11

2.4K 126 0
                                    

🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾

*ME KE FARUWA?*

🎗⚾🎗⚾🎗⚾🎗⚾

*A TRUE LIFE EVENT*

        *WRITTEN*

              *BY*

_*BILKISU Z. YAU (🅱K )*_
_( Autar Marubuta )_

               &

_*AISHA ISA*_
_( Mummy's Friend )_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
_(Gidan zaman lafiya da amana., In Shaa Allah)🤜🤛_

*SADAUKARWA GA:*

*MAMAN SALEEM*
_( Aunty lipson )_

            &

*UMMU AKRAM*
_( Aunty Aisha )_


_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

_Manzon Allah S.A. W yace : K'ololuwan azaba yatabbata ga wasu gurab'e a wuya._

*BABI NA GOMA SHA 'DAYA* 

      Murmushi Amira tayi tace " Maryam Allah ya kaimu ya bada zaman lafiya.

"Ameen Amira nagode, Allah kema baki miji nagari.....I can't wait to see that day wallahi".

Murmushi Amira tayi ta gyara kwanciyar tana mai juyawa Maryam baya sannan ta lumshe ido. Juyo da ita Maryam tayi tace " dalla malama kin wani juyo baya maimaikon ki amsa addu'ata".

"Auchh!,  zaki k'arasani ki barni da jinya ke kuma kina can  kunshan soyayya.... " duka Maryam  ta kaiwa Amira cikin wasa tace " wallahi Amira baki da dama Allah ya shiryeki".

"Ameen amma ai gaskiya na fad'a".

"Kya ji dashi" Maryam tace sannan tashi tare da ajiye bakar ledar da ta shigo dashi tace " Amira ni na tafi,  ga leda ki duba anko ke ciki kuma dole ki siya ehee".

Ledar Amira ta jawo ta ciro atamfar,  "wow! Wallahi tayi kyau amma nidai....."

"Kedai me?" Maryam ta katse mata hanzari, taka kara da fad'in " karma kice min bazaki siya,  wallahi sai kin siya koda 4 yards ne, ni kin ga tafiyata" sannan ta juya ta nufa hanyar fita.

Da sauri Amira ta sauka daga kan bunk din tace ganin har ta kai bakin kofar ko " toh ai sai ki tsaya na raki ko.." ta k'araso gunta tayi mata rakiya har hostel nasu da yake ba hostel d'aya suke da Maryam.
Kan gabo ta fada bayan dawowarta  daga rakiyan Maryam ta fara tunani yanda abubuwa suke tafiya mata "oh ya ilahi wai *meke faruwa*?, sai yaushe zanyi aure kamar sauran k'awaye na, ya zanyi indan hasashena yazama gaskiya kasim dinna ne?,  Ya ka jibanci lamarina, ka bani ikon danne zuciyata.... " duk wannan maganar a zuciya Amira ke yinta yamin da hawaye ke bin gefen fuskanta. Knocking din aka a kofar dakin su ne ya fargar da ita daga duniyar da ta lula, hawaye ta goge da sauri ta daidai natsuwarta kannan tace " come in the door open".

Kofar aka bude tare da sallama Firdausi ce ta shigo rike da littafai a hannunta da alamar daga lectures take.  Amsa mata Amira tayi sanyi murya.  Yanayin da Firdausi taji murya ta yasa tace "lafiya naji muryanki haka?, kodai har lokaci yakai...?"

"Lafiya kalau"Amira ta fad'a koda yake tana jin alamar zuwan nasa amma bata son ta daurawa kowa laluranta.

"Kin tabbatar,karfa kizo ki hana mu barci anjima,  don Allah idan kisan shi ne".

Murmushi Amira tayi tace " karki damu In Shaa Allah bazan hanaku barci ba".

Baki Firdausi ta tab'e tace " ke kika sani wallahi ko kin tasheni bazan tashi sabida yau a gajiye nake ehee.  Mutum yasan laluransa amma sabida rashin son magani sai yaki fad'a, am off to bed kuma karki tadani " sannan ta bi lafiyan gado.

MEKE FARUWAWhere stories live. Discover now