YARAN MIJINA

9.5K 293 11
                                    

❣️❣️❣️❣️YARAN MIJINA❣️❣️❣️❣️

written by zainab shuaibu
(ZABSHA)
dedicated to meemaluv

Based on truelife story

masu bada shawarwari ina mika godiyata gareku.
masu kira a waya da turo sakwanni na fatan Alheri kuma ina gode muku kuma inasonku sosai.

maman walid, mmn salim,da maman fauwaz naga sakon ku nagode da kulawarku.
ban manta dakeba maman ashraf Allah ya barmu tare nagode .
luv u ol.

page 52

madina jiri ya debeta ta tashi kenan jiri ya kwasheta ta fadi a kasa ta suma.
hafsat na ganin haka tayi tsaki tace ni dama zaki mutu shegiya.

hafsa na zaune ta hango babanta na tahowa ta window ai sai ta kwala kara wayyo Allah!
Ta fara jijjigata tana cewa
Anti madina!Anty madina!! Anti madi!!!

dan Allah ki tashi
aikuwa Alhaji jin ihun hafsa yasa ya shigo da gudu ba tare da sallamaba a rude yake magana lph hafsa bari na kira doctor ya juya da sauri ya nufi office din doctor.
yana shiga yafara magana a rude doctor matata ta suma
Dr najin haka da sauri ya tashi ya dauki kayan aune aune ya bi bayanshi suna shiga Alhaji ya dauketa ya dorata a saman gado doctor ya fara dubata ya gwada b.p dinta yaga yayi high nan da nan ya kira wata nurse ta mata allura sannan ya fara ma Alhaji bayani na cewa jinintane ya hau sosai kuma ba'a so mace tasamu matsalan eclampsia dan 50% sukan rasa ransu anfiso haka ta faru kafin haihuwa Amma karkadamu insha Allahu zata samu lph.

hafsa dai tabe baki kawai takeyi tama fatan ma da'ace ta mutu.
tajuya taga duk jikin madina ya kumbura kuma ga miyau na fitowa ta bakinta da karfi tace
daddy! daddy!!
kalli anti madina yace eh anmata allura insha Allahu zata samu sauki.
tace Allah ya yarda.

daga haka ya tashi yace bari yaje ya siyoma bbyn madara yaga yanata kuka.
tace toh sai kadawo.
yace ki kula dashi hafsat kafin na dawo tace toh.

yana fita ta ajiye yaron gefen mamanshi gashi yana kuka amma tayi tsaki.
karshe ma earpiece tasa a kunnenta ta kure wakan dan karma taji kukan yaron.

Allah sarki yaro yayi kuka daganan yayi bacci.
hafsa kuwa banda chatting da jin waka ba abinda takeyi .

Bayan 2 hours

sai ga Alhaji nan ya dawo
tace daddy kadawo yace eh "
"sannu dazuwa "tace dashi
yace "yauwa"
sannan ya samu wuri ya jawo kujera ya zauna.

yace hada mishi madara ga feeder nan tace toh
ranta besoba haka dai ta hada mishi ta mika mishi feeder yace haba hafsa ki bashi mana
ta karbi yaran ta bashi aikuwa ya fara zuka tas ya shanyeshi dan tunda aka haifeshi besha ko ruwa ba balle ruwan nono.
ya na gamasha zata kwantar dashi yace ki sa shi a kafada ki shafa bayanshi tukunna yayi gyatsa sai ki kwantar da shi tace toh.
haka ta sa shi a kafada tana shafa bayan shi har yayi gyatsa bata sauke shiba har sai da taga yayi bacci sannan ta kwantar dashi.

madina kuwa batasan me akeyiba dan in banda snooring ba abinda takeyi bata ma san wake kanta ba hafsa kuwa haushi ne ya isheta yasata ta maida earpiece a kunnenta.
suna zaune yan uwan madina sukazo suka ga bby sai dai maman baby bata hayyacinta haka dai zuka zauna sukayi jungum jungum sun dan jima kadan daganan sukace zasu tafi Su kama Alhaji Allah ya sawake sukace zasu bar kanwar madina ta zauna da ita.

washegari

madina har yanzu bata farfado ba Alhaji dai hankalinshi ya tashi gani yake kamar bazata rayuba .
kanwar madina na zaune hafsa ta shigo da flask ta ajiye tana zumbura baki.
tace mata hafsa ina kwana
hafsa ko kallon mutunci bata mata balle ta amsa gaisuwanta.
batace komai ba illa tace Allah ya shirya.

hafsa ta juyo ta murguda baki tace ya shiryemu gaba daya .
mtseeww tayi tsaki ta samu wuri ta zauna tana taunan cingam.
A na cikin haka madina ta fara tari dasauri kanwarta ta juyo tace sannun anti madina ta taimaka mata tadago tace bari nakira doctor da sauri taje takira doctor .
ya na zuwa ya dubata yace karta sha ruwa
tace dr wllhy kishi nakeji yace a'a bazaki sha ruwa ba tace toh .
kawai kwantawa tayi mintuna kadan bacci yayi awon gaba da ita...

bayan kwana biyu

Alhamdulillah yanxu jikin madina yayi sauki doctor yazo ya sallamesu tare da ja musu kunen kar tayi wanka da ruwan zafi sosai .
a haka suka amsa mishi ta toh suka kwashe kayansu suka sa a mota suka nufa gida.....



taku har kulllum

ZABSHA✍️

YARAN MIJINA COMPLETEWhere stories live. Discover now