Shafi na uku

2.4K 197 16
                                    

*KUNDIN HASKE*

*AL-K'ALUMAN MARUBUTA...*

✍🏻

*_NA KUNGIYAR:-_*
     _HASKE WRITERS ASSO...._

TAREDA AL-K'ALAMIN...
       *_Nana Hafsat_* _(MISS XOXO)_

*_🙆🏻‍♀NI NA JAWA KAINA!!😭_*
(SHAYE SHAYEN MAGANIN MATA)

*BABI NA BIYAR.*

     *SHAFI NA UKU*

   *A*ngo yacigaba dashan amarci da amaryarsa, yayinda Maman Zara'u aketa k'ara d'irkar kayan mata.Kwanaki bakwai nacika kuwa ranar data kasance zai dawo d'akin Maman Zara'u kenan.

Aranardai kam ba'a cewa komai, Dan bak'aramin shiri Maman Zara'u tayima kantaba, dai-dai da kayan matsi tamatsa yafi kala biyar, banda wad'anda taitayi acikin kwanaki 9 dasuka shige,nasha kuwa aii ba'a cewa komai, ita kanta harta k'osa yadawo d'akinta, Dan bak'aramin matsuwa tayiba.

Babban kuskurenta kuwa shine duk wannan shirin datakeyi na tarbar maigida babu muhimmin gyaran jiki datayi, irinsu kitso, k'unshi, yankan farce, dadai sauransu, sannan tsaftar d'akintama yanada rauni sosai, hakama 6angaren girki saidai ahankali kawai, dukda haryanzu ba muji  na amaryaba, tunda bata faraba.

Dawuri ta lalla6a Zara'u tayi barci kuwa, dantace yaud'in ranace tadaban.Baban Zara'u dai aka shigo ana 'Yar kunya irin wadda maza sukanyi bayan sunsha amarci sun dawo d'akin uwargida.

   Takuwa rungume kayanta, dukda ko kwalliya batayiba,hasalima tun wankan rana datayi bata sake waniba, duk da shige da ficen dataitayi yayin d'ora girki, amma bataji kunyar zama hakaba har mijin yashigo, hasalima ita hakan awajenta bawani kuskure baneba.To shima yarigada yasaba daganinta hakan, shiyyasa kokad'an baiwani damu kansaba, shidai yacire nasa kayan yace tazuba masa ruwan wanka.

   Kamar tayi kuka hakataji, Dan bawani son aikine da itaba, haka tatashi tana zun6ure-zun6ure tahad'a ruwan, sannan tasanar masa.Tashi yayi yaje yayo wankan yadawo, ta ajiye masa abinci,

“Uhmm Nafisa! Inaga ki aika Zara'u takira Hafsat muci abinci,Dan tare zamu ringaci.Inama Zara'u tunda nashigo bangantaba?”

“Zara'u tafayi barci tuni.Abincin kuma bazamu iyaci mu biyuba sai'an kirata kuma? Itama lokacin dakana d'akinta naga ba kirana kukeyiba?”

“Hakane, amma kiyi hak'uri, wancan kwanakin anmata uzurine amatsayin bak'uwa, kinga daga yau kuma ai sai mu fara, inason takuma sanin matsayinki na babba agareta, shiyyasa nabari sai ranar girkinki ko?”

  Kanta tad'an jinjina, dantaji dad'in hakan, mijinta nasonta, tace,

“To bara nakirata”

“A'a yizamanki, bara na kirata kawai awaya..”

Babu dad'ewa kuwa saiga Hafsat, saida tayi sallama, aka bata izinin shigowa sannan tashigo.

Daga mijin nasu har Maman Zara'u saida suka bita da kallo, Dan cikin kwalliya take zani da riga na atamfa, batawani yi kwalliya mai yawaba, amma sai bulbula k'amshi takeyi na khumrah da turaren fesawa me sanyin kamshi..

Baban Zara'u yalumshe idanu,yayinda k'amshin turarenta yanemi narkar dashi.

Cikin ladabi Hafsat tagaishesu, sannan tace,

“Gani..."”

“uhm dama abinci zamuci,daga yau kuma tare zamu dinga ci gaba d'aya”

Hafsat ta jinjinakai tana fad'in,
  '”to”

Maman Zara'u kam tayi tsit,Dan dukta gama raina kanta, yanda taga Hafsat cikin kwalliya.Sunacin abinci amma hankalin mijinsu nakan Hafsat, sai satar kallonta yakeyi k'asa-k'asa, Maman Zara'u talura dashi,ita kanta Hafsat talura dashi tsaf.

KUNDIN HASKE💡Where stories live. Discover now