*HUDAH Y'AR KARYA..* 21-30

1.7K 132 6
                                    

☁️☁️☁☁☁☁☁☁☁️☀
🐔 _*(HUDAH Y'AR KARYA....💁🏼)*_
         🐤🐤🐤🐤🐤🐤🐤
  🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🐛

_Written By *ASY KHALEEL...✍🏻*_

         Wattpad@asykhaleel
           Facebook Group
        Asy khaleel Novel's grp
             IG @asykhaleel


                  2️⃣1️⃣-3️⃣0️⃣

*HUDALLAH*

Yarinya ce wanda bazata wuce shekaru goma sha bakwai, tsayawa bayanin suffofin Hudah wannan zai zama cin lokaci, kai tsaye zamu iya cewa  Hudah masha Allah, ajawan halitta duk wani abu da akeso ga 'ya mace Hudah ta hadasu,  abu dayane ya hanamu karyata malam bahaushe dayace,
     (mutum tara yake bai cika goma ba)
    Wannan abu shiya  tauye Hudah harya hana asalin sahihin kyawun halittar ta ya bayyana wato quncin rayuwa, ma'ana rashin wadata,

    Hudallah yarinya ce ma'abociya kwarjini da farin jini duk wanda ya zauna da ita koda na yini gudane nan da nan yake jin tashiga ransa, tin tana karama ta kasance yarinya maison ado da kyalkyali, yar qarama da ita tasan tashafa wannan ta liqa wancan, abin nata har yakai ga Mamy bata da damar aje kayan kwalliya afili, in kuwa tayi koskuran ajewa yanzu Hudah zata mamayeta tai kaca kaca dasu, haushi yayi kamar ya kashe Mamy, tayi bugun harta gaji, Baba kam lallashin ta yake  da cewa tayi hakuri yarinya ne kuma daman su mata ai da ado aka sansu, don haka ya fara sayawa Hudah kayan kwalliyarta ita kadai tayi yanda takeso, atakaice dai Hudah tin tana karamar yarinyar da bata wuce wasan kasa ba, karyane kaganta ka raina mata, mace ko namiji kowa sonta ake don kuwa ko kaine
   ( hasidin iza hasada)
dole kaganta ka yaba koda kuwa a cikin zuciyar ka,
Wannan hali ko ince dabi'a nata yana matukar burge iyayenta sosai, dan Hudah sam bata shiga cikin kazaman yara sa'an ninta, sai ma kyamarsu da takeyi, abunda iyayenta basu gane ba shine, acan kasan zuciyar ta tana da wani ra'ayi ko kuma sha'awa, ita dai a rayuwa babu abinda yafi burgeta kamar rayuwan 'ya'yan masu kudi, dik inda zataga majiya dadi ita dai suna burgeta tanajin inama iyayenta masu kudine, hatta a makaranta in kinga Hudah tana haba haba da mutum tana yashe hakora to taga alamun sassauci ga yaro, misali tana ganinka a koda yaushe cikin tsafta kuma kana zuwa da kayan lashe lashe irin na yan gayu, lallai yanzu zaku kulla abota da Hudah,
   Abun nata yayi kamari a cikin zuciyar tane lokacin da Mamy ta kaita wajan Munirah, nan fa Hudah tafara karo da 'ya'yan masu kudi wa'inda iyayensu ke kawosu don agwada su, ta fata ganin fitattun yan mata masu ji da kansu, kasancewar Munirah gwanace acikin teloli kuma duk yawancin customers dinta masu kudine irinsu takema dinki, wannan dalili yasa Hudah ta zabi zaman plazan Munirah akan karatu, akwana atashi Hudah tana kara wayo tana qara sa buri aranta, har yakaiga ta fara tsarawa kanta irin rayuwan daza tayi da irin wa'inda suka canci tayi rayuwan dasu *wannan kenan.*

     Nidai nace..

Anya kuwa HUDALLAH?
Anya haqanki zai cumma ruwa?
Shin mutum ya isa yakai kansa inda Allah be nufeshi da zuwa ba??

To anan dai marubuciyar take tunatar daku  iyayen yara!!

   Musan cewa kananan yara wa'innan da kuke gani amanarsu Allah yabamu, kuma tabbas saiya tambayemu akan tarbiyan da mukai masu, don haka.
Ya zama dole musa ido sosai akansu dolene mu lura da yanda suke tafiyar da rayuwansu domin wani yaron, yana tasowa ne da halin sa mekyau ko akasin sa,
   Yake yar uwa kisa ido bisa tarbiyan 'ya'yanki, idan kika lura danki ko yarki nada wani hali wanda kin tabbata idan wannan hali yabishi har girma, lallai bazai kaishi gacin nasara ba, to anan abinda ya kamaceki shine,
Tin wuri ki dage da roqa masa Allah kada ki aje abun amatsayin yarinta, ki daure kina tashi tsakiyar dare kina kai kukan ki ga Allah kuma ki yawaita yin sadaqa da nufin Allah ya dubeki ya biya miki bukatarki ya canjawa danki wannan mugun hali, ya kuma shirya miki su bisa dai-dai din hanya, wallahi matukar kika rike wannan kika zamo uwa tagari mai yiwa 'ya'yanta wannan adduar insha Allah koda an hukunta  danki sai yayi takadaranci tofa abin zaizo dasauki sosai,  kai da yardan Allah bama zai gagareki ba yar uwa je ki gwada!.

  Sosai iyayen yara suna babban koskure bisa kola da tarbiyan 'ya'yansu, walh wata uwar batama kaunar ace ga laifin danta, gasunan acikin gari, kiga karamin yaro ya taso da muguwar bakar zuciya tamkar ya kashe kansa, tsakanin sa da yara yan uwansa kuwa sai zalumci,  yau ya cuci wannan gobe ya cuci wancan, amemakon ke uwa kinga haka, ki dage dayi masa nasiha da addua ba dare ba rana, kuma lokaci lokaci kina bada sadaqa ga manyan malamai don su tayaki addua,  a a sai kiji ana cewa yarinta ne kowa da irin nasa, wanima abunda yayi ai ba'a tona ba, gashi yanzu angirma an bari, dan haka shima bari zeyi, kai wata uwarma wlh kai tsaye zatace ai da'ace shi ake cuta gara shi yayi, iyaka dai in anzo in bada hakuri, amma miye amfanin raganci kullum yaro yazo maka da kuka, to bari kiji uwar san zuciya,
Irin sune da zarar yaro ya fara zama matashi saiya zama dan sara suka, gasunan muna gani acikin gari qananan yara yan  15 to16yrs sune suka addabi mutane da soke soke, sai alokacin ne hankalin iyaye ke tashi aita wani fade fade, basu gidan boka basu gidan malam, tana fadin a temaketa wane ya fara bin yan sara, Hmmm Hajiyata sai yanzu?
Sai yanzu bayan kin baro shiri tin rani?
Eh yanzu fa dole hankalinki ya tashi tinda kinsan danki bashi da garantin zega gobe, rayuwansa tana cikin hadari, kullum cikin dayan biyu yake, ya kashe ne ko kuma shi a kashe shi, to mudai.
Ya Allah ka shirya mana zuria ameen.

Ku dai bini sannu ahankali danjin cigaban lbr, luv u all my followers, voters n readers😍

*HUDAH 'YAR KARYA....*Where stories live. Discover now