||

697 82 2
                                    

Anyi suna lafiya an gama yarinya taci sunan kakarta ta wurin uwa wato Fatima Bintu. Yan uwa da abokan arziqi duk sun koma gidajen su ya rage daga Subaiha, Sa'adatu sai kuma sirikar su wato maihaifiyar su Bashir da Uthman sai kuma yaran gidan.

Hajiya Tafada ba a gidan take zaune ba kawai dai tazo ne ta taya Subaiha jego. Uthman daman dan mama ne dan har izuwa yanzu in abun nasa ya motsa sai yayi ta zuba shagwaba kamar bai ajiye yara ba. Shi kuwa Bashir bai wani saba sosai da ita ba kuma yawa yawan lokaci ma basa shiri. Sai kuma 'yar autar ta Basma wacce take auren wani mai kudi da yake zaune a UK.

Ansha fama da ita kuwa kafin ta amince ta aure shi saboda irin kamar auren hadi ne ga kuma contract. Sai take ganin kamar kawai anaso a siyar da ita ne. Yo ban da abun ta ay ko wacce mace ma siyar da ita akeyi tunda, kudi ake bayar wa da goro, ga lefe kuma sai Fatiha shikenan ace anyi wa yarinya aure.

Meye banbanci wannan da siyarwa toh? Lol.

Wani abun da yasa ta qara qin amincewa dashi wai bazawari ne ya taba aure suka rabu da matar kuma duk a dalilin kudi ne. Shiyasa ta qi shi fir! Da lallami da dabara aka lallaba ta aure shi cikon Allah kuma ko kan su ba'a ji. Zaune suke lafiya babu wata damuwa. Duk sanda sukayi waya da Hajiya sai ta tsokane ta tace 'abun da babba ya hango ko dala yaro ze hau baze gani ba' a haka dai Basma zatayi dariya a watsar da zancen.

Fa'idar bin iyaye kenan. Ko da kuwa mutum baya son abu sai ya daure yaga ya bi umarnin su. Sanadiyar wannan biyayyar sai Allah ya taimaki mutum. Allah ya raba mu da iyayen mu lafiya.

Zaune suke a parlourn da ya fi ko wanne girma a gidan wanda yake a tsakanin part din Subaiha da Sa'adatu. Parlour ne babba sosai mai hade da bandaki. Kallon labarai suke yi amma kowa dai saqe saqen sa ya keyi a rai irin wanda ba'a rasa ba.

Sallamar Uthman ce ta katse wa kowa tunani. Da gudu yaran suka je suka rungume shi suna tsalle har 'yayan Bashir. Sa'adatu ce ta gyara mayafin ta sannan ta gyara zaman ta tana murmushi. Abun yana birge ta yanda yaron suka dauke shi kamar shi ya haife su.

Bayan ya miqa musu kayan qwalandamashe duk sai suka watse suna murna. Ganin Hajiya na wajen ne ya hana Subaiha tashi tayi masa welcome hug. Kallon ta yayi ya kashe mata ido. Ta danyi murmushi har cikin ranta, basu sani ba ashe Hajiya tana kallo amma sai ta kau da kai. Itama Sa'adatu akan idon ta akayi. Nan taji gaba daya tana missing Bashir kamar kullum.

In banda kasuwanci a qasashen qetare ba abun da ya saka a gaba. Sai ya dawo yayi ta mata dadin baki wanda baya wuce kwana biyu. Ita kuwa abun duk ya ishe ta. Wayar ta dauka ta fara kiran sa, jin wayar ta shiga yasa ta miqe ta bar parlourn.

Ta kira ya kai sau biyar ba'a dauka ba. Qarshe ma dai sai ji tayi ance wayar a kashe. Tsaki tayi hawaye na sauka akan kumatun ta. Taje ta tabbatar yaran kowa ya kintsa yayi shirin bacci. Kamar kullum, Madina rubuce rubuce takeyi. Kawai murmushi tayi mata ta bar wajen. Sa'adatu bata taba tsayawa duba abunda Madina take rubutawa ba. Kullum sai shirgin takardu.

