👭AMINIYA KO KISHIYA👭

804 31 1
                                    

https://m.facebook.com/Brilliant-writers-216569899280295/?refid=52&ref=opera_speed_dial_freefb&__tn__=H-R

*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom, home of exceptional and magnificient writers_ }


👭 *AMINIYA* *KO* *KISHIYA* 👭


⏩5⃣


WRITTEN
           AND
             STORY

*FAUZIYYA TASI'U* *UMAR*
® *FAUZAH*

*TRUE LIFE STORY*

*SHORT STORY*


Yini tayi ranar bata da walwala saboda kalamansa sunyi mugun bata mata rai bata fatan ranar da wani namiji zai tunkareta da mgnr soyayya sai qarfe biyu ta gama lecture nata ta fita abin mamakin tana fitowa daga faculty din nasu taga motarsa sosai gabanta ya fadi ganinshi tsaye jikin motar ya zuba mata sihirtattun idanunsa yanayi mata wani irin kallo data kasa gane manufarsa.

Jiki a sanyaye ta qarasa inda yake tayi qasa da kanta sabanin dazun yanzu yadine a jikinsa milk da hula baqa da bakin takalmi sau ciki, kamar yasan abinda take tunani yace “kinyi mamaki ko Fauzah?”

Jinjina kanta tayi alamar eh murmushi yayi hadi da ajiyar zuciya lkc daya ya danna remote din motar qofofin suka bude yace “bismillah shiga mu tafi” kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ta zagaya ta shiga motar ciki babu qarfi.

Kamar dazun yanzun ma zaman kurame sukayi saida sukayi tafiya me tsayi sannan ya shiga Shop Rite yayi parking dagowa tayi idonta ya fada cikin nasa cikin 5 second ya tura mata saqon daya sanyata kasala da wata muguwar mutuwar jiki wanda hakan ya sanya shi farin ciki murmushi yayi mata ya bude motar ya fita.

Tunda yafita ta kifa kanta a saman cinyoyinta tana karanta wasiqar jaki babban abinda yafi tsaya mata a rai shine maganganunsa na dazu tabbas ya kamata ta dauki matakin qaurace masa saboda koma menene yana da masaniya akan maganganunsa na dazu babban tashin hankalinta kar ya kasance shine mutumin da yake mgn akan yana sonta tsayin shekaru biyar da kanta tabawa kanta amsa da hakanma bazai faru ba duk rashin kunyarsa ai baya ce yana sonta ba bayan yasan matarsa aminiyarta ce wadda sukejin junan kamar yan uwa.

Yadan dauki lkc kafin ya dawo ya bude but akasa masa kayan ya dawo ya zauna tare da ce mata “na bata miki lkc ko kiyi hqr ”  ajiyar zuciya ta sauke ba tare data bashi dama beyi tsammanin amsar daga gareta ba yaja motar suka fita daga Mall din har suka je gda babu wanda ya qara yima wani mgn tsakaninsu yana tsayawa ta dago da siririyar muryarta tace “na gde ka gaidamin da sister”

Tana fadin haka ta bude ta fita ya bita da kallo gabadaya jiyake dama ace matarsa ce gdansa ya kawota ta huta dama ace itadin ta amince dashi a matsayin miji. numfashi ya sauke ya fita ya samu yara suka shigar mata da kayan daya siyo cikin gda karbar kayan tayi a hanun yaron ta juya da nufin mayar masa amma kafin ta kai wajen yaja motarsa ya tafi.

Qwafa tayi ta juya ta shiga gdan a tsakar Gda ta zube tana mayar da numfashi kamar tayi wasan tsere zuba mata ido Ummah tayi tana nazarin ta, janyo kayan tayi ta shiga budewa wasu tsadaddun material ne guda biyu sai dogayen riguna uku da set na takalmi jaka da mayafi suma bibbiyu sai kayan shafa da sabulai masu tsadar gaske sai kwalin waya qirar Tecno K9 dagowa Umman tayi tace.

“Fauziyyah wannan kayan daga ina” dagowa  tayi tace “Ummah Dr Jameel ne bansan me yake nufi ba bansan me kalamansa suke nufi ba wlh ina tsoron faruwar wani abu tsakanina dashi Ummah namiji bashida kunya” nan ta kwashe abinda ya faru tun daga fitarta da safe har Kawo yanzu data dawo gda ita kanta Ummah hankalinta ba qaramin tashi yayi ba juyowa tayi ta dubeta duba na nutsuwa tace.

