1-15

4.8K 192 32
                                    

**🔴🔵🔴Makirin Namiji🔴🔵🔴*

                By

     **Hafsat A Sadiq**


          
            **Dedicated**
                     To
      _My luvly sis Maryam_
                _(M twins)_


              _Page 1-5_



              *_Bismillahir rahmanur rahim*_



Kururuwan da jama'ar unguwar sukaji tayi yawane yasasu kotsawa cikin gidan inda sukaga wayam' zuwa can suka fada dakin dasuke jiyo ihu tare da sallallami turus sukayi sakamakon tozalin da idonsu yayi da umma sheme a kasa ba alaman rai atare da ita a sukwane wani makobcinsu malam sabo yayi kanta inda ya tabbatar umma ta rigamu gidan gaskia', rufe mata idanu yayi tare da fadin Allah rahamsheki asabe mutuniyar kirki daidai lokacin yaja xani ya rufeta tare da fadin Allah sa can yafi maki nan aituni wurin ya kaure da hayaniya masu kuka nayi masu addua nayi kowa tausayin yaran ya kamashi wasu ma ba mutuwar ke sasu kuka ba abunda tabari sukema wa



Zuwa wani lokaci gidan yacika makil inda akayi suturtata tare da sallah aka mikata gidanta na gaskia Haka su Hannah sukayi ta kuka abun gwanin ban tausai😭 Allah sarki umma mutuniyar kirki ba wanda zaice ga aibunta
Hannah Kam tasha kuka harta ba uku lada tausan rayuwar yan kannanta ya mamaye mata zuciya........abunda zaibaku mamaki ko reader's kunsan har akayi 3 days ba Abba Babu labarinsa inda wasu suka cika da mamaki wasu kuma suke fadin abunda yafi haka ma zaiyi indai malam bawa ne dan imaninsa ragaggene



Aran kwana na biyar ne da rasuwar umma saiga Abba kaman Wanda aka koro nan yashiga bin jama'ar dake gidan da kallo irin kallon kaskancin nan wa'inda mafiya yawansu dangin umma ne daga bisani yayi hanyar dakinsa ko gaisuwar da ake masa bai amsa ba" shigarsa ba wuya sai mukajiyo muryarsa yana kwala Kiran Hannah nan ta Mike zuwa dakinsa inda ta sameshi kwance dagashi sai singlet da gajeran wando da sauri ta kauda idonta tana mai kyamatar halin mahaifin nasu durkusawa tayi tana fadin gani Abba wannan wane salon rashin mutumci ne ina magana kina kawar mun dakai kamar wadda taga kashi saboda dama ankoya muku rashin tarbiya bakwa ganin girman Abba dan Allah kayi hakuri wlh b..........dallah rufemun baki munafukar banza da wofi to maza ki koma ki kiramun asabe saboda tsabar rashin mutumci shine aka tara mutane anata makokina andauka na mutu to ki sanar mata nadawo ina nemanta ta Allah bata mutum ba nan ganin nan bari ehhhe........... shesshekar kukanta ne yadawo dashi daga duniyar bala'in daya Lula kuka take mai matukar cin rai kamar zata shide tare da fadin haba Abba haba Abba dawane zamuji da mutuwar umma Koda cikin sauri ya katse ta da fadin kina nufin kice mun asaben ta rasu ne? Da dama Abba bakasan umma ta rasu ba cikin in'ina tayi maganar ai tuni zuciyarta ta tsinke a sukwane ta bar dakin cikin wani irin kuka matukar ban tausayi dakin umma tafada ta garkame bugun duniya Aunty Zahra tayi kanwar umma amma abanza haka tagama magiya ta hakura awajen ma su ihsan ganin yayar tasu tana kuka yasasu suma fara kukan inda suka nufi kofar suna fadin Aunty kibude kofar aunty? Aunty?? Da sauri ta mike ta bude zuciyar cunkushe tana arba dasu taji jikinta yayi sanyi janyosu tayi ta rungume tashiga rarrashi tana ta aikin rarrashi da Kiran umma har kananan sukayi barci


Ba'adauki lokaci ba suka fara jiyo hayaniya da sauri sukayo waje inda suka samu mahaifin nasu nata zuba ruwan bala'i akan wai saisun bar gidan yau inba munafurci ba miye zasuta zama har kwana bakwai da sauri Hannah ta zube gabansa da magiya akan yabari ayi bakwai Amma kememe yaki haka suka harhada kayayyakinsu aunty Zahra ce taita lallashinsu tare da fadin suyita hakuri komai mai wucewa ne sannan su cigaba da biyayya ga mahaifinsu dan basu da kowa saishi aduniyar nan sannan suka dauki hanya kowa zuciyarsa a cunkushe


Ran bakwai Yan'uwan umma sun nemi tafiya dasu amma fur Abba yaki amincewa haka suka tafi da jimamin barin
Da dare suna zaune adakin umma inda kananan sungaji da rigima sunyi barci saiga Abba da bako wai anan gidanmu zai zauna Hannah gaba daya zuciyarta bata yarda da mutumin ba amma ba yanda ta iya haka kowa yaje ya kwanta inda Hannah taita tuna mayataccen kallon da bakon yaketa mata har bacci barawo ya saceta


Kamu telah mencapai bab terakhir yang dipublikasikan.

⏰ Terakhir diperbarui: Mar 11, 2019 ⏰

Tambahkan cerita ini ke Perpustakaan untuk mendapatkan notifikasi saat ada bab baru!

MAKIRIN NAMIJITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang