chapter two

19 3 1
                                    

Asubar fari, momma ta zo dakin zahra domin yin shirin sallah. But already zahra ta riga ta farka ta na ta yan nafilfilunta da addu o I, sbd yarinya ce mai kula da addinin ta sosai bbu wasa.

Aw ashe kin farka, momma ta tambaya tare da zama gefen gado. Eh momma na tashi tun dazu ma sbd yau na kwanta da wuri ne dan jiya ko se da safe ban ce miki ba.ki min afwa momma.

Babu komi baby ta, amma kar fa ki Kara tafiya barci ba mu yi sallama ba. Insha Allah momma.
Toh madallah se mun hadu da safe .momma ta fada tara da nufar kofar dakin.

Bayan ta idar da sallarta ne ta kunna heater ta bandakinta kana ta dakko wata cream handbag ta shirya hands out dinta na makaranta sbd bata so ta makara zuwa lectures tunda yau ya kasance ta safe Gareta. Bayan ta gama ne ta ta shiga wanka ta fito ta shirya zuwaga wata black and yellow abaya ta sanya tare da rolling Black Veil. Ba ta yi wata kwaliya ba se DE powder da kwalli da take saka wa. Kasancewar ta ita ba ta yin irin heavy make up din nan idan zata fita ko da kuwa biki za ta je,ba wai kuma rashin iyawa Ko rashin wayewa ba ce. Ita a ganinta wayewar kenan ,I. e being simple and natural.

Ta rufe dakinta tare da dauko mukulin red benz dinta ta nufi family dining kamar yadda ta Saba inda tarar da kowa a dining table. Ina kwana daddy ta fada tana risinawa .morning my dear, kin tashi lfy. Lafiya lau daddy,ta amsa tare da matsawa kusa da mommanta.ina kwana momma, ina kwana baby. Ina kwana mama ta gaida maman deeni.lfy lau yar gidan momma ta amsa a ciki Ciki.Morning  aunt pretty, cousin din dinee mai kimanin shekaru goma ta gaida Zahra.morning princess Zahra tayi replying back tare da zama kusa da ita.plantain ne da chips tare da kwai sukayi serving junansu.
Aunt pretty baki sa min ketchup ba, ayush ta fada tare da tabe Baki.oh sorry princess, barin in sa miki da yawa ma. In ji zahra, Sun kusa kamalla breakfast din kenan se ga deeni sanye da wani black jeans da milk shirt se brown blazer da ya dora. Kana ganin kayan kasan masu tsada ne Sosai.

So what's for breakfast, ya fada tare da jan kujerar da take opposite momma .zahradeen baka iya gaisuwa ba ne, daddy ya tambaya cikin takaici.
Aw ina kwanan ku fa.shiru ne ya biyu bayan gaisuwar.
Mtsww, ya ja tsaki,so what's the use of greating bayan bbu mai amsawa, Dad I hope Kana gani.

Daddy kawai tashi yayi daga tebur din tare da daukar brief case Dinshi.ni Zan wuce textile industry na. zahra ma ta mike,nima Zan wuce school, ta fada tare da zuwa gefan daddy sukai pecking Juna.so also zan wuce asibiti, momma ta fada tare da daukar lab coat dinta .ta yi pecking diyarta da mijinta. Ayush ma ta tashi ta ce mama ina lunch box dina yau momma ta ce she will drop me off school.

To shikenan,mama ta fada tare da mikewa. Uwargida na wuce, kaikuma deeni meet me there OK. Daddy ya fada ya nufi wurin motar shi.

See you princess zahra ta fada yayin da ta tsuguna tai pecking dinta.see you aunt ayush ta yi replying tare da pecking back.

Munafukan banza,uwargida ta fada yayinda ta kara hankara abinci a kwananta ta soma Ci.
Mama wlh kiba kike ta yi, yakamata ki fara dieting wlh. Deeni ya fada ya na yatsine fuska.
To zaka zauna ne ka ci abincin kokuma kaima se ka kara guma min bakin Ciki.
A a ni de gsky na koshi mama. Ba ki san yan mata su soni NE, ai idan nai kiba ko tumbi ba za su soni ba, yan mata Sun fi son namiji body builder. Ya fada tare da nuna dantsen hanunsa.
Dalla rufe min baki ka fita ka bani wuri.shashan yaro kawai.
To mama Allah baki Hakuri,kawai de ina gayamiki ne ki zama yar gayu kar ki koya ma ayush irin wannan cin .ba kiga yadda zahra da Doc suke ba, yan caras da su mama. Bugu da kari ke ba fita kike ba kinga.

Ita de maman dinee kawai cin abunta ta ke ta barshi yana ta surutun banza. Zaka zo ka tafi wurin ubanka ko yaya. Ta fada tare da mikewa daga kujera.
Ai dole ma kuwa mama. Daman ina bukatar kudi wlh, ya fada tare da ficewa daga dining room din. Yayin da uwarsa ta shiga kiran yan aiki su zo su gyara wurin sannan ta shige dakinta ta jabe.

Momma kuwa tun da ta ajiye ayush ;wato cousin din dinee ta bangaren uba.ta kama hanya zuwa asibinta mai suna  Z. Y health care center. Asibitin ya na da dan girma amma ba sosai ba, duk da asibitin bai hana shi zama popular a garin yola ba. Ya kasance daya daga cikin asibitocin da suke bada himma da kulawa dan ganin samun lafiyar mutum. Sannan ga sponsoring marasa karfi da sukeyi wajen raba kyautar magungunguna .Babu shakka zahra ta yi halin Doc. Zuhair wurin tausaya mutane domin itama haka take da dan san temakawa mutane.

In Quest Of Peace Where stories live. Discover now