PART 25-26

3.1K 90 3
                                    

*_RASHIN ASALI_*

      🕊🕊🕊🕊

*_WRITTEN~BY✍🏻_*
*_ANTY MAIMOUNATH O.G_*

       _Wattpad@maimounathog_

*_SADAUKARWA GA👇_*
*_MAHAIFIYA TA😘_*

*🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟*
                    *G.W.F*

*~Home of gorgeous, intelligent and experts writers, we are d best among d rest~*

Https://www.facebook.com

*~_________________________~*
_RABBI HABLI MILLADUNKA ZURIYYATAN 'DAYYIBA🤲_

*~_________________________~*

*Asha rawa rawa mata asha rawa💃💃Kusha sha'aninku duniya ce sama mata ahaa💃💃💃*

*'Yan gorgeous writers forum wannan shafin naku ne, kuna wuta ina binku da petur, Allah ya k'ara muku basira da hazak'a, hak'ik'a kuna matuk'ar birgeni😍Ina alfahari daku, Allah k'ara had'a kawunan mu🤝kuma kusha sha'aninku duniya ce😆inji ni antyn ku O.G😅*

*_LITATTAFAI NA MASU FITOWA👇_*

*_'YAR GADARA CE_*
*_BAZAN AURE SHI BA_*
*_ZAMBA CIKIN AMINCI_*

        *25-26*

*_BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHIM_*

Juyowa tayi ta kalleshi jin abinda ya fad'a, cewa dan Allah ta taimaka mishi UMMI ta tare cikin satin gaba,

'' Oh ni shikenan yanzu ka zama marar kunya ko?, to tashi ka bani wuri ba yanzu ba dan ban shirya baka 'yata ba'',

Kai ya sunkuyar yana murmushi yace'' Ayi hak'uri dai mama'',

'' Naji tashi ka tafi kazo ka hanani hira da 'yata'', kallon inda UMMI take yayi yaga suna d'an wasa da little yarinyar ta saba da ita dan wani lokacin ma idan ta mak'ale mata bata yadda kowa ya amshe ta, tun ma kafin ita UMMI ta zama matar daddyn ta, shak'uwa ce a tsakanin su,

Bai yi magana ba ya tashi zai d'auki little amma k'ememe tak'i zuwa wajensa ta shige jikin UMMI kamar mai shirin shan nono,

Mama tayi murmushin jin dad'i tace'' Au yau daddyn naki ma bazakije wajensa ba?,

'' Ah to kin gani dai sai in tafiyata in barta ai, kuma inada chocolat bazan bata ba'', jin zancen chocolat yasa taje wajensa tana gwaranci dan bâ kowace maganar ta ba akeji,

Sai da safe yayi musu ya fice, mama ta kalli UMMI tace'' 'yata kin tabbata baiyi miki komai ba d'azu?",

'' A,a fa mama wlhy bai min komai ba sai dai....'', bata k'arasa maganar ba ta kyale,

'' Sai dai me, uhmm?, mama ta tambaya, kallon mama tayi ta shagwab'e fuska tace'' dan Allah mama karki dakeni idan na fad'a miki abinda yayi min'',

Kai UMMI ba dai yarinta ba inji mama a cikin ranta amma a zahiri tace'' fad'a min bazan dake ki ba'',

'' Uhm..uhmm daman fa yayane mukaje wani gida, da muka shiga ciki shine fa sai ya kwantar dani...uhm sai...sai yayi ta wasa da nono na kuma har da bakinshi ya had'a da nawa yace wai lada zan samu'',

Dariya fal cike a cikin mama amma sai ta gumtse ta d'an had'e fuska tace'' iyyyeee abinda kukeyi kenan UMMI?, daga nan kuma sai me ya faru?",

'' Dan Allah mama kiyi hak'uri shikenan bai min komai ba, karki fad'a mishi ya dakeni'',

'' Naji amma kar inji wannan maganar a wajen wani ko su Ramlat kar inji kin fad'a musu kina jina ko?",

'' To..to mama Allah d'aya bazan fad'a ba'', nan mama ta sallameta ta tashi ta fice, bin bayanta tayi da kallo tace'' oh zai lalata min tsari ji yanda yasa yarinyar nan tayi baki yau d'aya, UMMI da bata da hayaniya da surutu, hmm Allah ya kyauta dole ne in kira mai hajiya  Laura mai gyaran amare ta gyara min ita tun kafin yaron nan ya kaini ya baro

RASHIN ASALIWhere stories live. Discover now