Dakin mai aykin gidan ta leqa taga itama tayi bacci saboda irin masu baccin wurin nan ne. Asabe babu ruwan ta, dattijuwa ce wadda mijinta ya mutu tun da saurin yarintar ta amma bata qara aure ba. Yaran ta duk masu hali ne kasancewar jajircewar da tayi taga lallai sun zama yara nagari wanda al'umma zatayi alfahari dasu. Duk irin hidimar da suke yi mata, haka ta nace ta kafe wai ita sai tayi aykatau saboda ta dinga motsa jikin ta wai kar ta tsufa da wuri. Haka suka haqura suka qyaleta.

Sa'adatu koma wa parlor tayi inda taga Hajiya ita kadai tayi kicin kicin ran nan a bace. Kamar ba zata ce wani abu ba, sai kuma tace

"Hajiya lafiya kuwa? Ko ciwon qafar ne?" Hajiyan ce ta tabe baki.

"Wai ki ga yaran nan, haka suka shige daki suka bar ni. Gaskiya na soma gaskata abun da ake gaya mun." Murmushi Sa'adatun tayi. Daman tasan komai daren dadewa sai Hajiya tayi tunanin an asirce mata da ne.

Dama mata haka suke, in mijin su yayi musu abu to kyautatawa ce amma idan mijin wata musamman in mijin dan uwansu ne, indai yayi wa matar sa abu toh fa wannan asiri ne. Kai Allah yasa mu dace.

"Haba Hajiya kar kiyi tunanin haka. Wallahi ba haka bane." Su Subaiha daman sun gaji da yiwa Hajiya kara ne. Daga ranar suna zuwa yau kwana sha biyar kenan. Saboda ita ko gaysawar kirki basa yi saboda kar tace sunyi rashin da'a.

"Yo ay shikenan. Ko ma meye dai ay jego takeyi nasan ma saboda sabon jariri yake tattalin ta. Zaiyi ya gama ne bashi nan da sati daya." Ita dai Sa'adatu bata tanka mata ba.

"Wai ina ja'irin yaron nan Bashir? Mutum in banda kudi ba abunda yake qauna a rayuwar sa? Kai Allah ya shirya mana zuri'a. Ina mahaifiyar sa guda amma sai ya kwashe sati guda bai kira ni ba." Sa'adatun ce ta girgiza kai. To ita tana matar sa ma sai tayi wata hudu bata saka shi a idon ta ba. Ko da yake uwa tafi ta matsayi amma a matsayin ta na matar sa wacce take da haqqi akan sa ya kamata ya tausaya ma rayuwar ta amma shikam ta kudi yake kawai.

"Allah ya kyauta. Amma Hajiya dan Allah ayi masa fada. Inayin rabin shekara ban ganshi ba wani lokacin." Sa'adatun gwanin tausayi ta fadi haka.

"Ka ji mun ya. Shikenan kuma zaki qala masa sharri ko? To ba zan lamunta ba. In banda lalacewar zamani ma, yaushe har zaki iya duba ta ki min magana irin wannan." Wasu lokutan sai Hajiyan ta dinga abu kamar wacce bata yi karatu ba ko kuma ace kamar ba wayeyyiya ba kuma alhali diploma gare ta. Ko da yake mutanen da haka suke. Sa'adatu tayi tunanin fadawa Hajiya zai saka tayi masa magana kamar yanda ta saba amma sai ga sabanin haka ya biyo baya. Batayi wani mamaki ba saboda taga yau ran Hajiyan a bace ya ke.

Hamma tayi kafin ta miqe tana duban agogo.

"Hajiya zan kwanta, sai da safe." Bata jira ko sakan daya ba ta wuce dakin ta. Kukan da take riqewa ne ya kufce mata. Kuka ya zame mata al'ada, in bata yi ba radadin zuciyar ta baya raguwa. Alwala tayi ta fara jero nafilfili tana roqan Allah ya sassauta mata wannan jarrabawar ya kuma bata ikon tsallake ta. Bata ankara ba, tana kan dadduma bacci ya sace ta.

****

Akwai wanda yadan Fahimci wani abu? A yi voting ta hanyar danna tauraron qasan nan na hannun hagu.

Haka kuma zaku iya bayyana ra'ayinku ta hanyar comment. Shima ga gidan comment a qasa.

Zaku iya sharing ga masoyan littafin Hausa. Nayi muku alqawarin zakuji dadin littafin da yardar Allah.

Kuyi following dina domin samun updates da wuri. Nagode❤❤

Dare daya.Where stories live. Discover now