Ta tuno har kofar gida ta rakota tana fadin
_"Aniyar moda tabi randa,in kinji haushi kije ki ce ya aureki man sai ki burgeni.._
Kuka Zahran ta fashe dashi tare da barin harabar gidan ita kam ta inda take shiga ba tanan take fita ba.

Ajiyar zuciya tayi dan ji take tamkar lokacin komai ya faru,sai a yanzu ne ta gano batai ma Zahra adalci ba.
Tabbas abinda take fuskanta yafi kama da sakayyar da ta sanarta tana nan zuwa gareta,domin tai auren kece rainin amma da ita da wanda ba miji kusan duk daya.

*"Bilal"*..
Sunanshi ta furta ido rufe.
A duniya tasan duk inda yake toh tabbas bashi da abar tsana sama da ita..
Da ta wuce,gashi yanzu ya kamata a hotel tare da mijin da ba nata ba,tabbas in duniya za ta yarda da ba abinda ta aikata yayin da suka ke6e da ita da Kabir tasan Bilal bazai aminta ba..domin maballin riga sukai ido hudu tana ballewa..

Gefe ta jiya tare da janyo filo ta matse tare da matso kwalla, in za ta hadiyi Al'Qur'ani gun rantsuwa tasan sai dai ta yaudari zuciyarta, domin har yau a ckinta babu na biyun Bilal,son duniya ne ya shafe hakan.

Feenat Ja'afar.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 03, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HANGEN DALA..Where stories live. Discover now