CHAPTER ONE: HADUWAR AHMAD DA ALHAJI SAMBO

224 11 1
                                    

  Ahmad saurayi ne dan shekara ashirin da biyar ya kammala karatun sa a jami'ar bayero, yau shekara uku kenan babu aiki babu abinyi kullum cikin sa rai. Yayi nema har ya gaji addu'ar sa a koda yaushe Allah ya kawo masa canji dan a yanda yake ciki yanzu yasan yana cikin manya-manya guda biyar da talauci ke musu yanda yake so a cikin Unguwar su dake birnin kano.
  Wata rana ahmad ya fita yawon neman aiki tun safe yake yawo cikin gari har la'asar amma shiru, ba inda aka dace dan haka ya kamo hanyar sa ta zuwa gida,yana tafiya a gefen titi saboda ko kudin abin hawa bashi da shi.
  Kawai sai yaga wasu taron mutane a gaban sa har ya wuce kome yayi tunani kuma sai ya karasa wajen da isarsa wajen sai ya tarad da wasu mutane suna ta faman raba fada tsakanin wani tsoho mai keke da kuma wani direba da yake Jan wata jeep kirar kamfanin Mercedes.               Mutane sunyi iya kar kokarin su dan su raba su amma tsohon yace samsam shi bai yadda, ahmad yana fahimtar me ake ciki sai ya nufi wajan tsohon cikin hikima da dabara ya shawo kansa tsohon ya hakura ba karamin mamaki ahmad ya bawa mutane ba dan kafin ya zo babu yadda ba ai da tsohon ba akan ya hakura amma yaki. Dukkan abinda ya faru akan idon alhaji sambo ne wanda shine a cikin motar da direban da sukai fada da tsohon yake ja,dan haka da su kai gaba sai alhaji sambo ya bada umarnin a tsaya direba yayi fakin a bakin titi har ahmad ya karaso wajen direba ya leko ta taga ya kira shi yace masa yazo.
  Ahmad ya karasa wajen motar alhaji sambo yace ya shigo ciki ya shiga ba tare da fargaban komai ba,alhaji sambo ya kalleshi yace dan samari ya sunan ka ahmad yace masa sunana ahmad alhaji sambo ya cigabada da cewa ni Sunana alhaji sambo kuma ni dan kasuwa ne duk naga abinda ya faru tsakanin ka da wancan tsohon abin ya burgeni lalle kayi aiki da basira da hikima wanda hakan yasa naji na gamsu da kwakwalwarka dan haka yanzu ga wannan alhaji sambo ya bawa ahmad compliment card dinsa yace ya nemeshi ranar monday.
 

Chegaste ao fim dos capítulos publicados.

⏰ Última atualização: Jul 05, 2018 ⏰

Adiciona esta história à tua Biblioteca para receberes notificações de novos capítulos!

AMANAR SOOnde as histórias ganham vida. Descobre agora