1-10

12.1K 466 10
                                    

Dariya take tana qarawa, duk wata damuwa tata takau,nishadi takeji kasancewarta tare da farin cikin xuciyarta, bata da wata damuwa a ynxu tunda gata tare da masoyinta

shima qasa qasa yake kallonta idanunsa cike da xallar soyayyarta bashida sauran damuwa tunda ya sami farin cikin sahibarsa, damuwarta damuwarsace farin cikinta nasa ne, bashi da buri da yawuce ganin ya mallaketa a matsayin matarsa kuma uwar ya'yansa.........xainab ta katse masu jin dadinsu tana fadin

uwayen soyayya anan xaku qare rayuwarku, suka juya a raunane suna kallonta fuskarsu ba walwala alamar basu so xuwanta a wannan lokacin ba.

kutashi an shiga philosophy kuma kunsan wicked lecturer ne....

Fari'ah  ta yatsina fuskarta hade da tunxuro bakinta tana kallonsa

tace ni xamana da farincikina yafiye min komai akan wata lecture yanxu.....

xainab ta saki bakinta da mamaki tana.kallonta
tace amma ke meyasa bakya tunani da hankalinki meyasa xaki xabi soyayya akan karatunki?

saboda soyayya itace jigon rayuwa, Jiyad ya bata amsa a fakaice, hakan ya faranta fari'ah sai ta saki.murmushi tana kallonsa

xainab batare da tayi mgn ba ta juya ta fice...jiyad yace ki daukar mata attendance pls,

ta juyo a raunane ta watsa masa wani kallo mai cike da takaici taja dogon tsaki tafice......suka tabe baki hade da kallon juna suna murmushi.
[9:10PM, 4/5/2016] pherty: *
Da sassarfa ta shigo gidan lokacin ummanta na saukowa kan steps ta cillar da handbag dinta da handout hade da dafe goshinta

oh umma kinsan yau na wahala, lectures din yau da xafi suke wlhy....

umma ta xauna tana fadin Allah yasa da gske dinne kinyi lectures din yau baki tsaya tare da wannan yaron ba...

ta yatsina fuskarta hade da xaunawa kusa da umman, ta langabe kanta tana kallonta cikin wani yanayi

tace umma ina son jiyad, ina sonsa sosai umma fiye da xatonki, ki taimaka kima baffa mgn ya amince dashi yace xai aura min shi pls ummana....sai ga hawaye shar nabin kumatunta

ta janye hannuwanta cike da takaicinta
tace ina gargadinki ina kuma qara gargadinki kimanta wannan yaron ki fuskanci karatunki, baffanki baxai yarda ya aura miki yaron da bayada aikinyi ba yana karatu hassalima course mate dinki ne...ta katseta

ta katseta....but umma  yana da kudi, his father is rich kamar baffa, yana da kyau da qatuwar mota, umma motarsa ma tafi tawa, and he told me yana da qaton gida da abbansa ya gina masa kuma....ta katseta cikin tsawa

shut up....hakan ya firgitata sai ta fashe da wani irin kuka,ta tashi batare da taji me umman xata ce ba ta haura sama tana kuka, kallo kawai tabita dashi cike da takaici....

MATAR WAYE?Where stories live. Discover now