[10/15, 08:41] M Shakur.: *UMAR FARUQH*
23Da sauri yakara sa shiga rafin dan wanke kafafun shi dasuka baci da tabo. tsayawa yay chak dan ganin kaman inuwa inuwan mutum a cikin ruwan dake yawo kaman reshen bishiya da sauri yakara sa tumbulawa cikin rafin alokacin yakara gasgata kanshi ganin yarinyar nayin chan kasa yasa yafara iyo da sauri harya cimmata ya rikota gam yafito da ita daga rafin ya ijiyeta a bakin rafin kafin yakara sa fitowa yana share fuskarshi. Bakinta ya bude ya hura mata iska kafin ya danne cikinta saida yay haka kusan sau uku sanan tahau tari tana amayar da ruwan datasha saida tagama sanan tafashe da kuka sosai tana rawar sanyi dan tsohon ya kalleta yace "yarinya kin iya ruwa ne? Maiya kaiki shiga?" Bata amsaba tacigaba da kuka sosai Baffa ya kara kallon ta "anya ke yar garin nan cema kuwa?? Ko kece bakin danaji ance mai gari yayi daga birnin zaria?" Ahankali Bisma ta gyada mai kai tana hawaye. Baffa yace "ya isa to muje nakaiki gida ki chanza kaya naga kina rawar sanyi" ahankali ta mike tsaye tana kuka sosai Baffa ya kalleta "yakuri karki kara zuwa rafi tunda baki iyaba,kinga yanzu inda ban isoba da kin mutu" kara sautin kukan tayi sanan tace "nagode".
Saida ya ijiyeta a bakin kofar gidan mai gari sanan yajuya yatafi.
Gidan ta shiga tana tafiya a hankali matar mai gari tafara gani a tsakar gida tana wanke shinkafa da sauri ta ijiye shinkafan ta karaso da sauri tace "maiya sameki Bisma? Maiya jikaki haka?" Jin an ambato sunan Bisma yasa Amal tafito itama da gudu tai turus a bakin kofa tana kallon Bisma tace "maiya sameki?maiya jikaki haka?" Bisma tai murmushi tana rawan sanyi tace "fadawa rafi nayi,wani bafilatani ne ya cironi" Matar mai gari tace "dama baki iya iyoba kikaje rafi,karki kara Allah kiyaye gaba" Amin Bisma tace ta juya tabi bayan Amal suka shiga dakinsu tafashe da kuka tafada jikin Amal.Amal tace "U are hiding something, maiya faru dake Bisma?" Ahankali ta mike ta cire kayan jikinta kafin tadau towel ta daura tayi hanyar fita Amal tace "Madina na bayi kijira tafito sai kije kiyi wankan" ahankali ta dawo ta kwanta kan gado tareda shigewa cikin bargo tana makyarkyata Amal takara matsowa tace" Bisma wos wrong" Bisma cikin tsawa da tsiwa tace "ki kyaleni,don't insist i can handle all my problems" takarashe maganan tana sheshekan kuka "kuma wlh kutashi mubar garin nan yanzu,am sick of dis damn village" tacigaba da kuka. Madina dake shigowa dakin ta kalli Amal tace "sis maiya sameta? " Amal ta sauke ajiyan zuciya tace "i donno,yanzu ta shigo wai tafada rafi,yanzu kuma tahau kuka tana masifa,Ya Madina dan kira dogari kifada mai su shirya zamu tafi yanzu" Madina da ita kadai ce ta tuna ta taho da wayarta kauye ta dauka ta kira dogari nan da nan aka shiryama tafiyar da kyar Bisman tai wanka ta shirya cikin riga da sket na Brown nd golden atampha ta yafa dan karamin golden gyale a wuya tadau golden takalmin ta flat tasa. ko mai bata shafaba turare kawai tafesa tafito fuuu su Amal nabinta abaya.
Wajen mai gari sukaje yay musu shatara na arziki yabasu dubu uku da kyar suka karba dan karyaga kaman sun raina yayinda matarshi ta cika musu buhunhuna dasu goruba, tofi,hanjin ligidi,shasshaka,danta matsisi,iloka,tuwon madara, bulalar kishiya,taabo,da dai sauran su suka karba sukai godiya.
A kofar gida Bisma taga Auta, dari biyar tabashi da ragowan chocolates dinta tace mai "Auta ina zan iya ganin na Yanka yanzu?" Adan tsorace ya kalleta "yar bunni nidai bazani ba,amma nasan yanzu yana dandali" kallon driver su tayi tace "kasan dandalin kauyen nan?" Eh nasani to kaimu wajen. mota suka shiga su Amal dai basu cemata komiba ganin masifa tajeji. Fadawa ma suka shiga motar su a kofar dandali sukai parking inda babu wanda yafito sai Bisma takara sa gaban Na Yanka dayay kaman bai ganta ba yana hira da gang dinsa.
Kirjinta na mugun bugawa kaman zai fashe saboda tsoro takaraso ciki, cikeda tsiwa tace "Allah ya isa,mugu kawai azzalumi wlh inda namutu dazu da baka kwana lafiya ba yau " sai alokacin ya juyo dakai ya kafeta da idanu yaranshi ma haka. Shiru tayi saboda tsoro da kuma yanda idanunshi suka cika mata ido juyamai baya tayi da sauri ta cigaba da magana "I will make ur life miserable, ba'a taba marina ba,but u took dos ur damn filthy hands and slapped me" ta goge hawaye tace "you will pay for it,wlh saikasan kataba yar gatan Miemie da Abba na, mugu kawai,basamude" a zuciye Murucci yay kanta zai mareta Na Yanka yace " Bas! barta tacigaba".
Alokacin takara juyowa ta kalleshi shima ita yake kallo, yadan cije yatsan shi tareda yin kara kaman dan yaro yace "wayyo Miemie na Abba na hannu na kizo, wayyo bapi " duka yaranshi suka fashe da dariyar keta dan gane dawa yake. Dip ya dauke murmushin dake fuskarshi yamata kallon sama da kasa ya tofar da miyau a gefe. Kafin ya fashe da dariya yace "Murucci Miemie na,Abba na" kya kya kya suka fashe da dariyar mugunta suna nuna Bisma. da gudu Bisma tajuya ta shiga mota tana kuka sosai kaman ana zare mata rai.
Maman Abd Shakur😘
