Epilogue.

3.1K 276 10
                                    


Epilogue 1.

6 Months After...

▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪▪

Iska sosai ake a lokacin da ya sauko daga private jet dinsa. A hankula ya dinga takawa har zuwa arrival lounge din airport din. Dan rufe ido yayi ya shaqi iskan and that soothed his soul, it gave him a sense of peace and security.

"You came". Yaji muryar ta.

Juyowa yayi suka hada idanu, sai a lokacin ya sake ganin striking resemblance dinta da Begum. They had the same hazel brown orbs "I did". Ya fadi a hankula. He wasn't prepared for what she did next. Matsowa kusa tayi ta kankame sa in an affectionate embrace. Wani sanyi dukansu suka ji a ran su. Growing up as an only child, it had always been Khalifa's dream to have a sibling; a sister he could dote on, one he would love with all of his heart and now that he had found her, he was going to protect her with his life.

"Malika" ya kira sunan softly "Malika Al-Haydar". Sosai taji dadin sunan da ya kirata dashi. Riqo hannunsa tayi har zuwa inda tayi parking motar ta.

"The kids are eager to meet their uncle". Ta fadi bayan sun shiga ta fara tuqi.

"How're you holding up?". Ya tambaya voice dinsa cike da so da kulawa.

"I'm doing just good and you? Have you spoken to...".

"Look ahead". Ya fadi changing their topic of discussion dan for the past 6 months daga Yasmeenah har Begum ba wanda ya nema. Tun faruwar abun he has been hiding at Saudi Arabia, too scared to face the truth. Be dawo Nigeria ba har sai ranar da yayi receiving invitation din Leek. He could never say no to his newfound sister.

Wani qatoton gate suka isa Leek ta fara honking. In no time wani lower ranking soldier ya buda gate din gida ta shiga da gudun ta. Yaranta da ke wasa da nanny dinsu a waje suka rugo da gudu gare ta.

"Come, come say hi to uncle". Ta fadi bayan ta daga Amaani from her baby walker. Reyhaan dake bayan ta ya buya ne ya fara fitowa ya miqawa khalifa hannunsa for a handshake. Murmushi khalifa yayi kan ya zuquna to the little boy's height. Ganin brother dinsa na conversing freely with their estranged uncle ya sa Amaan shima matsowa kusa. Sosai suka ji dadi lokacin da khalifa yace zai tafi da su Abuja in aka yi hutu and he'll introduce them to their cousin.

"Now come let's go in, uncle has to rest". It baffled Leek how good khalifa was with children saboda in no time yaran sunyi warming up to him. She thought a yadda he's always busy he'll hardly spare time for family but he proved her wrong, he was a committed family man. Guiding dinsa tayi har zuwa bakin kofar dakin da aka shirya musamman saboda zuwar sa. "Freshen up and come down for lunch". Ta fadi masa bayan ta ansa Amaani from his arms. Buda kofar dakin yayi ya shiga, it was a large and elaborate bedroom befitting his status. Ba tare da wani bata lokaci ba ya shige bathroom ya yi wanka tare da alwala kan ya fito ya shirya cikin wani navy blue cotton t-shirt and black sweatpants. Just as Leek asked of him, ya sauka qasa inda ya sama yaran suna kallon cartoon ita kuma tana cikin kitchen trying to set the table. Tana gamawa ta shigo living room din ta kira su to the kitchen for lunch. Hira suka dinga yi jefi jefi whilst eating, har zuwa lokacin basu riga sun gama sakin jiki da juna ba. Immediately after lunch khalifa ya koma dakin da aka basa dan ya dan huta, in no time barci ya kama sa ba shi ya tashi ba sai da aka fara kiran maghreb salaah. Bathroom ya wuce ya daura alwala, har zai kabbara sallah kenan sai ga knock a baki kofar dakinsa. Koh da ya bude wani mutum ne dogo, fari wanda daga gani ba dan arewa bane tsaye a other side na door din. Cikin fara'a yayi introducing kansa to khalifa as Hakeem, Leek's hubby.

JIRWAYE✔Donde viven las historias. Descúbrelo ahora