Kafin in zama lawyer 25 to 30

197 11 0
                                    

👨🏻‍🎓KAFIN IN ZAMA LAWYER👨🏻‍🎓                                           👨🏻‍🎓       👨🏻‍🎓👨🏻‍🎓👨🏻‍🎓👨🏻‍🎓👨🏻‍🎓     

 
              Nah
   Marubuciyar Zamani

NABILA RABI'U ZANGO
      (Nabeelert Lady)

  @House of Novella Association
        (H,O,N,A)

www.NabilaLady5@gmail.com

        Season 25 🖤 30

Numfasawa Abdul yayi yace babu wani abu da zakayi da yawuce ka kara kwantar da kai, kada kabari su fahimci kanaso kasan abinda suke ciki, aduk lokacin da kaga zasuyi wata magana idan kana gurin kayi kokarin barin wajen.

Amma karika bibiyarsu aboye hakan zesa ka kara fahimtar yanayin aikinka, kuma kasamu duk wani abinda kakeso. Amma tabbas Sageer har cikin zuciyata naji inaso atemaki wannan bawan Allah.

Kuma na tabbata sune zasuyi nasara domin babban lawyer ne kuma wanda yasan makamin aiki, kayi kokari kasamu wani abu, bance kabada sheda ba, amma ina me tabbatar maka idan kasamu wani abu daga shari'ar nan tozatayi maka ammafi wata rana.

A jiyar zuciya Sageer yayi yace shikenan abokina nagode, a kullum bana damuwa da duk wani abu daze shigemun duhu saboda nasan ina da kai, hakika zurfin ilimi bashine nasara ba.

Mutum yakasance me zurfin tunanin shine nasara arayuwa, Abdul kai jigone arayuwata Allah yabarmu tare kuma yayi maka sakayya da gidan aljanna. Abdul yace amin abokina, tashi muyi sallah muci abinci.

Rayyana tana zaune bayan tagama sallah wayarta tafara kara, saurin tashi tayi, ta dauka saurayinta ne, sede kuma sabuwar number ta gani, dauka tayi tare da sallama.

Murmushi Anwar yayi yace kai kanwata ko kina tsoron asaceki ne? Dariya Rayyana tayi domin tagane me magana, gaishe shi tayi yace lafiya lau ya kuka isa gida? Tace lafiya lau, su Umma suna maka godiya.

Yace haba ai bakomai, ina Yayarki? Rayyana tayi murmushi tace wlh tunda muka dawo tashige daki wai kanta yana ciwo, da alama akwai abinda yabata mata rai adakin Laila.

Domin tun bayan fitowarta daga dakin naga ranta yabaci, bayan kuma ba haka muka shigo ba, kuma nasan halin Yaya Nabila bakomai bane yake bata mata rai ba.

Gaba daya jiyayi beji dadi ba, shiru yayi can yace Allah sarki, kinga na manta ban anshi number dinta ba, kituromun in dubata, Rayyana tace toyanzu zanturo maka, godiya yayi mata yakashe wayar.

Jingina yayi da kujerarshi ya lumshe idonshi, babu abinda yakeson kara kallo kamar fuskarta, hakika betaba tsintar kanshi cikin soyayya ba amma ayau kadai ya fahimci yafada tarkonta.

Wayarshi tayi kara alamun kira, saurin dauka yayi ganin kanwarshi ce take kira, bayan sun gaisa ya tambayeta ya karatu? Tace yaya lafiya lau ai munkusa gamawa saura 1 month.

Yace lallai ashe muna da babban party. Dariya tayi tace Yaya dama Faisal ne yake so iyayenshi su zo. Ganin nakusa gama karatuna shine nace yabari nafada maka seka fadama Abba.

Dariya yayi yace lallai yarinyar nan, wato kin gama rayuwarki amakaranta, yanzu zaki gama amma bazaki bari kizauna damu ba harzaki fara maganar aure ko? Turo baki tayi tace kai Yaya!

Kafiso nima Abba yafaramun magana kamar yanda yake maka? Kuma fa bada nagama za'ayi auren ba, bayanma ko rana ba'a saba. Anwar yace naji kuma zan fada ma Abba bama seya dawo ba tunda de kanwar tawa tagirma.

Nadauka ma zaki jira Laila ai? Dariya tayi tace Yaya kasanfa bata gama karatun taba, yace hakane, Allah yasa alkhairi tace amin. Can tace yauwa Yaya dazu munyi waya da Umma take fada mun wai Aunty tazaba maka mata ko?

Kafin in zama lawyerWhere stories live. Discover now