page 13

5.1K 407 60
                                    

*M🅰K'OT🅰N JUN🅰*

*REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*  *P.M.L*

® REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS

ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# IG PML WRITERS
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-08144932303

         *Written by*

         💅💅💅    *SADNAF*💅💅💅

*Follow me on wattpad @ Sadnaf*

*ZUWAIRA MUHAMMAD WANAN SHAFIN NAKINE KE KAD'AI NA GODE DA KAUNARKI AGARENI MUCH LOVE DEAR*

*Page 13*

Aliya aranar tamkar mahaukaciya haka ta zama dan ko kuka ta k'asa yi ko yaya ta juya Sai ta ga yanda Adnan ke juye juyen rashin gaskiya ta kuma hango irin kallon so da sha'awa da Zara kebin Adnan da shi bata tab'a tunanin Adnan rashin tsoran Allahnsa ya kai haka ba  ya iya Neman matar mak'ocinsa wanan wane irin masifa ne tun yaushe suka fara soyayya ba tare da ta sani ba

babu shakka gidan da Zara taje Adnan yaje suka had'u har taji k'amshin turarenta a jikinsa da shattin Jan bakinta.

Aliya bata tab'a sanin Kuka rahama bane sai Aranar dan wani abune ya tsaya mata a kirji da mak'ogaro babu abinda take yi Sai juyi tana hasko yanda taga Adnan da Zara dazu.

Sai da ta Dade a matsanacin hali tare da tafasar zuciya kafin abin da ya tokareta a kirji yafara narkewa Hawaye suka hau zubo mata.

Aliya tayi kuka idonta har wani Zafi yake

Tana  tausayin kanta dan babu mummunan jarrabta daya wuce Allah ya jarrabceka da Mazinaci Wanda bai San hakkin mak'otaka ba bai dubi darajar mak'otaka ba babu tsoron Allah a ransa ya iya muamalla da matar Aure ina Adnan zai kai wanan zunubin ga k'eta had'in Aure ga na mak'otaka bata wani ga laifin Zara ba dan can asali bata da kamun kai babu abinda bazata iya aikatawa ba

Adnan fa yasan Zara tana da Aure matar mak'ocinsa  ce amma ya iya huld'a da ita wanan wane irin bala'i ne dame ta ragi Adnan  da zai ringa Neman mata banza awaje ciki kuwa har Da matar Aure dame Zara tafita tayi tunanin Duniya taga abinda take mishi da har  bata iya gamsar dashi amma Ina bata gano abinda take mishi ba.

Aliya tayi kuka kamar hawayenta zasu k'afe Wanda sabida kuka da tunani kanta ya ringa wani irin ciwo ko sallah ta kasayi sabida tashin hankali da rashin  nutsuwa.

Adnan kuwa bai waiwayi d'akin Aliya ba duk da yana jiyo sheshek'ar kukanta tab'e baki yayi yace ita tasani yana zaune zata kawo kanta amma idan shi take jira ya bita d'akinta ya bata hakuri zata shekara duk da yana tsananin bukatar ta abincin da ta dafa ya take a cikinsa yayi gyatsa ya koma d'akinsa yayi wanka ya shirya ya k'ara ficewa daga gidan dan yana bala'in bukatar mace zai fita ya zab'a a cikin 'yan good evening masu tsayawa a bakin titi suna jiran masu tayasu at least ya rage zafi kafin ya samu Zahra.

Zarah  kuwa juye juye kawai take tana Allah Allah gari ya waye Ameer ya fice daga gidan Adnan yazo dan tana San kasancewa tare dashi ta kurmance akan Adnan ta makance bata sha'awar zama da Ameer ko k'adan bata da burin da ya wuce ya saketa ta Auri Adnan.

Washegari da sassafe Ameer ya shirya ya bar gidan dan baya San abinda zai ringa had'ashi da Zara ko kad'an  dan tsanarta link'uwa yake aransa a duk lokacin da ya tuna irin rashin Kunyar da tayiwa Mommy Hauwa.

Zara tana jin Fitarsa taji kamar ta buga tsalle ta taka rawa dan mafarkai kawai take da Adnan abun shaidan wani mugun sha'awarsa takeji  Yanda take ji indai ta samu Adnan ya shigo gaskiya sai ya kashe mata k'ishin dake damunta.

Mak'otan junaWhere stories live. Discover now