Part 17

1K 51 2
                                    

💠💠💠💠💠
*©® 2019.*
*6/Feb.*

*ZAB'IN WA ZANBI...???* 💥
(ιyayena ĸo zυcιyaтa).?

💐💐
💥

*ѕtσrч______wríttєn*
*вч*
♡нawwa м.υ {$mαѕhєr}.♡
*_____________________*
★★★ ★ ★★★
*_____________________*
*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/
___________________________
___________________________
بسم الله الر حمن الر حيم...........

_Allahumag-firliiy,wali-walidiyna,wali-mashayikina,wali-akhwatina,wali-ikhwanina,wàli-asdik'a'ina,al-ahya'u minhum,wal-amwaat,Allahumag-firnà war-hamna._

*83--84.*
_____
_____

°°°°°°°°Bai kai k'arshe ba ta buga masa tsawa mai firgitarwa daya sashi yin shiru,cikin k'ara jin masifa ta shiga zazzaga masa maganganu masu kaushi,da suka sashi dawowa cikin nutsuwarsa
"Akan mene zaka dunga kirana da irin wad'annan sunayen alhalin baka sanar dani laifi d'aya dana aikata maka ba,idan da ace ka kamani da laifin yaudara,ha'inci game kuma da butulci shi ne zaka kirani da wad'annan sunayen,shin ka tab'a jin hukuncin da aka yankewa mutum ba tare da an sanar da shi laifinsa ba..Ko kuwa kai haka ka tarar ana yin shari'a a naka tsarin kundin...?"
Shiru yayi ya kasa magana,sai kallonta da yake,sassauta murya tayi itama tana ci gaba da fad'in
"Kafin ka tuhumi mutum akan abunda bai sani ba ka fara bincike tukun,idan ka tabbatar ya aikata laifin ka sanar da shi laifinsa ta yiwu wani ya aikata hakan ne acikin rashin sani,ta yiwu kuma yana sane ya aikata,amma kafin yanke hukunci ka fara tuntub'ar mutum kasan gaskiyar al'amarinsa..."
Juyawa tayi da niyyar ficewa yayi saurin dakatar da ita,tsayawa tayi cak ba tare data juya ba,k'arasawa yayi kusa da ita ya tsaya,a hankali ta kalleshi idanunta suna cikowa da hawaye
"Dawo muyi magana..!"
Babu musu ko ta juya ta nemi guri ta zauna tana goge y'an siraran layin hawayen da suka zubo mata,da farko kasa magana yayi ya tsaya kawai sai juya abun yake a ransa
"Kace za muyi magana kuma kayi shiru baka cemin komai ba har yanzun."

Kallonta ya sake yi yana had'iye wani abu dake masa d'aci a zuciyarsa,sai daya zauna a kusa da ita sannan ya fara magana
"My lady dan Allah ina son ki fad'amin gaskiya,kin san dai yadda muke da juna,bamu tab'a yiwa juna k'arya ba,haka duk runtsi da wahala mukan sanarma junanmu gaskiya idan ta kama ko..?"
Kai ta d'aga masa
"To ina so ki duba girman Allah da manzonsa ki sanarmin gaskiya shin akwai wani wanda kike so bayan ni..?"
Kai ta girgiza masa
"A'a My lady kada muyi haka dake,magana zaki bud'e baki kiyimin,wannan maganar tana da matuk'ar muhimmanci ne a garemu,ki bud'e bakinki muyi magana ta fahimta.."

"A'a babu.."
Ta fad'a tana kallonsa
"Ok naji wannan..To amma shin a gida ko wani gurin kin tab'a jin labarin ga wani da yake sonki bayan ni..?"
Nanma dai amsar tata irin ta farko ce,sai daya sauke dogon ajiyar zuciya sannan ya furta
"Shin kinsan da cewa iyayena sunje gidanku nemamin aurenki..?"
Amsar dai hallau irinta farko ce wato 'A'a,jijjiga kai yayi
"To a hak'ik'anin gaskiya shi ne Unaysa iyayena sunje gidanku kimanin kwanaki sha takwas da suka gabata,amma labarin da suka tarar shi ne an riga da ansa miki rana da wani...!"
Mik'ewa tayi a razane tana dafe chest
"Me kace..?"

"Tabbas! Unaysa abunda kunnuwanki suka ji babu k'arya cikinsu,iyayenki sun riga sun yanke hukuncin aurar dake ga wani na,kuma ina da tabbacin lefen da kike min maganarsa bana kowa bane face naki da wancan wanda iyayenki suka *ZAB'A MIKI."*

"Innalillahi wa'inna ilai raji'un..Allahumma ajirniy fiiy musibatiiy wa'aklufniiy khairan minha..."
Abunda bakinta ke maimaitawa kenan,zuciyarta tuni tayi k'unci,yayin da hawaye suka shiga ambaliya,hanya ta kama zata fice a matuk'ar razane yayi saurin rik'ota yana girgiza mata kai
"Dan Allah ka sake ni naje gida.."

ZAB'IN WA ZANBI.? (IYAYENA KO ZUCIYATA) COMPLETEDOù les histoires vivent. Découvrez maintenant