page 3

9.4K 507 9
                                    

*Haske writer's Association* (home of expert and perfect writer's)

*SIRRIN MIJINA*

*Billy Galadanchi*

  Sadaukarwa ga qawata
*Nafeesatu sani kibiya....(Pheey)*

                03
Zaneerah ke gayawa maman su zancen Dr. Hisham akan Aunty qwasai

"Mama sefa kin wa Dr. Magana sabida shi sam yakasa fahimtar wacece qwasai, sabida tsabaragen surutunta da kuma wayon tsiya ake kiranta da Aunty K'wasai karki dauka wai sharrin mutanene bako d'aya wlhy kurin dai tun tana qarama ko a gidansu haka ake cemata sabida uban surutu" kallonta mama tayi tace

"ke yanzu dan Allah zanneerah bakya majin kunyar zagin zuhrah ina qanwa jalal kike nufi? Yarinyar nan banda surutu banji kince tana bin maza ba,ko tanada qarya,kokuma acan school d'in dakike vice principal kin taba ji ance anzo tukarta tayi gulmar wani? Ki sani a irin haqqi ke dawo muku gashi nan kina zaune gida shekaru ashirin da tara ba mijin aure,kin kasa gane cewan irin hakan ce take korar miki mazan ire iren ku wanda basa shaidar alkhairi akan kawai surutu se a fasa auren mutum halittace ta Allah haka yayita  kuma bazan hanashi aurenta ba dan kawai tanada surutu" shiru tayi ta kame bakin ta sabida bawai da wata manufa tayi maganr ba taga yanda kowa kr zancen mugun aurutunta ne komai akayi agidansu yana makaranta se kowa yaji sedai kuwa idan anyishine batare da sanin taba batada rufin asiri ko kadan tana jiyewa yayan nata illar tonon asiri kar wata rana ya dawo musu dukkansu ta kula mama bata fahimcetaba gwara tayi shiru abinta tamasa fatan alkhairi.....

    Washe gari koda sukaje school Zuhrah seda ta gayawa kowa tayi sabon saurayi ajin farko, koda aka tashi break tasoma jin zazzab'i kasancewarta me yawan samun zazzabin lokaci zuwa lokaci tasani kuma bawai sauka ze mata da wuri ba, takanyi sati idan ya kamata gashi sam batasan allura, dauriya taci gaba dayi sabida tasan halin nurse din dake kula da marasa lapia a school din tsaf zece ze gantsara mata allura ita kuwa abinda bazata taba yadda dashi bane amata allura ciwo kan ciwo a hallakata a banza a wofi.....Saratu zubairu ce taga yanayinta tace

"Zuhrah ina bakin? Najiki shiru tun dazu gashi banj8 kina challenging maths teacher ba yau har ya fita" dago idanta tai tana kallon saratu har sunyi ja sabida azabar ciwon da kanta yake mata tace daqyar

"Zazzab'ine ya tasomun kaman daga sama,kuma kinsan dai bazanje amun allura ba dan Allah karma ki gayawa wani tunda an kusa tashi idan munje gida zansha magani"

"Amma dai bawai kina nufin ko magani bazakije ki karb'a ba yanzu fa after 11, muda gida kuma se 4 ina zaki iya zama da zazzabi haka? Kalli idanki" shiru tayi tana kallon saratu batama so tana yawan magana yau sabida kanta sara mata yake sosai, ganin bazata tashiba ya sanya saratu zubairu zuwa ta gayawa Nurse d'n har class din yazo ya duba ta sannan yace su riqo masa ita, tun anan tasoma kuka tana surutun data iya

"Dan Allah sir karkace zakamun allura wlhy zan iya macewa ma gaba daya, banasan alluran dan Allah kamun rai" be kulataba danshi yayi gaba, se turjiya take musu gashi ba qarfi ajikinta har jiri take gani dama sam zuhra bata iya zazzab'i ba har sambatu takeyi....a can clinic d'in kuwa koda sukaje Dr. Hisham yazo duba magunguna, ita sabida azaba ma bata ganeshiba shine yayi saurin ganeta kai tsaye tun a muryanta ma, miqewa yayi tamkar wanda aka tsikara yace yana kallon nurse din daya shigo kafin su

"Yadai Meya sami zuhra?"

"yarinyar nan sir bakaji yanda take bani haushi ba wlhy, ban taba ganin mutum me surutu da kafiyar tsiya ba irinta,zazzabi takeyi shine tamkar lapian ta ajikin wani yake taqi zuwa a dubata, kuma naje na duba dole se an mata allura jikinta tamkar gaushin wuta amma sam wai bazatazo amata ba, shine kaga jiri na iban ta amma tana turjewa sabida tsabaragen iya shege da raina mutane, wannan zuqeqiyar zatace tana tsoron Allurah" kallonshi Hisham yake cikeda takaici koshi ya kula da hakan, yanaso ya rainawa Kwasai hankali banda haka yaya zema kalleshi yace yanaji haushin zuhra

SIRRIN MIJINAWhere stories live. Discover now