“Kul Fauzah ahir dinki da wannan cin amanar wlh ki kiyayeni kar na kuskurana qarajin kin bashi fuskar da har zai daukeki a Mota ya rinqa yi miki wadannan kalaman kinji dai na fada maki wlh Fauzah bazan yafe miki ba idan kikaci amanar Amina saboda Amina mutum ce”

Gyada kanta tayi alamar yarda da abinda Uwar tata ta fada mata mikewa tayi ta debi ruwa tayi wanka tayi sallah ta kwanta.

Bata jima da kwanciyar ba Amina ta kirata sun jima suna hira sannan sukayi sallama ta ajiye wayar ta kwanta bacci ya dauketa sai bayan la'asar ta farka jikinta yayi mugun sanyi saboda mafarkin da tayi wai gata dauke da wani jariri a hanunta gefe kuma Amina ce tsugune tana kuka.

Batasan abinda hakan yake nufi ba don haka tayi addu'a tayi sallar  la'asar ta shiga kitchen ta dora musu jallop rice and  beans wadda ta wadatu da kayan lambu bayan ta gama ta hada lemon kankana tasa a frigde ta gyara kitchen din da gdan gaba daya lkcn data gama ana kiran magrub dan haka tayi alwala ta bada farali.

Qa'idar gdan da anyi   sallar isha ake cin abinci daga nan kuma ayi zaman hira masu kalloh kuma suyi itakam Fauzah dake ba damunta kalloh yayi ba dakinta ta shiga ta kwanta ta dauki wayarta ta bude data kafin saqonnin wtsp su fara shigowa na SMS ne ya shigo budewa tayi ba tare da ta damu da abinda ya qunsa ba tunanin ta company MTN ne amma sai taga sabanin hakan.

“ _Rayuwata ta dade da shiga garari saboda ke Fauzah zuciya ta ta dade tana azabtuwa da sonki amma bansamu damar bayyana miki ba sai yanzu ki bani dama kiji abinda ke zuciya ta inasonki Fauzah ina burin yin rayuwa ta har abada dake ki yarda dani Fauzah pls wlh kece farin ciki na ”_

Ta maimaita karanta saqon yafi sau goma tare da qara duba number tabbas ba gizo takeyi mata ba number Dr Jameel ce  gabanta ya tsananta faduwa da sauri ta goge saqon tana karanta.

“ Inanillahi wa innah ilaihirraji'un Allahumma ajjirni fi musibatih wa'akalufni khairan minha, dafe kanta tayi da sauri tana fadin me wannan mutumin yake nufi da itane me yakeson ja mata meyasa yake neman zama shedan tsakaninta da matarsa duka duka yaushe akayi daran da har garin zai waye yaushe mijinta ya mutu da har zai fara bijiro mata da wadannan kalaman to wai ko dama Dr jira yake mijinta ya mutu ne???"

Tambayoyin da taketa jerowa kanta kenan wadanda bats da amsarsu ji tayi kanta yana juyawa dan haka ta kashe datarta ba tare da tayi abinda tayi niyar yi a online dinba ta kwanta can bayan kamar 2 hours har bacci ya fara daukarta kira ya shigo wayarta dauko wayar tayi ta kara a kunnenta tayi sallama da sexy voice dinta wata wahalalliyar ajiyar zuciya ya sauke yace.

“Lovely nakasa bacci saboda rashin jin amsarki wlh da gaske nake Fauzah shekara biyar na shafe soyayyarki tana azabtar dani ki taimakeni ki amsheni a matsayin miji na maye miji gurbin abokina don Allah...”

Saurin dakatar dashi tayi da cewa “haba Dr wacce irin mgn kake kamar me gusasshen hankali? inayi maka kallon me hankali da tunani ashe tunaninka na yara ne?? gaskiya ka bani mamaki kuma kabani kunya ashe duk abinda kakeyi mana badon Allah bane Dr ??? To na roqeka daga yau ka daina kuma bazan taba amincewa da abinda kazomin dashiba kai bari na qare maka zance wlh dadai na aureka gara na qarashe rayuwata babu aure saboda kaidin bana sonka kuma bazan taba sonka ba kai bayan haka ma na haramtawa kaina aure tsakanina dakai har abada saboda kaidin Mijin Amina ne Amina kuwa ba qawa tace kawai ba yar uwa tace.

Tana kaiwa  nan ta kashe wayarta cike da faduwar gaba wannan wanne irin bala'i ne ya tunkaro ta lkc guda wacce irin masifa Dr yake Neman jefata a ciki wanne kalloh Amina zatayi mata idan taji wannan katobarar da mijinta yakeyi dafe kanta tayi tace

“nikam na shiga uku Dr kar kayimin haka don Allah pls karka bari Amina taji lbrn nan don Allah karka zama silar rusa mana zumuncinmu karka zamo takobin dates amintar da muka ginata domin  Allah”.




*UMMUH HAIRAN* *CE* ...✍🏻

True Life StoryWhere stories live. Discover now